Ahmed Isah Doro

Ahmed Isah Doro politics
latest news
Sports
Entertainment

ALLÀHÙ AKBÀR: Shaharareń dan kwallön kafan Kàsar Morocco, Ashraf Hakimí, mai taka leda a kasar Faransa Inda yake bugawa ...
14/04/2023

ALLÀHÙ AKBÀR: Shaharareń dan kwallön kafan Kàsar Morocco, Ashraf Hakimí, mai taka leda a kasar Faransa Inda yake bugawa wasa a PSG, yana daya daga cikin 'yan kwallò masu kwasar albashi mai tsoka a Faransa saboda bajintarsa.

A yayin da ya samu matsala da matarsar, inda ta kai shi kara kotu tana bukatar a raba dukiyar sa biyu a mallaka a mata rabi.

Isar su Kotu ke da wuya sai ta fahimci ashe Hakimi Ashraf ba shi da ko sisi a asusun ajiyarsa na banki, duk dukiyarsa da komai nasa ya jima da maida su karkashin sunan Mahaifiyarsa, wanda hakan ke nuna ya mallakawa mahaifiyar sa dukiyar sa baki daya, wanda hakan ya hana matar samun komai daga dukiyar dan kwallon.

Ni ko na ce ka ji Dan Kwallo mai neman albarka.

Allah Ya yi maka albarka.

DAGÀ: Usman Rabiu Kwankwaso

13/04/2023

Allah baya tabar da Zuri'ar masu TAQAWA Professor Isa Ali Pantami

11/04/2023

Professor Isa Ali Pantami Bayani akan yayan mu da irin Gudummuwar daya kamata iyaye su Bama yayansu Domin Samun Hardar Al'qurani Mai Girma.

Ayi sauraro lafiya

08/04/2023
*YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA**SAURANSU*Daga: Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam[Rahimahullah].(Malam ya yi ...
14/09/2022

*YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA*
*SAURANSU*

Daga: Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam
[Rahimahullah].

(Malam ya yi wannan bayanin ne a Tafsirin
Maiduguri na shekarar 2006M a cikin Suratut-
Taubah aya ta 100)
“Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai
‘siffatul ijza’ (ta wadatar), kuma wacce ake kira
‘siffatu kamal’ (ta kamala).
*Wankan Janaba a siffar sa ta kamala* shi ne:
Idan ka zo za ka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a
gabanka. Farkon abin da za ka fara yi shi ne:
Za ka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke
hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a
cikin ruwan sai ka debo ka wanke gabanka, a
dai-dai lokacin da za ka wanke gabanka a lokacin
za ka kulla niyya ta wankan Janaba (Ko
waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke
gabanka ma’ana ka yi tsarki kenan, to daga nan
kuma sai ka yi alwala irin yanda kake alwala ta
sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah za
kayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan
za ka kyale shi ba za kayi shi ba, to daga nan sai
ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba
tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka
saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da
maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma
yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude
musammam gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa
a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani
abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikin
tafin hannunka daya sai ka zuba a kanka ka
tabbatar ya game ko ina a kanka, ka sake
kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko ina a
kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko ina a
kanka.

To idan ka yi wannan sai ka debi ruwa ka game
dukkanin jikinka da shi kana mai farawa da
bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan
na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko ina. To idan
ka yi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi
ne sai ka wanke kafarka ta dama sannan kafarka
ta hagu shi ne cikon alwalar da ka riga ka faro.
Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan Janaba.
In wankan Janaba ne haka za ka yi, in na Haila
ne haka za a yi in ma wanka ne na Biki haka
mace za ta yi, idan wankan Jumu’a ne ma haka
za a yi, wankan Idi ma haka za ka yi, banbanci
kawai shi ne NIYYA.
*Idan mutum zai yi siffa ta ‘Al ijza’* wadda ta
wadatar ba sai ka yi alawa a cikin ta ba, kana
zuwa ka yi niyyar yin wanka din kawai sai ka
dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko’ina,
in ma wani kududdufi ne ko rami ko “swimming
pool” sai ka yi tsalle ka fada a ciki, dama ka kulla
niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito abin da za
ka yi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar baki da
kuma shaka ruwa a hanci da fyacewa. Shi kenan,
kuma ya halatta ka yi sallah da wannan wankan,
Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.
Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fi ka
kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fi ka
cikar kamala, ya fi ka lada.
Kasancewar ba a yi alwala ba ciki, wannan ka’ida
ce ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL
ASGAR) idan sun hadu da babban kari
(HADATHUL AKBAR) to da ka kawar da babban
kari, karamin ma ya tafi. Amma ba lallai bane
idan ka kawar da karamin a ce babban ma ya
tafi.”

We are on the move
29/08/2022

We are on the move

16/08/2022
16/08/2022

Yanzu-Yanzu: Sha’aban Sharada ya fice daga APC inda ya samu tikitin takarar gwamna a jam'iyyar ADP mai littafi

Dan majalisar wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni a jihar Kano, Shaaban Ibrahim Sharada, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADP.

Bayan sauya sheka, DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa dan majalisar ya koma jam’iyyar ADP kuma ya karbi tikitin takarar gwamna na jam’iyyar.

Majiya mai tushe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC da ke Kano, ta ce Sharada zai yiwa jam’iyyar ADP takara tare da abokin takararsa, Rabiu Bako.

Sharada wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro da leken asiri, ya yi takarar neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC amma mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna ya kayar da shi.

16/08/2022

    Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, bayan wasu gwaɓaɓan alƙawura da ake zargin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi masa. Malam Shekarau, wanda ke wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, ya fi...

15/08/2022

Asibitin Aminu Kano zai fara dashen ɓargo

Asibitin koyarwa na Aminu Kano, AKTH, da ke Kano, a yau Litinin ya ƙaddamar da wani sabon sashin kula da cututtukan jini kuma hakan ya nuna cewa za a fara dashen ɓargo a cibiyar.

AKTH zai kasance asibitin koyarwa na biyu a Nijeriya da zai riƙa yin dashen ɓargo a kasar.

Babban Daraktan Asibitin, Farfesa Abba Sheshe ne ya bayyana haka a wurin kaddamar da cibiyar a hukumance, wanda wani Injiniya Umar lbrahim ya bada ita a matsayin gudunmawa.

Ya bayyana cewa asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas ne kadai ya yi nasarar dashen ɓargo a Najeriya.

Ya kuma jaddada cewa kayan aikin da za a sanya a cibiyar za su sanya a samu nasarar dashen ɓargo a asibitin.

Ya yabawa mai bayarwa lbrahim, kuma yayi addu'ar Allah ya saka masa da alkhairi.

Da yake jawabi a madadin mai bayar da tallafin, Farfesa Mahmoud Daneji, ya ce an yi hakan ne domin tunawa da marigayiya mahaifiyarsa.

Ya kuma yi kira ga wadanda s**a ci gajiyar ayyukan da aka gudanar a unguwar, da su yi wa mahaifiyar wanda ya bada gudunmawar addu'a, da shi kansa da kuma dukkan iyalanta.

15/08/2022

The Independent National Electoral Commission (INEC) says the All Progressives Congress (APC) has no candidate for Yobe North and Akwa Ibom North West Senatorial Districts.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ahmed Isah Doro posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ahmed Isah Doro:

Share