Alaqa Media Ltd

Alaqa Media Ltd News, Information, Entertainment, Advert Placement.

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Shugabar Mata Ta Jam'iyyar PDP Ta Karamar Hukumar Bakori A Jihar Katsina Ta Rasu Alla...
28/09/2025

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Shugabar Mata Ta Jam'iyyar PDP Ta Karamar Hukumar Bakori A Jihar Katsina Ta Rasu

Allah Ya Yi Wa Sananniyar Ƴar Siyasa Kuma Shugabar Mata Ta Jam'iyyar PDP A Karamar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, Hajia Iklima Musa Rasuwa a Yau Lahadi. Bayan ta Samu Hatsarin Mota A Kwanakin Baya,

Allah Ya Jikanta Da Rahama!

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

DA DUMI-DUMI: NRC za ta dawo da jirgin Abuja–Kaduna daga ranar 1 ga watan Oktoba 2025Hukumar Jirgin Ƙasa ta Najeriya (NR...
28/09/2025

DA DUMI-DUMI: NRC za ta dawo da jirgin Abuja–Kaduna daga ranar 1 ga watan Oktoba 2025

Hukumar Jirgin Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta sanar da dawo da zirga-zirgar jirgin Abuja–Kaduna daga ranar 1 ga watan Oktoba bayan kammala gyare-gyare a tashar Asham.

Hukumar ta ce ta mayar da kuɗin tikiti ga fasinjoji 512 daga cikin 583 da s**a shiga jirgin da ya samu hatsari a ranar 26 ga watan Agusta.

LIKE // SHARE & FOLLOW US => Alaqa Media Ltd

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN) ta dakatar da jigilar mai da iskar gas zuwa tashar Dangote saboda...
27/09/2025

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN) ta dakatar da jigilar mai da iskar gas zuwa tashar Dangote saboda rikici da kamfanin kan sallamar wasu ma’aikata da s**a shiga ƙungiya.

Dangote ya ce sallamar ta shafi sake tsari ne, ba tare da tauye hakkin ma’aikata ba.

Wa kuke goyon baya Dangote ko PENGASSAN?

DA DUMI-DUMI: NAHCON ta rage kuɗin Hajji zuwa N8.1m a Najeriya Hukumar Hajj ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da sabon kuɗin Haj...
27/09/2025

DA DUMI-DUMI: NAHCON ta rage kuɗin Hajji zuwa N8.1m a Najeriya

Hukumar Hajj ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da sabon kuɗin Hajji na shekarar 2026 ga masu niyyar zuwa Makka.

Daga cikin sanarwar, an bayyana cewa mutanen da za su tashi daga yankin Maiduguri-Yola (jihohin Borno, Yobe, Adamawa da Taraba) za su biya N8,118,333.67, yayin da waɗanda suke a sauran jihohin Arewa za su biya N8,244,813.67.

Sai dai kuma, ga mutanen kudu, za su biya N8,561,013.67.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya ce ana rage makamancin ₦200,000 daga abin da aka biya a shekarar da ta gabata.

Ya kuma gargadi masu sha’awar zuwa Hajji su kammala biyan su kafin 31 ga Disamba, 2025.

Wa kuke fatan Allah ya kira Hajjin Bana?

DA DUMI-DUMI: Dangote Refinery ya dakatar da siyar da man Fetur a Naira Kamfanin Dangote Refinery ya dakatar da siyar da...
27/09/2025

DA DUMI-DUMI: Dangote Refinery ya dakatar da siyar da man Fetur a Naira

Kamfanin Dangote Refinery ya dakatar da siyar da fetur a farashin naira daga Litinin, 28 ga Satumba, 2025, saboda ƙarancin ribar da yake samu a tsarin “Crude-for-Naira” wato sayen danyen mai a Naira.

Wannan na zuwa ne bayan korar ma’aikata sama da 800 da kamfanin ya yi wanda ya jawo s**a daga ƙungiyoyin ma’aikata, tare da yiwuwar tasiri kan farashin man fetur a kasuwa.

Ya kuke ganin wannan lamari?

DA DUMI-DUMI: Ba za a ci gaba da mulkin soja a Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea ba -inji Shehu Sani Tsohon Sanatan Ka...
27/09/2025

DA DUMI-DUMI: Ba za a ci gaba da mulkin soja a Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea ba -inji Shehu Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea ba za su ci gaba da zama karkashin mulkin soja ba. Ya bayyana cewa a karshe dole su koma ga mulkin farar hula da gudanar da zabe, yana mai gargadin cewa mulkin soja na barazana ga dimokuradiyya a Afirka.

Da mulkin Soja da na farar hula wanne kuka fi so?

Da dumi'dumi: Dangote ya kori duk ma'aikatan sa 'yan Najeriya dake matatar man fetur saboda yawan Sata.Lagos, Alhamis, 2...
26/09/2025

Da dumi'dumi: Dangote ya kori duk ma'aikatan sa 'yan Najeriya dake matatar man fetur saboda yawan Sata.

