Katsina Media House

Katsina Media House Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Katsina Media House, Media/News Company, Katsina.

DA DUMI DUMINSHILADO YOUTHS CONSULTATIVE FORUM TA BAIWA COMR. MANSUR HAMZA DARMA SA’O’I 95Kungiyar Lado Youths Consultat...
21/08/2026

DA DUMI DUMINSHI

LADO YOUTHS CONSULTATIVE FORUM TA BAIWA COMR. MANSUR HAMZA DARMA SA’O’I 95

Kungiyar Lado Youths Consultative Forum ta baiwa Comr. Mansur Hamza Darma wa’adin sa’o’i 95 domin ya janye kalamansa kan H.E Sanata Yakubu Lado Dan Marke dangane da dangantasa da Yayi a matsayin “dan kwangilar siyasa”.

Kungiyar ta ce idan bai yi hakan ba, za su hadu da shi a kotu.

21/08/2026
2027: Katsina Will Repay Tinubu’s Goodwill Through Re-election, Says Gwajo-GwajoThe Political Adviser to the Katsina Sta...
21/08/2026

2027: Katsina Will Repay Tinubu’s Goodwill Through Re-election, Says Gwajo-Gwajo

The Political Adviser to the Katsina State Governor, Rt. Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, has described the re-election of President Bola Ahmed Tinubu in 2027 as an opportunity for the people of Katsina State to reciprocate the goodwill and support the President has extended to the state and its people.
Gwajo-Gwajo made the remarks on Thursday, August 20, 2026, when he received a delegation of the Tinubu Again Support Movement on behalf of the Katsina State Governor, Malam Dikko Umaru Radda, at his office at the Old Government House, Katsina.

The delegation was led by the North-West Coordinator of the organisation, Hon. Umar Maiwata, as part of the group’s engagement and mobilisation activities ahead of the 2027 general elections.

The Tinubu Again Support Movement comprises former political appointees that includes SSA and SA, who served under past governors of the North-West states, as well as serving political office holders. The movement was established to mobilise support for President Bola Ahmed Tinubu, APC governors across the North, and other candidates of the All Progressives Congress (APC) ahead of the 2027 elections.
Hon. Umar Maiwata, who spoke on behalf of the movement, disclosed that the organisation enjoys the support of the Minister of State for Defence, His Excellency Alhaji Bello Matawalle.

Speaking on the significance of the movement, Gwajo-Gwajo said its establishment was a strategic step towards consolidating support for President Tinubu and ensuring the success of the APC in the 2027 elections.
He noted that the people of Katsina State have compelling reasons to appreciate and support President Tinubu, particularly considering his longstanding relationship with and contributions to prominent sons of the state, including former Presidents Umaru Musa Yar’Adua and Muhammadu Buhari.

According to him, the people of Katsina have a duty to acknowledge the President’s goodwill and support, adding that voting for his re-election in 2027 would provide an opportunity for the people to express their appreciation and reciprocate the positive gestures extended to the state and its people.

In his remarks, the National Chairman of the Tinubu Again Support Movement, represented by the organisation’s spokesperson, reaffirmed the movement’s determination to work tirelessly towards securing President Tinubu’s victory in the 2027 presidential election.

He explained that the delegation was on a familiarisation and mobilisation tour aimed at strengthening collaboration with its members and stakeholders across the North-West.
He disclosed that the tour would cover five states, with Katsina State serving as the first point of call.

Also speaking, the Katsina State Coordinator of the movement, Hon. Bashir Ya’u (Bershow), stressed the importance of unity, cooperation and collective effort among APC stakeholders to ensure the success of the party’s candidates in the 2027 elections.

He reaffirmed the organisation’s commitment to sustained public enlightenment, grassroots mobilisation and engagement with relevant stakeholders in pursuit of the objectives for which the movement was established.

The visit culminated in the presentation of a letter of appointment to Rt. Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, formally recognising him as the National Patron of the Tinubu Again Support Movement.
The organisation also nominated Hon. Bashir Ya’u (Bershow) as the Katsina State Coordinator of the movement.

