World News Post

World News Post Muna tabbatar da Sahihancin Labarai

INEC Ta Kammala Sanar da Sakamakon Kananun Hukumomi 30 Na Zaɓen Gwamnan jihar Osun, Jam'iyyar Accord ce kan gabaHukumar ...
16/08/2026

INEC Ta Kammala Sanar da Sakamakon Kananun Hukumomi 30 Na Zaɓen Gwamnan jihar Osun, Jam'iyyar Accord ce kan gaba

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta kammala bayyana Sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Osun na 2026 daga ƙananan hukumomi 30, inda jam’iyyar Accord ta samu gagarumar nasara a kan APC.

Jimillar kuri’u:

— Accord: 511,067
— APC: 444,815
— ADC: 17,180

Hakan ya sa Accord ke gaban APC da tazarar kuri’u 66,252.

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Gusau da Tsafe daga jihar Zamfara Hon. Kabiru Ahmadu Mai Palace zai sake raba...
15/08/2026

Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Gusau da Tsafe daga jihar Zamfara Hon. Kabiru Ahmadu Mai Palace zai sake raba wa ƴan mazaɓarsa waɗannan motoci a matsayin tallafi a garesu, inda aka bayyana cewa daga cikin waɗanda za su amfana har da yaransa na siyasa da s**a yi masa hidima.

YANZU-YANZU: An Hango Tinubu Yana Tafiya Da Ƙafa Zuwa Ofis Ba Tare da Ayarin Motoci Ba, Lamarin da Ya Sake Tabbatar da M...
11/08/2026

YANZU-YANZU: An Hango Tinubu Yana Tafiya Da Ƙafa Zuwa Ofis Ba Tare da Ayarin Motoci Ba, Lamarin da Ya Sake Tabbatar da Maganganun Shugaban NRS Na Baya

Kungiyar Triple T Kannywood Ta Ziyarci Mai Girma Gwamnan Jahar Jigawa Mallam Umar Namadi Danmodi Yau a Gidan Gwamnatin J...
10/08/2026

Kungiyar Triple T Kannywood Ta Ziyarci Mai Girma Gwamnan Jahar Jigawa Mallam Umar Namadi Danmodi Yau a Gidan Gwamnatin Jahar Jigawa.

Yadda aka gudanar da taron Maulidin Sheihu Ahamdu Tijjani wanda ya gudana a gidan Sarkin Kano Dake Nassarawa wanda Mai M...
10/08/2026

Yadda aka gudanar da taron Maulidin Sheihu Ahamdu Tijjani wanda ya gudana a gidan Sarkin Kano Dake Nassarawa wanda Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado CFR CNOL JP ya kasance Mai masaukin baki.

HOTUNAYadda Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya kai ziyara ɗakin tiyata na Babban Asibitin General dake cikin ga...
08/08/2026

HOTUNA

Yadda Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya kai ziyara ɗakin tiyata na Babban Asibitin General dake cikin garin Katsina, don ganin yadda aka sabunta shi tare da saka kayan aiki, da kuma wasu ɓangarorin asibitin domin inganta ayyukan tiyata da sauran ayyukan asibitin.

Yadda Tawagar Amare 1,500 da angwayen 1,500 wanda aka yi wa auren Gata, s**a shiga Gidan Gwamnatin jihar Kano, inda Gwam...
08/08/2026

Yadda Tawagar Amare 1,500 da angwayen 1,500 wanda aka yi wa auren Gata, s**a shiga Gidan Gwamnatin jihar Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf zai jagoranci gudanar da Walimar Aurensu a yau Asabar.

📷: AKY

Da Dumu-Ɗumi:- Dr. Mustapha zai fice daga ADC ya koma APC a katsina Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustaph...
08/08/2026

Da Dumu-Ɗumi:- Dr. Mustapha zai fice daga ADC ya koma APC a katsina

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha Inuwa zai fice daga ADC ya koma APC da magoya bayansa domin tallata tazarcen Tinubu a zaben 2027 a Katsina

Katsina Reporters ta ruwaito cewa Dr. Mustapha Inuwa yayi kaurin suna wajen s**a da caccakar gwamnatin APC musammam kan matsalar tsaro a Katsina

Mustapha Muhammad Inuwa ya cimma wannan matsayar ne bayan wata ganawa da Tinubu a makon nan.

Ya kuke kallon wannan batu?

sources Katsina reporters

Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Babban Asibiti na Farko a Tarihin Ƙaramar Hukumar ZangoA ranar Alhamis, 6 ga Agusta, 2026, G...
06/08/2026

Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Babban Asibiti na Farko a Tarihin Ƙaramar Hukumar Zango

A ranar Alhamis, 6 ga Agusta, 2026, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya ƙaddamar da sabon Babban Asibiti (General Hospital) na Zango, wanda shi ne babban asibiti na farko da aka taɓa kafawa a tarihin Ƙaramar Hukumar Zango.

