Yan gida

Yan gida Salam

AMFANIN TSAMIYA DA KUMA ILLOLINTA GA LAFIYA. Tsamiya na daya daga cikin 'ya'yan itatuwan da ake amfani dasu a kasar Haus...
01/10/2023

AMFANIN TSAMIYA DA KUMA ILLOLINTA GA LAFIYA.



Tsamiya na daya daga cikin 'ya'yan itatuwan da ake amfani dasu a kasar Hausa k**a daga fannin abinci da kuma magani .Tana da amfani mai tarin yawa haka kuma tana da wasu illoli musamman idan aka sha ba'a bisa ka'ida ba,tana kuma da illa ga wasu daidaikun mutane,domin akoi mutanen da take tadoma cutukkan iska k**ar na kumburi ko qaiqayi da kurajen jiki.



Ana amfani da tsamiya wajen sarrafa kayan sha,inda a yau wajaje dadama wasu kan qullata a leda bayan sun tace sun gaurayata da s**ari sai su sakata a na'urar sanyi (refrigegrator).
Wasu kuma sun dauketa a matsayin magani ko a hada abinci da ita domin akan yi kunun tsamiya da kuma tuwon tsamiya a wasu yankuna k**ar a Zuru,ri6a da suru dake a jihar kebbi.



matsalolin da tsamiya ke magancewa.Ga kadan daga cikinnsu :

1.Cushewar ciki da rashin yin bahaya.
2.Ciwon ciki.
3.Tashin zucya ga masu juna biyu.
4Tsutsar ciki.
5.Matsalolin da s**a shafi na hanta (liver da kuma madaciya (bile)
6.mura da zazza6i.
7.Tana wanke dattin ciki da kuma cushewar hanji
8.Ana amfani da ganyenta wajen magance cutukkan daji (cancers)
9.Ana tafasa ruwanta ayi wanka dasu dan magance ciwon ga6o6in jiki.(arthriries)
10.Tana saka cin abinci,a duk sanda ka ci abinci ka sha tsamiya to za kayi saurin jin yunwa.


Illolinta sun hada da :

Tsamiya tana iya haifarda illa ga masu ciwon s**ari (diabeties patients) saboda tana illa ga adadin yawan s**arin dake a cikin jini.

Haka kuma ga wadanda za a yiwa fida (surgery) to kada su sha tsamiya a kalla makonni biyu kamin ayi tiyata.

Gamai fama da rama,yawan shan tsamiya na iya kara sanya ramar saboda tana rage qiba sosai.

A guji shan tsamiya a sanda ake shan
wasu magunna rukunin Ibumol da aspirin.
Tsamiya tana rage shawar namiji,idan matsananciyar shawa ta yiwa namiji yawa to ya lazimci shan tsamiya zaiji leqes.



Idan kiba ta yiwa mutum yawa a jiki kuma yana son ya rage kibar to ya zanka shan tsamiya amma a san adadin da za a sha.

Mai fama da gembon

Address

Batsari
Katsina
BABAYYE

Telephone

+2348104151092

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yan gida posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category