The development further underscores the growing mobilisation and political engagement among supporters of the APC ahead of the 2027 general elections.

ICPC na bibiyar ayyukan mazabu na sama da N1bn a KatsinaHukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya ICPC, ta ce tana...
21/08/2026

ICPC na bibiyar ayyukan mazabu na sama da N1bn a Katsina

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya ICPC, ta ce tana bibiyar ayyukan mazabu 21 da darajarsu ta haura Naira biliyan daya a fadin Jihar Katsina.

Karin bayani: DCL Hausa

‎"Kai Ne Haƙiƙanin Ma'anar Jahilcin Tattalin Arziƙi", Martanin Atiku Ga Tinubu‎‎Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku A...
21/08/2026

‎"Kai Ne Haƙiƙanin Ma'anar Jahilcin Tattalin Arziƙi", Martanin Atiku Ga Tinubu

‎Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu martani mai zafi, bayan da shugaban ya soki alƙawarinsa na sake duba tsarin tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.

‎Tinubu, a yayin wani taro da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a ranar Alhamis, ya bayyana alƙawarin dawo da tallafin a matsayin abin da ke nuna “tsananin jahilci kan shugabanci da tattalin arziki", kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

‎Sai dai a martanin Atiku ta bakin Babban Mataimakinsa na Musamman kan Sadarwa, Phrank Shaibu, ya yi watsi da s**ar, yana mai zargin gwamnatin Tinubu da aiwatar da manufofin tattalin arziƙi da s**a ƙara wa ƴan Najeriya matsin rayuwa.

‎Atiku ya ce cire tallafin man fetur, tare da sauye-sauyen farashin canjin kuɗi, ya haifar da jerin matsalolin tattalin arziƙi da s**a haɗa da tashin farashin man fetur, tsadar sufuri da samar da kayayyaki, faɗuwar darajar naira da hauhawar farashin abinci.

‎Ya ƙara da cewa shirin da yake gabatarwa ba wai komawa ga tsohon tsarin tallafin man fetur mara iyaka ba ne, sai dai samar da wani tsarin tallafi mai iyaka, kasafi tabbatacce, wa’adi ƙayyadadde da kuma binciken kuɗaɗensa, wanda za a danganta shi da bunƙasa samar da man fetur a cikin gida.

‎Atiku ya kuma ƙalubalanci iƙirarin cewa an kawo ƙarshen duk wani nau’in tallafin man fetur, yana mai tambayar dalilin da ya sa har yanzu ake samun wasu abubuwan da ake kira energy security costs da petroleum under-recoveries a bayanan kuɗaɗen NNPC.

‎A cewarsa, idan tallafin man fetur ya ƙare, to ya kamata gwamnati ta bayyana wa ƴan Najeriya dalilin da ya sa ake ci gaba da samun irin waɗannan kuɗaɗe a cikin tsarin kamfanin mai na ƙasa.

‎Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma soki hujjar gwamnatin tarayya cewa cire tallafin ya ƙara yawan kuɗaɗen da jihohi ke samu daga FAAC, yana mai cewa ƙarin kuɗaɗen gwamnati bai kamata ya zo da tsadar da za ta jefa iyalai cikin matsanancin hali ba.

‎“Ba za a gina tarayya ta hanyar talauta ƴan ƙasa domin Abuja da jihohi su samu ƙarin kuɗaɗe ba,” in ji shi.

‎Atiku ya ce matsalar tattalin arziƙin Najeriya na buƙatar manufofin da za su daidaita tsakanin bunƙasa kuɗaɗen gwamnati da kuma kare ƙarfin sayen ƴan ƙasa.

‎Martanin nasa na zuwa ne yayin da batun tallafin man fetur ke ƙara zama ɗaya daga cikin muhimman batutuwan siyasar Najeriya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

An Kammala Shirin Horas Da Malamai Na Wucin Gadi, Guda 200 Da Injiniya Muttaka Rabe Darma Ya Ɗauki Nauyi.A ranar Juma'a ...
21/08/2026

An Kammala Shirin Horas Da Malamai Na Wucin Gadi, Guda 200 Da Injiniya Muttaka Rabe Darma Ya Ɗauki Nauyi.

