01/09/2025
Yaa ArRahmaan ka shiga cikin wannan lamari domin dunbin Rahmar ka!
Masu Makarantun Kudi Sun Yi Fatali da Sabon Tsarin Ilimi na Gwamnatin Katsina
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times | Litinin, 1 ga Satumba 2025
Kungiyar National Association of Proprietors of Private Schools (NAPPS) reshen Jihar Katsina ta yi tir da sabon tsarin ilimi da gwamnatin jihar ta gabatar, tana gargadi cewa wannan mataki zai iya hallaka makarantu masu zaman kansu tare da jefa makomar ɗalibai cikin haɗari.
Shugaban NAPPS a Katsina, Malam Mansir Sani Jibiya, ya bayyana haka ne a taron manema labarai da aka gudanar a ginin KEBRAM, kan titin Mani, kusa da WTC, inda ya kira wannan tsari a matsayin mai “tsauri, wariya da kuma barazana ga ilimi a jihar.”
Muhimman Abubuwan da S**a Jawo Cece-kuce
Jibiya ya bayyana aƙalla batutuwa shida da s**a zama manyan matsaloli ga masu makarantu:
1. Sake Siyan Takardun Rijista: Duk da cewa makarantu masu zaman kansu sun riga sun sayi fom daga gwamnatoci da s**a gabata, yanzu an umarce su da su sake siya.
2. Sake Rijistar Makarantun da Aka Riga Aka Ba Lasisi: An tilasta wa makarantu da aka riga aka ba lasisi su sake rijista, abin da Jibiya ya kwatanta da “sake yin rajista ga ɗalibin jami’a da ya kai matakin shekara ta uku.”
3. Kudin Haraji na Shekara: Sabon tsarin ya wajabta a biya gwamnati kashi 3% na kuɗin makaranta daga kowanne ɗalibi a duk shekara, abin da masu makarantu s**a ce bai taɓa shafar sauran ɓangarorin kasuwanci a jihar ba.
4. Haɓaka Kudin Lasisi: An sanya makarantu cikin rukunoni uku – ₦250,000 na birane, ₦175,000 na unguwannin matsakaici, da ₦100,000 na yankunan karkara, tare da ƙarin kudin “haɓakawa” na ₦200,000.
5. Lasisi Mai Ƙarewa Bayan Shekaru Biyar: Sabon tsarin ya tanadi cewa duk lasisin makarantu zai ƙare bayan shekaru biyar, lamarin da zai tilasta musu sake fara dukkan matakan rijista ko kuma su kasance a matsayin “makarantu marasa doka.”
6. Hanawa Ƙara Kuɗin Makaranta: An haramta wa kowace makaranta ta ƙara kuɗin makaranta ko da sisin kwabo ba tare da izinin kwamishinan ilimi ba, abin da Jibiya ya ce “ma fi muni ne fiye da mulkin soja.”
Shugaban kungiyar ya ce wannan doka za ta durƙusar da makarantu masu zaman kansu, waɗanda da dama ba su da isasshen ƙarfin kuɗi saboda tsadar rayuwa, rashin tsaro da hauhawar farashi.
“Yanzu haka, wasu daga cikin makarantu ba su iya biyan ma’aikata albashin watan Yuli ba. Muna da fiye da makarantu 1,400, muna koyar da sama da dalibai 500,000, kuma muna ɗaukar ma’aikata sama da 14,000. Tilasta biyan waɗannan kudade ba tare da izinin ƙara kuɗin makaranta ba tamkar tursasa mana rufewa ne,” in ji shi.
Ya kuma yi zargin cewa Kwamishinar Ilimi ta Firamare da Sakandare, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta ƙi sauraren kungiyar a ofishinta, maimakon haka tana amfani da barazana da kausasan maganganu.
“Muna kiranta da ‘Her Majesty’ saboda salon mulkinta na doka-da-ƙarfi. Mun aiko mata da wasiku da dama domin mu gana, amma ko sau ɗaya ba ta ba mu lokaci ba. Maimakon haka ta yi barazanar rufe makarantu, tana zarginmu da neman kuɗi da rashin kishin jiha,” in ji Jibiya.
Kungiyar ta roƙi Gwamna Mallam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, da ya hanzarta shiga tsakani.
“Idan aka rufe makarantu masu zaman kansu, makomar ɗalibai dubban ɗaruruwan za ta salwanta. Wannan ba batun masu makarantu kaɗai ba ne, batun makomar yaran Katsina ne,” in ji shi.
“Mu Malamai Ne, Ba Ɓarayi Ba”
Jibiya ya ce masu makarantu suna taimaka wa gwamnati wajen rage rashin tsaro da samar da ayyukan yi, don haka bai kamata a raina rawar da suke takawa ba.
“Mu ba ‘yan fashi ba ne. Chalk muke riƙewa, ba bindiga ba. Muna rage rashin tsaro ta hanyar ilimantar da al’umma. Amma duk abin da muke samu daga gwamnati shi ne tsauraran dokoki da wariya,” in ji shi.
NAPPS ta bayyana cewa idan gwamnati ta dage kan wannan sabon tsari, tana da niyyar ɗaukar matakin shari’a bayan tattaunawa da shugabancin ƙasa na kungiyar.
“Ko yaƙi a ƙarshe kan teburin tattaunawa ake kammalashi. Idan gwamnati ta ƙi sauraro, matakin karshe zai iya kasancewa kotu,” Jibiya ya ƙara da cewa.
Bangaren ilimi a Katsina na fama da cunkoso da ƙarancin kayan aiki a makarantu na gwamnati. Makarantu masu zaman kansu sun cike wannan gibi tsawon shekaru, amma sabon tsarin gwamnati ya jefa makomarsu cikin ruɗani. Inji shi.