04/10/2023
Gwamnan jihar Katsina Malam Dr. Dikko Umaru Radda, zai dauki nauyin dalibai 'yan asalin jihar Katsina zuwa karatu kasashen waje.
Mai girma gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, ya amince da a fara tattara takardun neman guraben Karatu (wato scholarship) daga dalibai ‘yan asalin jihar Katsina zuwa Jami’o’in Kasashen waje wanda Gwamnatin Jiha za ta dauki nauyinsu.
Kwasakwasan da za a karanta sune; Karatun ilimin likita (wato MBBS) Karatun ilimin kirkire-kirkiren Na’ura mai kwakwalwa dake da kaifin basira (wato Artificial Intelligence) Karatun ilimin tattalin arziki dake da alaka da hallittu da tsirrai. (wato Bio-Economy).
Daliban da suke da sha’awar shiga shirin su kasance suna da takardu kamar haka:-
Takardar Sakamakon gama makarantar sakandare WAEC/NECO a zama guda, da yabo (wato credit) akalla takwas (8) a darussa kamar haka:-
Darasin ilimin kwakwaf (Physics)
Darasin ilimin hada magunguna (Chemistry)
Darasin ilimin sanin hallittu da tsirrai (Biology), kona Ilimin Aikin Gona (Agric Science)
Darasin Turanci
Darasin Lissafi
Darasin ilimin Na’ura Mai Kwakwalwa [a inda keda bukatar haka]
Bugu da kari, daliban da ke neman karatun likitanci (wato MBBS), wajibi ne su kasance suna da sakamako mai daraja ta “A” ko “B” akalla a darussa ukku masu alaka.
Sauran Kwasakwasan biyu kuma (wato, Artificial intelligence da Bio Economy) dole dalibi ya kasance yana da sakamako mai matakin daraja “A” ko “B” akalla guda biyu (2).
Sannan dole dalibi ya kasance bai gaza shekaru goma sha shidda (16) ba, kuma bai wuce shekaru ashirin da biyu (22) ba na haihuwa a lokacin neman wannan gurbin Karatu.
Daliban da s**a gama makarantun gwamnati kawai ne za su shiga wannan shiri.
Sannan Kowace Karamar Hukuma za ta samu wakilci a cikin daliban da za a tantance a kuma dauka.
Za a aiko da takardun neman gurbin karatun tare da Takardun shaidar gama makarantar primary da na sakandare WAEC/NECO, Takardar haihuwa, Takardar shaidar zama dan Karamar hukuma, Takardar shaidar nuna hali n