06/07/2022
Harin gidan yarin Kuje: Na ji takaici ga tsarin tsaron sirri na ƙasar nan -- Buhari
A yau Laraba ne dai Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ziyarci gidan yarin Kuje da ƴan ta’adda su ka kai wa hari, inda ya nuna rashin jin dadinsa da tsarin tsaron sirri na kasar nan.
Bayan duba illar da harin ya yi, Buhari ya zanta da manema labarai, inda ya nuna rashin jin dadinsa ga tsarin tsaron sirri na ƙasar nan da kuma yadda a ke gudanar da shi.
Ya ce: “Na ji takaici ga tsarin tsaron sirri na ƙasar nan. Ta yaya ƴan ta’adda za su iya shiryawa tare da ɗaukar makamai, su kai hari a kan cibiyar tsaro kuma su tafi salin-alin?"
Shugaban, wanda kamar yadda akasarin ’yan Najeriya, ya nuna kaɗuwarsa ga irin girman harin, inda yayi tambaya “ yaya aka yi jami’an tsaron gidan yarin s**a kasa daƙile harin? Fursunoni nawa ne ke cikin gidan yarin?
“Nawa ne za ku iya lissafowa? Ma'aikata nawa ne ke da su a bakin aiki? Nawa ne a cikinsu ke ɗauke da makamai? Akwai masu gadi a hasumiyar tsaro? Me s**a yi? Shin kyamarar CCTV tana aiki?" Tambaya bayan tambaya.
An kuma sanar da Shugaban kasar, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Senegal, cewa, jami’an tsaro sun kamk fursunoni 350 daga cikin wadanda s**a tsere, yayin da wasu kimanin 450 ba a san inda su ke ba, kuma ana ci gaba da aikin nemo sauran.
Buhari, tare da rakiyar Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya, ya ce a karshen ziyarar yana sa ran samun cikakken rahoto kan lamarin.