26/08/2024
YAU RANAR HAUSA 26/8/2024
Ranar Hausa (Ko kuma ) da turanci Hausa Day, Rana ce da aka keɓance domin nuna muhimmancin harshen Hausa, da tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali akan irin ƙalubalen da harshen yake fuskanta.an fara bikin farko a shafukan sada zumunta musamman ta shafin twitter da niyyar hada L1 da L2 na masu magana da harshen Hausa. An zaɓi ranar 26 ga watan Augusta domin tuna ranar da aka ƙirƙiro haruffan "ƙ" da "ɗ" da "ɓ" wanda babu su a haruffan Turanci.
A Yayin bikin na cika shekara 5, mutane fiye da 400,000 s**a gudanar da bikin ta yanar gizo da wasu kasashen da Hausawa suke zaune a sassa daban daban na duniya irinsu Faransa, Amurka, Kamaru, Ghana, Nijar, da Najeriya, kuma a irin wanan rana hausawa na duniya na cika shafukan zumunta da da zantuttuka masu nuna Alfahari da yarensu, wasu wajajen s**an shirya bukukuwa a wanan rana.
Asali
Ranar Hausa dai ta samo asali ne a shekarar 2015 bayan ɗan jarida Abdulbaqi Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta s**a ayyana ranar a matsayin ranar da masu magana da harshen Hausa za su haɗu su tattauna ci gaba da kalubalen da harshen ke fuskanta a karni na 21. Kuma ana bikin Ranar Hausar ne a 26 ga watan Agustan kowace shekara a Duniya.
Muhimmanci
An ƙirƙiri wannan rana ce domin duba da mahinmancin ta ko kuma mahinmancin da zata bada. Makasudin wannan rana dai itace. Domin ciyar da yaren hausa gaba, al'ummar su, al'adunsu da kuma samun hadin kan hausawa a duniya baki daya.
A kowace shekara idan ranar ta zagayo ma'abota shafukan sada zumunta ke yin amfani da tambarin domin tattaunawa da yin muhawara.
Nasarorin da aka samu
Wadanda s**a ƙirƙiro wannan ranar sun ce sun yi haka ne domin tuna wa da al'ummar Hausa game da muhimmancin harshen da yadda za a ciyar da shi gaba.
Sannan kuma ranar ta kasance a matsayin wata rana da ake ƙalubalantar al'ummar Hausawa domin fiddo da sabbin bincike da nazarce-nazarce domin habbaka harshen na Hausa.
Babbar nasarar da za a ce