A M Hausa

A M Hausa News, Information, Entertainment, Advert Placement.

Takaitattun Labaran  Safe daga A M Hausa na 12 Yuni 2026🇳🇬 Najeriya •Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga masu ...
12/06/2026

Takaitattun Labaran Safe daga A M Hausa na 12 Yuni 2026

🇳🇬 Najeriya
•Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga masu ɗaukar nauyin ta’addanci da su mika wuya ko su fuskanci matakan gwamnati.
•Majalisar Dokoki ta ƙasa ta amince da kudirin kafa ‘yan sandan jihohi domin ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar.
•Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Dimokuraɗiyya (12 ga Yuni) a matsayin ranar hutu ta ƙasa.
•Sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan maboyar ‘yan ta’adda a jihar Borno, inda aka ce an kashe wasu kwamandoji da mayaƙa.

Jihar Katsina
•Majalisar Dattawa ta nuna damuwa kan yunƙurin yin sulhu da ‘yan bindiga a wasu jihohi ciki har da Katsina.
•Dikko Umaru Radda ya bayyana sabon matsayi game da batun sulhu da ‘yan bindiga yayin da ake ci gaba da kokarin dawo da zaman lafiya a jihar.
•Jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukan daƙile hare-haren ‘yan bindiga a yankunan da abin ya fi shafa.

Wane labari ne yafi jan hankalin ka?

Ga taƙaitattun manyan labarai na yau, 11 ga Yuni 2026:🇳🇬 Najeriya •Gwamnatin Tarayya ta ce kuɗaɗen ajiya ƙasar waje (ext...
11/06/2026

Ga taƙaitattun manyan labarai na yau, 11 ga Yuni 2026:

🇳🇬 Najeriya
•Gwamnatin Tarayya ta ce kuɗaɗen ajiya ƙasar waje (external reserves) ya kai dala biliyan 50.12, wanda shine mafi girma cikin kusan shekaru 17.
•Ana ci gaba da muhawara kan samar da ‘yan sandan jihohi, yayin da Majalisar Wakilai ke duba akan batun.
•Gwamnati ta samu yarjejeniya da ƙasar Habasha domin sauƙaƙa dawo da wasu fursunonin Najeriya da ke can.
•Ana bincike kan hatsarin jirgin ƙasa na Warri–Itakpe da ya faru kwanan nan.
•Rahotanni sun nuna gwamnati na ƙara mayar da hankali kan yaƙi da zazzabin cizon sauro da kuma inganta lafiyar al’umma.

A Jihar Katsina
•Batun tsaro da hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da jan hankali. Wani rahoto ya nuna yadda wasu shugabannin al’umma a ƙaramar hukumar Kurfi s**a shiga sulhu da wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga, lamarin da ya taimaka wajen rage hare-hare da sace-sace a wasu yankuna.
•A fagen siyasa, ana ci gaba da sauye-sauyen jam’iyyu kafin zaɓukan gaba, inda aka ruwaito rikice-rikice da sauyin sheƙa a tsakanin wasu ‘yan siyasa a jihar.

Wane labarin ne yafi jan hankalin ku?

Yau ruwan sama ya yi ƙarfi a Katsina har ya haddasa ambaliya a wasu wurare. Yaya halin yankinku? Shin an samu matsala ko...
10/06/2026

Yau ruwan sama ya yi ƙarfi a Katsina har ya haddasa ambaliya a wasu wurare. Yaya halin yankinku? Shin an samu matsala ko komai lafiya?

Takaitattun Labaran Safe na 10 Yuni 2026🇳🇬 Najeriya1. IMF ta yi gargadi kan yarjejeniyar bashin dala biliyan 5Asusun Lam...
10/06/2026

