18/05/2026
MAULUDIN IMAM RIDHA (AS) NA GAMAYYAR ISLAMIYYUN SARIYYAR IMAM ALI ZAINUL ABIDIN A KATSINA.
A daren ranar Litinin 1 ga watan Zul-Hajji, 1447H, wanda ya yi daidai da 18 ga watan Mayu, 2026M, an gudanar da taron Mauludin Imam Ridha (AS) na gamayyar Islamiyyun da suke ƙarƙashin Sariyyatul Imam Ali Zainul Abidin a Katsina.
An fara taron da buɗe shi da addu’a tare da gabatar da karatun Alƙur’ani mai girma, sannan aka ci gaba da waƙoƙin yabo ga Ahlul-Baiti (AS), cikin yanayi na farin ciki da girmamawa ga wannan munasaba mai albarka.
Daga bisani, Malam Bishir MB ya gabatar da makasudin wannan taro, inda ya bayyana cewa haɗuwar tasu ba wai taro na al’ada kawai ba ne, illa wata hanya ce ta raya al’amuran Ahlul-Baiti (AS) da kuma tabbatar da cewa ƙaunar iyalan Manzon Allah (SAWW) tana nan a zukatan al’umma. Ya bayyana cewa tunawa da rayuwar Imamai na daga cikin hanyoyin ilmantar da matasa da ƙarfafa su wajen koyi da halaye da dabi’un bayin Allah na gari. Haka kuma ya jaddada cewa irin waɗannan taruka suna taimakawa wajen haɗa zukata da ƙarfafa zumunci tsakanin ɗalibai da malamai.
Bayan haka, aka gabatar da mai gabatarwa wanda ya kasance Malam Yaqoub Idris Katsina. Kafin gabatar da babban mai jawabi kuwa, ɗalibai daga Islamiyyu daban-daban sun gabatar da muƙalu masu ɗauke da bayanai kan rayuwar Imam Ridha (AS).
Madarasatul Tahrikul Islam, ta bakin Malam Hussaini Tasi’u, ta gabatar da muƙala kan haihuwar Imam Ridha (AS), inda ya yi bayani kan asalin haihuwar Imam ɗin da irin yanayin gidan da ya tashi, yana mai bayyana cewa tun daga ƙuruciyarsa ya kasance cikin ilimi, tarbiyya da ibada.
Sai Madarasatul Irshadun Islam, ta bakin Malama Fatima Bishir, wacce ta gabatar da muƙala kan ilimin Imam Ridha (AS). Ta bayyana yadda Imam Ridha ya kasance mashahuri wajen ilimi da hikima, inda malamai da masu neman ilimi daga wurare daban-daban suke zuwa domin amfana daga iliminsa da fahimtarsa.
Haka kuma Madarasatul Azzahara Gidan Kaji, ta bakin Malama Khadijah Sani, ta yi bayani kan ibadar Imam Ridha (AS), inda ta kawo yadda Imam ɗin ya kasance mai yawaita bautar Allah, haƙuri da tawakkali, duk kuwa da irin ƙalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa.
A nata ɓangaren, Madarasatul Rasulul Akram, ta bakin Malama Khadijah Zunaidu, ta gabatar da muƙala kan mu’ujizozin Imam Ridha (AS), inda ta yi bayanin wasu daga cikin abubuwan mamaki da hikimomi da s**a bayyana a rayuwarsa, waɗanda s**a nuna matsayinsa da kusancinsa ga Allah (SWT).
Daga bisani, babban mai jawabi ya fara da miƙa godiya ga Allah (SWT) bisa damar da Ya bayar na halartar wannan taro mai albarka domin raya munasabar Ahlul-Baiti (AS). Bayan haka ya tsunduma cikin jawabi mai zurfi kan rayuwar Imam Ridha (AS), inda ya bayyana cewa Imam Ridha ya kasance fitila ce ta ilimi, haƙuri da jagoranci a cikin al’umma.
Malamin ya yi bayani kan yadda Imam Ridha (AS) ya rayu a wani lokaci mai cike da ƙalubale da matsin lamba daga mahukunta, amma duk da haka bai gushe ba wajen kare addini da koyar da gaskiya. Ya bayyana cewa Imam Ridha ya yi amfani da hikima, ilimi da kyakkyawar mu’amala wajen jawo zukatan mutane zuwa ga tafarkin Allah.
Ya ƙara da cewa rayuwar Imam Ridha (AS) tana ɗauke da darussa masu yawa ga matasa, musamman ta fuskar neman ilimi, haƙuri a lokacin jarabawa da kuma tsayuwa kan gaskiya ba tare da tsoro ba. Ya jaddada cewa Ahlul-Baiti (AS) ba tarihi kawai ba ne, su makaranta ce ta tarbiyya da gyaran rayuwa.
Haka kuma malamin ya yi kira ga ɗalibai da matasa da su ƙara himma wajen neman ilimi da raya addini, tare da riƙo da halayen Imam Ridha (AS) na tawali’u, karamci da tausayi ga jama’a. Ya bayyana cewa al’umma ba za ta gyaru ba sai ta koma ga koyarwar Alƙur’ani da tafarkin Ahlul-Baiti (AS).
Daga ƙarshe, an rufe taron da addu’a, inda aka roƙi Allah Ya ƙara haɗa zukatan muminai, Ya ba su ikon koyi da Ahlul-Baiti (AS), tare da neman albarka da kariya ga al’umma baki ɗaya.
Media Forum Katsina Update
__ Litinin: 18/Mayu/2026M.