A ranar Juma'a 21, ga watan Agusta, na shekarar 2026, aka kammala shirin horas da Malaman makarantu na wucin gadi, guda dari biyu 200, da ministan gidaje da raya birane, Injiniya Muttaka Rabe Darma ya dauki nauyi, a ƙananan hukumomi guda bakwai dake jihar Katsina.

Shugaban kula da shirin Dr. Abdussalam Abubakar, ya bayyana cewa manufar shirin shi ne taimakawa matasa waɗanda s**a kammala karatu amma kuma basu da ayyukan yi, da kuma ɗalibai na sakandire, musamman masu shirin zana jarabawowin WEAC, NECO, JAMB da sauransu.

Ya kara da cewa, shirin ya bayar da dama ga matasa waɗanda suke da matakin karatu na Degree da kuma NCE guda 200, tare da horas da su akan darussan da s**a hada da, English, Maths, Physics, Chemistry, Biology, Economics, Accounting da kuma darasin Government, domin su ringa koyar da ɗalibai waɗannan darussa a ƙananan hukumomin su.

Dr. Abdussalam Abubakar, ya kara da cewa, Za'a ringa bayar da alawus na 40,000 ga masu Degree da HND, da kuma 30,000 ga masu NCE. Sannan kuma an fara shirin ne a kananan hukumomi bakwai a matsayin matakin farko, tare da sa ran shirin zai cigaba da gudana a dukkan kananan hukumomi 34 na Jihar Katsina, domin tasirin da shirin yake da shi a cikin al'umma.

Daga karshe ya yaba wa Injiniya Muttaka Rabe Darma, da wannan kyakkyawan shirin da ya kawo, kuma ya bayyana cewa yana sa ran sauran masu rike da mukamai daga matakin tarayya har zuwa na jiha su ma su kirkiri wani tsari wanda zai taimaka ma rayuwar al'umma domin cigabanta.

Radda Ya Tallafa wa Kungiyar APC Zallah da Motoci Uku don yakin neman zaben 2027Katsina TimesGwamnan Jihar Katsina, Mala...
21/08/2026

Radda Ya Tallafa wa Kungiyar APC Zallah da Motoci Uku don yakin neman zaben 2027

Katsina Times

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bai wa kungiyar APC Zallah Movement tallafin motoci uku domin saukaka ayyukanta da karfafa wayar da kan jama’a a fadin jihar, yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Gwamnan ya bayyana tallafin ne a ranar Juma’a, 21 ga Agusta 2026, a yayin kaddamar da shugabannin kungiyar a kananan hukumomi 34 da mazabu 361 na jihar Katsina. An gudanar da taron kaddamarwar ne a filin People’s Square da ke Katsina.

Baya ga tallafin Gwamna Radda, tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya bayar da mota guda tare da Naira miliyan biyu ga kungiyar.

Haka kuma, Kwamishinan Lafiya na jihar, Musa Adamu, ya bayar da Naira miliyan daya, yayin da wani dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Kankiya ya bayar da karin Naira miliyan daya domin gudanar da ayyukan kungiyar.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Radda ya yaba wa kungiyar bisa jajircewarta da goyon bayanta ga jam’iyyar APC da shugabanninta daga matakin kasa zuwa mazabu da rumfunan zabe.

Radda ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da kungiyar domin kara karfafa jam’iyyar APC da tabbatar da nasararta a zaben 2027.

Gwamnan ya ce nasarar da APC ta samu a zaben 2023 ta nuna karfin jam’iyyar, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta sake samun nasara a zaben 2027.

Sai dai Gwamna Radda ya soki wasu daga cikin masu neman takarar mukaman siyasa a jihar, yana mai zargin cewa wasu daga cikinsu ba su da cikakken shirin yi wa al’umma hidima, domin abin da ya fi damunsu shi ne harkokin kasuwanci.

