05/09/2026
An shiga jimami da alhini biyo bayan rasuwar Jamila Saleh Gwarzo, wadda ta rasu bayan fama da rashin lafiya.
Wani abokin aikinta na tsawon shekaru ya bayyana cewa bai taɓa samun saɓani da marigayiyar ba tsawon lokacin da s**a yi suna aiki tare, yana mai bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi da ya girgiza shi.
Ya ce a ranar Litinin ya kira wayarta domin ta haɗa shi da wani maƙocinta, amma lokacin da ya ji muryarta ya fahimci cewa ba ta cikin ƙoshin lafiya. Jamila ta sanar da shi cewa ba ta da lafiya.
Ya ƙara da cewa nan take ya tashi ya zarce gidansu domin duba lafiyarta, inda ya samu damar haɗa ta da Uwargidansa ta waya. Sun gaisa, sannan marigayiyar ta yi musu addu’a.
Sai dai, kamar yadda ya bayyana, bai san cewa ita ma a lokacin tana buƙatar addu’a ba, domin a daren wannan rana ne ya samu labarin rasuwarta.
An gudanar da jana’izar marigayiyar a Babban Masallacin Juma’a na garin Gwarzo, inda ‘yan uwa, abokan aiki da sauran al’umma s**a halarta domin yi mata addu’a.