A jawabin maraba, Kwamishinan Lafiya na Jihar Katsina, Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana aikin a matsayin wani babban ci gaba a ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunkasa tsarin kiwon lafiya da kuma inganta samar da ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.

A nasa jawabin, Gwamna Radda ya fara da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa bai wa gwamnati damar kammala wannan gagarumin aiki, wanda aka samu ta hanyar daga darajar tsohuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Matakin Farko (Comprehensive Healthcare Centre - CHC) ta Zango zuwa cikakken Asibiti.

Gwamnan ya bayyana cewa, an tanadi asibitin da ingantattun kayan aiki na zamani domin samar da ayyukan jinya da tiyata masu inganci, lamarin da zai rage yawan tura marasa lafiya zuwa asibitoci masu nisa tare da inganta lafiyar al’ummar Zango da maƙwabtan ƙananan hukumomi.

Ya jaddada cewa harkar lafiya na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta bai wa fifiko, inda ya lissafo muhimman nasarorin da aka samu cikin shekaru uku da s**a gabata.

Nasarorin sun haɗa da daga darajar cibiyoyin kiwon lafiya (CHC) guda huɗu zuwa Manyan Asibitoci, ci gaba da inganta wasu cibiyoyi, gyaran manyan asibitoci da ɗakunan tiyata, farfaɗo da sama da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 280, ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya 804 aiki, gina cibiyar wankin ƙoda ta zamani (Dialysis Centre), kafa cibiyar sarrafa magunguna, da kuma faɗaɗa samar da wutar lantarki ta hasken rana a asibitocin gwamnati.

Haka kuma, Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara shirin horas da likitoci (Medical Residency Training) a fannoni shida na likitanci a manyan asibitocin jihar. Ya kuma bayyana cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ɗaliban fannin likitanci a jami’o’in cikin gida da na ƙasashen waje domin magance ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan lafiya.

Tun da farko, Babban Manajan Hukumar Kula da Asibitocin Jihar, Dr. Muhammad Nazir, ya tabbatar da cewa za a gudanar da sabon asibitin cikin inganci da kwarewa domin samar da ayyukan lafiya ga al’umma.

A saƙon fatan alheri da ya gabatar, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Dakta Bishir Gambo Saulawa, ya yaba wa Gwamna Radda bisa ci gaba da zuba jari a fannin kiwon lafiya da sauran sassan ci gaban jihar, yana mai bayyana ƙaddamar da asibitin a matsayin cika wani muhimmin alƙawarin gwamnati na inganta rayuwar al’umma.

A nasa jawabin godiya, Shugaban Ƙaramar Hukumar Zango, Hon. Babangida Yardaje, ya miƙa godiyarsa ga Gwamnan bisa kafa wannan asibiti mai tarihi, tare da tabbatar masa da cewa al’ummar yankin za su ci gaba da ba da cikakken goyon baya wajen kula da kayan aikin asibitin da tabbatar da dorewar ayyukansa.

A ƙarshe, Gwamna Radda ya yi kira ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Zango da maƙwabtan yankuna da su kare wannan katafaren asibiti tare da ba ma’aikatan lafiya cikakken haɗin kai domin tabbatar da ingantaccen aikin kula da lafiyar jama’a.

Taron ya samu halartar kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Rt. Hon Nasir Yahya Daura, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Hon Abdulkadir Mamman Nasir, National Legal Adviser na jam’iyyar APC, Barr. Murtala Aliyu Kankia, kwamishinan yada labarai, Dr. Bala Salisu Zango, yan takarkari na jam’iyyar APC, Shuwagabannin Kananan Hukumomi, yan majalisar dokoki, yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

August 6, 2026.

‎Labari Cikin Hotuna‎Dr. Haruna Maiwada ya ba Abokin shi da s**a tashi tare kyautar sabuwar Mota a Katsina. ‎‎Domin taim...
05/08/2026

‎Labari Cikin Hotuna

‎Dr. Haruna Maiwada ya ba Abokin shi da s**a tashi tare kyautar sabuwar Mota a Katsina.

‎Domin taimaka ma matasa wajen ganin sun dogara da kan su Dr. Haruna Maiwada ya bada kyautar sabuwar mota kirar golf 3 ga daya daga cikin Abokanshi wato Muhammadu Malam (Milo) wanda ke sana'ar jigilar fasinjoji daga Katsina zuwa wasu garuruwa dake sassan ƙasar nan.

‎Dayake hannanta motar a madadin Dr Haruna Maiwada, Shugaban tafiyar Gidan Amana Akida na jihar Katsina Alhaji Abba Maiwada yace Dan Amanar yayi hakan ga matashin domin ya cigaba da neman abincin shi kamar yanda saba.

Haka kuma maiwada ya kara da cewa Sadaukin kaita yanayin hakan don ganin ya chanza rayuwar Matasan ta hanyar samar masu sana'o'in dogaro da kai.

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when World News Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share