
03/06/2023
Na Gamsu Da Cire Tallafin Mai Da Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi - Cewar Mawaki Rarara
Shahararren mawakin siyasa a Najeriya Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya bayyana cewa ya ji dadi akan cire tallafin mai da sabon Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a Najeriya.
Mawaki Rarara ya bayyana wannan matsaya tashi ne a wata tattaunawa da ya yi da Kafar Sadarwa ta DCL, kuma Accuracy News 24/7 ta kalato.
A cewar Rarara, Tinubu ya cire tallafin mai ne ba don ya kuntata ma yan Najeriya ba ne, illa iyaka wani mataki ne na fara daidaita lamurra a Kasar, bayan da aka rantsar da shi a matsayin Shugaban Kasa.
Dama dai tuni da damar yan Najeriya ke ta kiraye-kiraye akan cire tallafin man, inda suke ganin cewa baya da wani amfani ga talakawan Najeriya, domin kuwa wasu tsirarun mutane ne ke amfana da shi.
A cewar Rarara" Tinubu da dukkan iyalan shi masu arziki ne, ba sun zo mulkin Najeriya ba ne don su karu da kudin Kasar, dukkan su da shi Tinubu da matar shi da ya'yan shi duk masu arziki ne, basu bukatar ko sisin kwabon Najeriya.
A sabili da haka ya bukaci yan Najeriya akan su yi uzuri ga Shugaban Kasar, inda ya tabbatar da cewa da izinin Allah cire tallafin man zai zama alkairi ga yan Kasar, domin ba an yi shi ba ne don a kuntata masu, sai dai don a kawo gyara.
Mawaki Rarara ya kuma roki yan Najeriya akan su kara jajurcewa wurin gudanar da addu'oin samun nasarar sabuwar Gwamnatin ta Tinubu, domin inganata rayuwa da kyautata jin dadin su.