Lagos, Alhamis, 25 ga Satumba, 2025

Wani babban lamari ya faru a Matatar Mai ta Alhaji Aliko Dangote, inda kamfanin ya sanar da sallamar dukkan ma’aikatansa ƴan Najeriya daga aiki nan take.

A cikin wata takarda da Babban Manajan Janar na Sashen Kula da Ma’aikata (Human Asset Management), Mista Femi Adekunle ya sanyawa hannu, an bayyana cewa an dauki matakin ne sakamakon rahotanni masu yawa na ɓarna da s**a janyo matsaloli masu tsanani na tsaro a wasu sassan matatar.

Takardar ta ce: “Daga daren Alhamis, 25 ga Satumba, 2025, ba za mu sake buƙatar ayyukan ku ba.”

An umarci ma’aikatan da su mika dukkan kayan kamfanin da suke hannunsu ga shugabanninsu kai tsaye sannan su karɓi takardar ajiye aiki. Haka kuma, za a sanar da ranar karshe da za a kammala tsari daga baya.

Sashen kudi na kamfanin na da kwafin takardar, kuma an umurce shi da ya lissafa dukkan hakkoki da ribobin ma’aikatan bisa sharuddan aikin su, sannan a biya su abin da ya dace bayan sun kammala cike-ciken sallama.

Kamfanin ya kuma yi godiya ga ma’aikatan bisa hidimar da s**a bayar a lokacin da s**a yi aiki tare da su.

Gwamnatin Jihar Katsina zata gyara makarantun firamare 340 gaba ɗaya (full renovation) haɗin guiwa da ƙananan hukumomin ...
25/09/2025

Gwamnatin Jihar Katsina zata gyara makarantun firamare 340 gaba ɗaya (full renovation) haɗin guiwa da ƙananan hukumomin jihar.

Shin kun gamsu da ayyikan Gwamnatin Dikko Radda?

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, ya naɗa fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara a matsayin Sarkin Wakar Ƙasar Haus...
25/09/2025

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, ya naɗa fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara a matsayin Sarkin Wakar Ƙasar Hausa.

Wannan na cikin wani saƙo da mataimakin mamawaƙin na musamman kan harkokin watsa labarai ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis.

DA DUMI-DUMI: “Yarabawa za su riƙe manyan mukamai a gwamnatina - ba zan fi baiwa Hausa-Fulani fifiko ba” -inji Atiku Abu...
24/09/2025

DA DUMI-DUMI: “Yarabawa za su riƙe manyan mukamai a gwamnatina - ba zan fi baiwa Hausa-Fulani fifiko ba” -inji Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ya zama Shugaban Ƙasa a 2027, yawancin manyan mukamai za su koma hannun Yarabawa ne, yana ƙaryata zargin cewa ƙabilar Hausa-Fulani ne za su yi rinjaye a gwamnatinsa.

A wata sanarwa da ya fitar Atiku ya ce ƙabilar Yoruba na da “matsayi na musamman” a zuciyarsa saboda alaƙa ta iyali da soyayya. Ya ce ba gaskiya ba ne a cewa idan ya hau karagar mulki, zai baiwa Hausa-Fulani fifiko "domin mutanen Yoruba “su ne iyalina wanda na zauna tare da su.” Muryoyi ta ruwaito Atiku ya kuma yi alfahari da kasancewar matarsa Bayarabiya daga jihar Osun, da yadda dangantaka da iyali ya ƙara masa kusanci da al’ummar Yoruba.

Za a fara samar da sabon maganin riga-kafin kare mutum daga kamuwa da cutar HIV, a ƙasashe masu ƙaramin karfi, a kan far...
24/09/2025

Za a fara samar da sabon maganin riga-kafin kare mutum daga kamuwa da cutar HIV, a ƙasashe masu ƙaramin karfi, a kan farashi mai rahusa daga shekarar 2027.
Maganin allura mai suna lenacapavi wanda a ƙasashen da s**a ci gaba ake sayarwa da dubban daloli a duk shekara, zai koma dala 40 kacal a kowace shekara.
Wannan sabuwar hanyar riga-kafin za ta bai wa miliyoyin mutane damar ci gaba da rayuwa da kuma kauce wa haɗarin kamuwa da cutar HIV.
Za a riƙa samar da maganin mai rahusa a Indiya, sannan kuma za a watsa shi a duniya ta hannun gamayyar wasu ƙungiyoyin kiwon lafiya a ƙasashe guda 120.

Uwargidan shugaban Najeriya Remi Tinubu, ta sami kyautar Biliyan Ashirin da Miliyan Dari Hudu da Hamsin da Shida, da dub...
23/09/2025

Uwargidan shugaban Najeriya Remi Tinubu, ta sami kyautar Biliyan Ashirin da Miliyan Dari Hudu da Hamsin da Shida, da dubu Dari da Tamanin da Takwas da Dari Tara da Ashirin da Hudu da kwabo Tis'in da Uku a asusun da ta bude albarkacin zagayowar ranar haihuwarta.

Mai dakin ta Tinubu ta ce za ta yi amfani da wadannan kudade domin ci gaba da ginin dakin karatu da tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari ya fara.

Address

Sabon Titin Kwado
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alaqa Media Ltd posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share