Tun da farko, tsohon Minista Dangiwa ya bayyana shugaban APC Zallah Movement, Dr Bala Nuhu Kankia, a matsayin matashin dan siyasa mai kishin al’umma, gaskiya da amana.

Ya ce babban burin Kankia shi ne ci gaban al’umma da nasarar jam’iyyar APC, yana mai cewa ya kasance yana amfani da duk abin da yake da shi wajen tallafa wa ayyukan kungiyar.

Dangiwa ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa kungiyar gwargwadon iko domin taimaka wa APC ta samu nasara a zaben 2027.

Shi ma shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Dr Bishir Gambo Saulawa, ya bayyana kaddamar da kungiyar a fadin jihar a matsayin wani mataki da zai kara hada kan ‘yan jam’iyyar da karfafa kokarinsu na ganin APC ta samu nasara.

Saulawa ya ce ya san kungiyar da wadanda s**a assasa ta, yana mai cewa manufarta ita ce nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Radda da sauran ‘yan takarar APC.

Ya kuma yaba wa Dr Kankia kan yadda yake ci gaba da tallafa wa jam’iyyar, tare da tabbatar masa da goyon bayan shugabancin APC na jihar.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar APC Zallah Movement, Dr Bala Nuhu Kankia, ya gode wa Gwamna Radda da sauran masu ruwa da tsaki bisa tallafin da suke bai wa kungiyar.

Ya ce kungiyar za ta ci gaba da amfani da dukkan damar da take da ita wajen ganin APC ta samu nasara a dukkan kujerun da za ta fafata a zaben 2027.

Kankia ya kuma yaba wa Gwamna Radda kan ayyukan raya jihar da gwamnatinsa ke aiwatarwa, yana mai cewa nasarar APC za ta ba gwamnati damar ci gaba da ayyukan da ta fara.

Ya amince cewa kungiyar ba ta da kudade, amma ya ce za ta ci gaba da amfani da abin da take da shi wajen tallafa wa jam’iyyar.

Ya kuma bukaci Gwamna Radda da ya taimaka wajen kai ayyukan kungiyar zuwa wuraren da ba za ta iya isa da kanta ba, domin kara mata karfin gwiwa wajen ci gaba da wayar da kan jama’a da tallafa wa jam’iyyar APC.

21/08/2026

TATTAUNAWA DA COMR. MANSUR HAMZA DARMA
Dan Jam’iyyar APC

Comrade Mansur Hamza Darma ya bayyana cewa Jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta shirya cin zabe "daga sama har ƙasa" a zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Karɓi Baƙuncin Tawagar Ƙaramar Hukumar Dutsin-ma, Ya Ƙara Jaddada Ƙudirin Ci Gaban Ƙaramar HukumarGwamna...
21/08/2026

Gwamna Radda Ya Karɓi Baƙuncin Tawagar Ƙaramar Hukumar Dutsin-ma, Ya Ƙara Jaddada Ƙudirin Ci Gaban Ƙaramar Hukumar

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya karɓi tawagar masu ruwa da tsaki na Ƙaramar Hukumar Dutsin-ma, wadda ta kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin jihar.

A yayin ziyarar, Shugaban Ƙaramar Hukumar Dutsin-ma ya gabatar da jawabin maraba tare da bayyana manufar zuwan tawagar.

Yandakan Katsina, Hakimin Dutsin-ma, Alhaji Sada Muhammad Sada, ya yabawa Gwamna Radda bisa ayyukan ci gaba da ayyukan alheri da gwamnatinsa ta aiwatar a ƙaramar hukumar. Ya kuma gabatar da wasu buƙatu da korafe-korafen al’ummar yankin.

Da yake mayar da jawabi, Gwamna Radda ya bayyana cewa Dutsin-ma tamkar gidansa ce, yana mai cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da ci gaban ƙaramar hukumar.

Gwamnan ya tabbatar da cewa duk abin da ya kamata gwamnatin sa ta yi domin ƙara bunƙasa Dutsin-ma da inganta rayuwar al’ummarta, za ta ci gaba da yin sa domin kawo cigaba a yankin.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

August 21, 2026.

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina Media House posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share