18/09/2026
Bafa barci suke ba😥😥
Mutuwa s**ai a hannun hukumar Civil Defense a jihar Niger. Laifin su shi ne sun kasance masu hakar ma'adanai ba bisa kaida ba acewar gwamnati.
Su ba barayi ba, su ba yan ta'adda ba, amma yanzu duka wadannan matasan da gwamnati ta kasa basu ingantacciyar rayuwa, ta kasa basu gobe mai kyau, sun fita su nema karshe ga inda s**a samu kansu.
Hukumar da yakamata ta tsare rayukan Alumma ita tai sanadiyyar mutuwar su, kuma fa babu abunda za ai akai, muna nan da ku,
Kwanannan baya ma an zargi wani jami'in Dansada mai matsayin DPO ada mikawa miyagu wata mata hakan yayi sanadiyyar mutuwar ta, wani mataki kukaji an dauka akan shi?
Allah swt yasa mudace.
Allah ya jikan ku da gafara!🙏✍️
Yunusa Umar Bn Umar