Tv arewa

Tv arewa Tv arewa news akoda yaushe, Tv AREWA Zata Cigaba Dakawo Maku Labarai Dazata Cigaba Da Kawo Maku Shirye Shirye Dazasu Kayatarda Daku Aciki Awanin 24.

news content

A lokacin da ake gudanar da zaben jihar mu ta Osun, Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya kirani yace in goge ...
18/08/2026

A lokacin da ake gudanar da zaben jihar mu ta Osun, Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya kirani yace in goge wani sako dana wallafa a shafin X amma naki.

Hakanan kawuna ma Dangote ya kirani yace in goge sakon amma nace masa yayi hakuri gaskiya sai INEC ta bayyana kawuna a matsayin wanda yayi nasara kamin in goge.

Inji Mawaki Davido

WATA SABUWA: Adeleke ya bayyana hakan ne yayin da yake gode wa shugaban ƙasar kan yadda ya ce ya tabbatar da an gudanar ...
16/08/2026

WATA SABUWA: Adeleke ya bayyana hakan ne yayin da yake gode wa shugaban ƙasar kan yadda ya ce ya tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin tsarin dimokuraɗiya.

DA DUMI DUMI: Yadda gwamnonin APC guda 15 suna ficewa daga ɗakin tattara sakamakon zaɓe Osun Me za ku ce?
16/08/2026

DA DUMI DUMI: Yadda gwamnonin APC guda 15 suna ficewa daga ɗakin tattara sakamakon zaɓe Osun

Me za ku ce?

16/08/2026

Yadda Mawaki davido yayanke Jiki yafadi Bayan ansanarda ademola edeleke shine Talashe zabe

AKWAI KURA: GWAMNONIN JAM'IYYAR APC SU SHAFA WA KANSU RUWABabban darasi daga zaben kujeran Gwamnan jihar Osun da ya guda...
16/08/2026

AKWAI KURA: GWAMNONIN JAM'IYYAR APC SU SHAFA WA KANSU RUWA

Babban darasi daga zaben kujeran Gwamnan jihar Osun da ya gudana jiya asabar

Ana dab da kammala kirga kuri'un zaben kujeran Gwamnan jihar Osun da aka yi jiya, sakamakon zabe na karamar hukuma daya ne kadai ya rage zuwa yanzu da nake rubutu

Ga sakamakon zaben:
👇
Accord: 487,553
APC: 420,164
ADC: 16,525
Jam'iyyar Accord Party ta bawa jam'iyyar APC mai mulkin Kasa ratar kuri'u 67,389, wanda hakan na nufin jam'iyyar APC ta fadi zaben jihar Osun

Gwamna mai ci Ademola Adeleke ya sake neman tazarce a jam'iyyar Accord Party, ya hadu da manyan kalubale kasancewar ba a jam'iyyar APC mai mulkin Kasa yake ba

Kafin a kai ga gudanar da zaben anyi ta samun manyan rikici na siyasa a jihar musamman tsakanin jam'iyyar Accord da APC da take son kwace mulkin

Akwai wani sanannen mawaki dan uwan Gwamna Adeleke da ake kira Davido, har karan Gwamnatin tarayya ya kai zuwa gaban Shugaban Amurka domin kar ayi amfani da karfin gwamnatin tarayya a murda zaben jihar Osun

Kusan Gwamnonin jam'iyyar APC gaba daya sai da s**a je jihar Osun shekaran jiya domin su bada gudunmawa wajen kwace kujeran mulki, har da Dr Abdullahi Umar Ganduje ya je, an tsaurara dukkan matakai na tsaro

To amma a karshe Allah Ya bawa Gwamna Adeleke nasara duk da karfin da jam'iyyar APC take da shi, zata iya murda zaben, amma ta bari akayi zabe na gaskiya, abinda ba'a yi zato ba

