12/06/2026
Ga fassarar jawabin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na ranar Dimokradiyya.
SAKON SHUGABA BOLA AHMED TINUBU A RANAR DIMOKURAƊIYYA TA 12 GA YUNI, 2026
'Yan uwana ’yan Najeriya,
A yau muna bikin dimokuraɗiyya da kuma juriyar ruhin ɗan Najeriya. Tsawon shekaru 27 a jere tun daga ranar 29 ga Mayu, 1999, al’ummarmu ta ci gaba da zaɓar shugabanninta ta hanyar akwatin zaɓe, tana ganin sauyin mulki cikin lumana, tare da warware sabani a kotuna da majalisun dokoki maimakon ta hanyar tashin hankali.
Dimokuraɗiyyarmu ba cikakkiya ba ce, amma tamu ce. Don haka wajibi ne mu ci gaba da kare ta tare da ƙarfafa ta.
A kwanaki masu zuwa, jihohin Ekiti da Osun za su gudanar da zaɓe. Ina kira ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), jami’an tsaro da dukkan masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa an gudanar da waɗannan zaɓuka cikin lumana da gaskiya. Dimokuraɗiyya tana raunana idan jama'a s**a rasa amincewa da tsarin zaɓe.
Ga Majalisar Tarayya, Bangaren Shari’a, ’Yan Jarida da Kungiyoyin Farar Hula: ku ne ginshiƙan da ke kare jamhuriyarmu. Ku ci gaba da s**ar gwamnati idan ya dace, ku yi sabani da ni idan kuna da hujja, amma kada ku daina yarda da Najeriya.
Ga matasanmu, Najeriya ita ce gidanku kuma makomarku. Ku gina ta a nan, ku kirkiri sababbin fasahohi a nan, ku yi aiki a nan, ku kuma kada kuri’a a nan. Manyan ƙasashe ba su samu ci gaba ba saboda mutanen da s**a gudu daga matsaloli, sai dai saboda waɗanda s**a tsaya s**a warware su.
Ina miƙa gaisuwa ta musamman ga dakarunmu, jami’an ’yan sanda da jami’an tsaro saboda sadaukarwar da suke yi. Haka kuma ina godiya ga sarakunan gargajiya, malamai da shugabannin al’umma saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da sulhu.
A yau muna tunawa da juriyar ’yan Najeriya da s**a ƙi yin kasa a gwiwa wajen kare ’yanci da dimokuraɗiyya. Muna girmama waɗanda s**a fuskanci tsangwama, kurkuku, gudun hijira har ma da rasa rayukansu domin al’ummomin gaba su more dimokuraɗiyya.
Muna kuma tunawa da shugabannin ƙwadago, ’yan jarida, masu fa