
12/06/2025
SHUGABAN GIDAUNIYAR JINƘAI TA EL-ARABIAN CHARITY FOUNDATION HON MUHAMMAD MUSTAPHA ABDUL YAKAI ZIYARA GIDAN HAJIYA TURERA SHUGABAN MATAN YARBAWAN FUNTUA.
Shugaban Gidauniyar Jinƙai ta El-arabian charity Foundation Funtua Hon Muhammad Mustapha Abdul ya kaiwa Hajiya Turera Funtua ziyara, Hajiya Turera Jigoce akan cigaban Mata marasa ƙarfi da marayu da kuma cigaban jam'iyyar APC da Matasan Funtua, wannan ziyara ce ta Bangirma,Barka da Sallah, da kuma sada zumunci Tare Da Gabatar mata da Wannan Gidauniya mai Albarka ta El-arabian charity Foundation a matsayin uwar Gidauniyar na dindindin.
Hajiya Turera taji daɗin ziyarar kwarai da gaske kuma ta sanyawa Wannan Gidauniya Albarka tareda ba yadda dimbin shawarar wari na yadda Gidauniyar zataci Gaba Da Gudanar Da ayyukan ta na Alkairee, Inda aka sake bayyana mata irin namijin kokarin da Gidauniyar takeyi akan Marasa lafiya, marayu da kuma ɓangaren ilimi da masu buƙata ta musamman.
A baya-bayan nan Gidauniyar ta El-arabian charity Foundation ta kashe naira milliyan 5 da Wani abu ₦5,000,000+ wajen taimakawa marasa lafiya da kuɗin magani da kuma biyan kuɗin manyan ayyuka na masu lalura ta musamman, Wannan bashi ne karon farko ba dama tun abaya Gidauniyar tana kokari wajen taimakawa marasa ƙarfi na kuɗin Abinci da sutura, domin Gidauniyar tasha ɗaukar nauyin karatun yara ƙanana da taimakon yan gudun hijira.
Itama anata bangaren k**ar sauran waɗan da ya ziyarta ta sake bada shawara ga matasa Masu Ra'ayin Siyasa Mu yi ƙoƙari mu riƙa kyautata mu'amala a tsakanin mu da kuma sauran mutane kada mu bari siyasa tasa mu riƙa s**ar junar mu saboda ana yiwa waɗanda muke tare da su adawa.
Hajiya Turera ta tabbatar da goyan bayanta ga Wannan tafiya da kuma cewa duk lokacin da ake bukatar wata shawara daga gare ta kaitsaya atuntuɓeta zata bada gudunmawa 100% musamman akan cigaban wannan Gidauniya ta El-arabian charity Foundation Funtua, ta tabbatar da cewa Irin wadannan matasa ne ake baiwa jagoranci na Al'umma ba ƴan tayi daɗiba.