Al-Asad Education Foundation

Al-Asad Education Foundation An kirkiri wannan page ne domin Wayar da kan mutane akan Abinda ya Shafi ayyukan AL-ASAD EDU. FDN
(2)

28/12/2025

Nasabarka ba ta tabbatuwa har sai ka kasance ka riƙe abinda ya jawo ma mahaifanka girma a idon duniya, in ba haka ba, nasabarka ba zata amfana maka da komai ba, Ɗan Annabi Nuhu Alaihissalam darasi ne ga kowa.

Jumu'ah Mubarakah 5th Rajab, 1447 | 26th December, 2025
26/12/2025

Jumu'ah Mubarakah
5th Rajab, 1447 | 26th December, 2025

22/12/2025

Alakar Shehu Ibrahim INYASS RADIYALLAHU TA'ALA ANHU da Alqur'ani mai girma..

Maulana Sheikh Goni Dr Muneer Ja'afar Katsina HAFIZAHULLAH yana cewa:"Akwai abubuwan da ba wanda yake da ikon yi ma kans...
20/12/2025

Maulana Sheikh Goni Dr Muneer Ja'afar Katsina HAFIZAHULLAH yana cewa:

"Akwai abubuwan da ba wanda yake da ikon yi ma kanshi, sai abinda Allah ya ƙaddara mashi, ni'ima ce daga gareshi ba zabinka bane sune kamar haka:

- MUSULUNCI: Ba iyawarka bace ta sanya Allah yayi ka a musulmi kuma mumini ba. Idan ya so sai yayi ka a cikin waɗanda basu yi imani ba.

- ƊAN ADAM: Ba ƙoƙarin ka bane ya sanya Allah yayi ka mutum ba, in da yaso sai yayi ka a cikin wasu halittun ba ƴan Adam ba, ni'ima ce babba abin godewa da Allah yayi ka a cikin mafi girman halittar da yayi.

- NASABA: ba zaɓin mutum bane ya sanya iyayen shi s**a zamo nashi ba, yin Allah ne, in da kowa shi zai zaɓi iyayen shi da babu wani wanda zai zaɓi gida ba gidan Shugaban halitta Sallallahu alaihi Wasallam ba.

- TSARIN HALITTA: Maulana yaci gaba da cewa, tsarin halittar ka ba aikin ka bane ko ƙoƙarin ka ya sanya Allah yayi ka da kyau, yayi wani da kyaun da bai kai naka ba, a'a shi ya so haka, ba wayonka bane ko dabararka.

Duka wannan bayanin na Maulana Sheikh, yana nuna mana cewa duka waɗannan abubuwan ba mai alfahari dasu sai wawa ko kuma marar ilmi saboda babu wanda yayi kanshi, ko yake da ikon samar ma kanshi wani abu sai abinda Allah ya ƙaddara mashi.

Barka da safiya.

Jumu'ah Mubarakah27th Jimadal Akhir, 1447 | 19th December, 2025
19/12/2025

Jumu'ah Mubarakah
27th Jimadal Akhir, 1447 | 19th December, 2025

19/12/2025

Barka da juma'a daga Maulana Sheikh Goni Dr Muneer Sheikh Ja'afar Katsina HAFIZAHULLAH.

MASOYI A GARIN MASOYINSA. Maulana Sheikh Goni Dr Muneer Sheikh Ja'afar Katsina HAFIZAHULLAH yana garin Madina a jiya dom...
17/12/2025

MASOYI A GARIN MASOYINSA.

Maulana Sheikh Goni Dr Muneer Sheikh Ja'afar Katsina HAFIZAHULLAH yana garin Madina a jiya domin jaddada ziyara da soyayya ga Masoyinmu, Shugaban Halitta, Sayyidna RasululLah ﷺ.

Ya kake ji idan ka kasance a kusa da masoyin da kake ta kirdadon haɗuwa da shi ko a nesa ko a kusa, Maulanmu Sheikh Ibrahim NYASSE RADIYALLAHU TA'ALA ANHU yana cewa "yana yawaita taku a cikin garin Madina ko da ya yi Sa'a ya tsaya a wani wurin inda Shugaba ﷺ ya taɓa tsayawa" wannan shi ne maƙurar ƙurewa na cimma muradin Soyayya.

Kasancewar Maulana Sheikh Goni suna son litattafai domin sune abokan hirarsu, sune abincin su ne abin shan su, sai s**a samu masauki wanda yake haɗe da wani ɗakin karatu, wanda ya ƙunshi littattafai na addinin musulunci musamman wanda s**a shafi Alqur'ani da kuma ƙira'at, wato abin nufi dai shi ne in anyi ziyara da ibada sai kuma a ba ruhi abinci da karatu.