Magana ta gaskiya Gwamnonin jam'iyyar APC su shiga taitayinsu, su shafa wa kansu ruwa, kar su yi tsammanin zasu ci bulus a babban zaben 2027, murdiyan zabe zai zama tarihi, muna digital era ne, komai a fili yake

Duk Gwamnan da ya san bai taimaki talaka ba, bai yi aikin da ya kamata ba, to ya shafa wa kansa ruwa, zaben 2027 iya ruwa ne fidda kai, shima Shugaba Tinubu ta kansa yake a zaben 2027 mai zuwa, pressure ya masa yawa, ana ta kai karansa zuwa Amurka

Zaben jihar Osun babban sako ne da fadakarwa zuwa ga Gwamnonin jam'iyyar APC wadanda suke ganin zasu ci bulus, su sani karfin i

Shahararren mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi kira ga ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Jam...
15/08/2026

Shahararren mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi kira ga ɗan Majalisar Wakilai, Hon.
James Faleke, da ya mutunta muradin al’ummar Jihar Osun, tare da kaurace wa duk wani yunƙuri na matsa wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) laata sakamakon zaɓen gwamna jihar.

Davido ya yi wannan kiran ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta a sassan jihar.

Mawakin, wanda ɗan’uwan Gwamna Ademola Adeleke ne, ya buƙaci Faleke da ya mutunta zaɓin masu kaɗa ƙuri’a.

Davido ya rubuta shafinsa na X:
“Hon. James Faleke, ka daina matsa wa INEC lamba domin ta sauya sakamakon zaɓen Osun. Ka mutunta muradin al’ummar Osun. Ba ma son Oyetola da AMBO.”

Rajotanni Sun Bayyana Cewa Ganduje Ya Sauka A Jihar Osun A Yammacin Yau, A Daidai Lokacin Da Ɓangaren Yaƙin Neman Zaɓen ...
15/08/2026

Rajotanni Sun Bayyana Cewa Ganduje Ya Sauka A Jihar Osun A Yammacin Yau, A Daidai Lokacin Da Ɓangaren Yaƙin Neman Zaɓen Gwamna Adeleke S**a Yi Zargin Hukumar Zaɓe Na Shirin Bayyana Zaɓen Jihar A Matsayin 'Inkwankulusib"

Yanzu Yanzu: Mawaki  DJ AB ya bayyana a shafinsa na Instagram cikin jin daɗi cewa jiya ya haɗu da fasihiyar jaumar fina-...
15/08/2026

Yanzu Yanzu: Mawaki DJ AB ya bayyana a shafinsa na Instagram cikin jin daɗi cewa jiya ya haɗu da fasihiyar jaumar fina-finai Kudancin Najeriyar nan Uche Montana, inda s**a yi hoto tare a wurin wani biki.

DA DUMI DUMI: Ruwan Sama Ya Tarwatsa Kayan Taron Da Jam'iyyar APC Ta Shirya Domin Sabbin Membobin Da S**a Sauya Sheƙa Zu...
15/08/2026

DA DUMI DUMI: Ruwan Sama Ya Tarwatsa Kayan Taron Da Jam'iyyar APC Ta Shirya Domin Sabbin Membobin Da S**a Sauya Sheƙa Zuwa Cikinta A Garin Azare

FASA KWAI: Bayan da Sanata Dino Melaye yayi zargin cewa shugaba Tinubu shine shugaban Najeriya da aka taba yi wanda bash...
15/08/2026

FASA KWAI: Bayan da Sanata Dino Melaye yayi zargin cewa shugaba Tinubu shine shugaban Najeriya da aka taba yi wanda bashi da abokan karatu, watau wani wanda s**a yi karatu bai taba fitowa yace shi dan ajinsu bane.

Na kusa da Shugaban kasar, sun zakulo wani bature me suna Alex inda s**a ce shine abokin karatun shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Address

Katsina

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Telephone

+2348099720634

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tv arewa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share