Takaitattun Labaran Safe na 10 Yuni 2026

🇳🇬 Najeriya
1. IMF ta yi gargadi kan yarjejeniyar bashin dala biliyan 5
Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya nuna damuwa kan wata yarjejeniyar kuɗi da Najeriya ta kulla, yana mai cewa irin waɗannan yarjejeniyoyi na iya haifar da haɗarin kuɗi idan ba a gudanar da su kan cikakken bayani ba
1. Sojoji sun kuɓutar da mutane 360 daga hannun Boko Haram
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto mutane 360 da aka yi garkuwa da su a yankin tsaunukan Mandara na Jihar Borno. 
3. Annobar kwalara na ci gaba da yaɗuwa a Borno
Rahotanni sun nuna cewa mutane 74 sun rasu yayin da dubban mutane s**a kamu da cutar kwalara a wasu sassan Jihar Borno. 
4. Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 10 domin shirin kariya daga Ebola
An kafa kwamitin gaggawa domin shirin tunkarar yiwuwar barkewar cutar Ebola a Najeriya. 
5. Majalisar Dattawa ta nemi farfaɗo da masana’antar yadi
Majalisar ta bayyana muhimmancin dawo da masana’antar yadi domin samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki. 

📍 Jihar Katsina
1. Gwamnatin Katsina na ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda akayi garkuwa da su
Gwamnatin Dikko Umaru Radda ta bayyana kwarin gwiwa cewa za a samu nasara wajen ceto Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su. 
2. Harin ’yan bindiga ya jawo ƙaura a wasu yankuna
Rahoton ƙaura ya nuna cewa hare-haren da aka kai a Bakori da wasu yankuna sun tilasta wa iyalai da dama barin gidajensu. 
3. An ceto mutum 32 daga hannun masu garkuwa
Dakarun tsaro tare da jami’an sa kai sun samu nasarar ceto mutane 32 a wani samame da aka gudanar a jihar.

4. Ana ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya
Wasu al’ummomi a Katsina sun samu raguwar hare-hare bayan tattaunawar sulhu tsakanin shugabannin al’umma da wasu ƙungiyoyin ’yan bindiga. 

Wane labari ne yafi Jan hankalin ka?

09/06/2026

Barkan ku da wannna lokaci jama’ar ALAQA MEDIA.

Bayan ɗan lokaci ba tare da wallafa abubuwa ba, mun dawo domin ci gaba da kawo muku sahihan labarai, bayanai masu amfani da shirye-shirye na musamman.

Ku kasance tare da mu gobe da safe domin samun takaitattun manyan labarai da sauran shirye-shirye.

ALAQA MEDIA- Muryar Al’umma, Gadar Bayanai.

Da ɗumi-ɗumi: Rahotanni na cewa wasu fusatattun matasa a unguwar Jan Bulo dake jihar Kano sun lakadawa Jarumi Musa Mai S...
01/04/2026

Da ɗumi-ɗumi: Rahotanni na cewa wasu fusatattun matasa a unguwar Jan Bulo dake jihar Kano sun lakadawa Jarumi Musa Mai Sana’a dukan tsiya da kuma jifar shi Sakamakon Tallan Tinubu

Gwamna Radda Ya Naɗa Sabbin Kwamishinoni Da Mataimaka Na MusammanYau Litinin, 2 ga watan Maris na shekarar 2026, gwamnan...
02/03/2026

Gwamna Radda Ya Naɗa Sabbin Kwamishinoni Da Mataimaka Na Musamman

Yau Litinin, 2 ga watan Maris na shekarar 2026, gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda yayi sabbin naɗe-naɗe a gwamnatinsa don ƙara inganta gudanarwar gwamnati.

Naɗe-naɗen sun haɗa da:

Kwamishinoni guda biyu:

1. Alhaji Muhammad Sani Ali Ahmad
2. Alhaji Mannir Ayuba Sullubawa

Naɗin su zai tabbata ne bayan majalisar dokoki ta tantance su

Managing Director guda daya:

1. Barrister Suleiman Mohammed Namadi – Managing Director, Katsina State Erosion and Watershed Management Agency

Senior Special Assistants guda uku:

1. Hajiya Jamila Salman – Senior Special Assistant
2. Alhaji Ibrahim Danjuma – Senior Special Assistant
3. Hon. Muddasir Mati – Senior Special Assistant

Special Assistants guda biyu:

1. Alhaji Musa Dankawu – Special Assistant
2. Alhaji Abdulfatah Kafur – Special Assistant

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government
March 2, 2026.

Address

Sabon Titin Kwado
Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when A M Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share