Crushbeatz 247

Crushbeatz 247 MUZIK NEVER GET LOST! FOR MORE VIDEOS šŸ‘‰ https://www.youtube.com/

23/07/2025

DON ALLAH JAMA’A KUYI MIN SHARING KUMA KUKARANTA INA SON SAKON YA ISA WAJEN YUSUF BUHARI.

Allah yasani ina matukar qaunar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma nayi kokari sosai wajen kulla alaka a matsayin uba da dana, nayi kokari sosai domin sonda nake masa da zato na alkhairi wajen yin takaransa a (2015-2023) saboda a wannan lokacin ina matsayin mutum kuma zan iya bada gudumowa a siyasance.

Duk abokai na idan suna son su batamun rai to suyi magana mara dadi akan buhari a lokacin ake fada dani fushina yake baiyana sosai don irin qaunarda nake masa, ba kuma ina qaunarsa saboda wani abun duniya ba, kawai Allah ne ya doramin sonsa ina masa kallo a matsayin uba kuma shugaba nagari wanda nake masa fatan alkhairi a koda yaushe.

Allah ya dauki ransa ban samu wannan daman ba, Buhari shine shugabanda nake tashi a dare nayi sallah nayi masa adu’a kuma har yanzu inde nayi sallan farinla yana daya daga cikin wanda nake yiwa adu’a neman masa gafara a wajen Allah madaukacin sarki yayi masa rahama da sauran musulmai baki daya,

tunda wan nan alakan nason zama daya daga cikin maku santan sa Allah bai nufa ba, a yanzu ina son don Allah duk wanda yakeda daman hadani da Yusuf Buhari ina son wannan zumuncin da Allah bai nufa zanyi da mahaifinsa ba ina maturkar son yinta dashi.

Ina matukar son hakan sosai ina son nayi alaka dashi ta mutuntawa da girmamawa. Wallahi Tallahi Billahi bana nufin neman alaka dashi don abun duniya, kawai ina son yasanni mudinga mutunci muna waya lokaci zuwa lokaci na samu damar da duk lokacin da nakeson ziyar tansa na samu, ya san ina matukar kau narshi a mastayin masoyin mahaifinsa a wani bangare akwai dan kan taka na jini a tsakaninmu amma dangi ne wanda yayi nisa sosai da sosai wani kakana ya taba fadamin, ina qaunar zuriarsu baki daya inada alaka mai karfi da Hon. Ahmad tsohon hadimin Buhari nasan zan iya samun wannan daman a wajensa domin ya daukeni kaman kaninsa,

amma na zabi yin wanan rubutun a social media ne domin na nunawa duniya irin sonda nakeyiwa Buhari da kuma zuriar sa baki daya, don Allah bayan Bashir Ahmad idan akwai wani wanda yakeda dama mai karfi wanda zai iya tai makona domin ganin wannan burin nawa ya cika a taimaka min don (YUSUF BUHARI) baya social media sosai b***e nasan asalin shafukansa a media ina neman wannan alfarman wajen Al’umma dasu taimaka mun har wannan sakon nawa yaje inda nakeso yaje. Don Allah jama’a karkuyi tunanin kwadayi ne yasa nake neman wannan alakar wallahi kawai ā€˜Kaunace da Allah ya doramin nason Buhari da kuma a halinsa baki daya.

Yana dakyau kaso mutun don Allah badon wani abun duniya ba kuma ance idan kanason mutun kafada masa to nayi hakan ina adu’a Allah yasa sakona yaje kuma Allah yasa mudace, a karshe ina kara adu’a Allah ya jaddada rahamarsa ga tsohon shugabansa kasa Muhammadu Buhari uba a wajen Yusuf, Zarah Hanan Lami Zulaihatu Nafisatu Musa kuma Miji wajen Mamarmu Hajiya. Aisha Buhari. BissalamšŸ™

BabaSadiq āœļø

GASKIYA YAKAMATA KAYI WANI ABU BABA😲BabaSadiq
17/05/2025

GASKIYA YAKAMATA KAYI WANI ABU BABA😲

BabaSadiq

17/03/2023

don't be afraid,_don't lose faith.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Crushbeatz 247 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Crushbeatz 247:

Share