Daga bisani Maulana Sheikh Goni sun tafi Makka a jiya domin gabatar da Umrah, muna roƙon Allah ya karbi ibadar su, ya maido mana da su gida lafiya albarkar shugaban halitta Annabi Muhammad ﷺ

16/12/2025

DARUSSA DAGA TAFSIRIN RAMADAN...

MAULANA SHEIKH GONI DR MUNEER SHEIKH JA'AFAR KATSINA HAFIZAHULLAH YANA KARANTA DUK AYOYIN DA S**A ZO DA KISSAR ANNABI NUHU A.S A CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA TUN DAGA CIKIN SURATUL A'ARAF HAR SURATUL NUHU ƊIN.

ALLAH YA ƘARA MA MAULANA SHEIKH LAFIYA DA TSAWON KWANA.

Maulana Sheikh Goni Dr Muneer Sheikh Ja'afar Katsina HAFIZAHULLAH, yana yawan maimaita mana wasu abubuwa guda biyu yana ...
15/12/2025

Maulana Sheikh Goni Dr Muneer Sheikh Ja'afar Katsina HAFIZAHULLAH, yana yawan maimaita mana wasu abubuwa guda biyu yana cewa:

- Duk sadda ka ga kana ganin girman Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam kayi godiya ga Allah domin Allah yana son yayi maka rahama ne, amma idan Ubangiji yana son yayi maka talala sai ya sanya zuciyarka ta rinƙa ƙaiƙayi idan aka ambaci girman Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.

- Duk lokacin da ka ji zaka iya ɗaga hannu ko kuma ka keɓance kanka a wani wuri ka roƙi Allah wani abu da kake nema, to daman Ubangiji ya shirya amsa maka buƙatarka.

Duk da na farkon da na biyun, abu uku ne suke tabbatar dasu sune karatun Alqur'ani mai girma, Istigfari, da kuma dagewa da Salatin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَىٰ سَيِّدِنَا مُحَمَّدٍ

الْفَاتِحِ لِمَا أُغْلِقَ،

وَالْخَاتِمِ لِمَا سَبَقَ،

نَاصِرِ الْحَقِّ بِالْحَقِّ،

وَالْهَادِي إِلَىٰ صِرَاطِكَ الْمُسْتَقِيمِ،

وَعَلَىٰ آلِهِ حَقَّ قَدْرِهِ وَمِقْدَارِهِ الْعَظِيمِ.

MU'UJIZAR MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM...Daga cikin abubuwan ban mamaki da s**a gagari hankali ya iyakance su...
14/12/2025

MU'UJIZAR MANZON ALLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM...

Daga cikin abubuwan ban mamaki da s**a gagari hankali ya iyakance su game da rayuwar rayuwar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, Maulana Sheikh Goni Dr Muneer Sheikh Ja'afar Katsina HAFIZAHULLAH yana yawan gaya mamu wasu abubuwa guda biyu cewa:

- Daga mafi girman ayoyi shine Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam ya zo ummiyyi (Ba ya karatu, ba ya rubutu) amma ya zo da Alqur'anin da ya gagari mutanen farko da na ƙarshe, wanda ya tattara labarin mutanen farko da na ƙarshe, ya karantar da abubuwan al'ajabi a cikin shi wanda babu wani mahaluƙi da ya taɓa zuwa da irin sbi.

- Bai ishe ka al'ajabi ba, mutumin da ya tashi mahaifanshi duk sun rasu, amma kuma ya kasance shine mafi kyawawan halaye da ɗabi'u tun daga farkon halittar duniya har zuwa ƙarshen ta, ka kula! Shi ɗin tarbiyyar Allah ne.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da girma yake, Allah ya ƙara ma Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam daraja da wasila.

Sallu Alan-nabiyyil Kareem.

13/12/2025

Alqur'ani wa'azi ne, waraka ne daga cututtukan zuciya shiriya ne, jin kai ne ga muminai..

Ƴan'uwa a riƙe Alqur'ani da kyau.

Jumu'ah Mubarakah21st Jimadal Akhir, 1447 | 12th December, 2025
12/12/2025

Jumu'ah Mubarakah
21st Jimadal Akhir, 1447 | 12th December, 2025

Address

Mani Road Katsina
Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-Asad Education Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Al-Asad Education Foundation:

Share

Category