Fadak Media Hub

Fadak Media Hub Media for a better world!

Mai ba Shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro NSA, Nuhu Ribadu, ya ce yaɗuwar ƙananan makamai da manyan su na ci g...
20/08/2026

Mai ba Shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro NSA, Nuhu Ribadu, ya ce yaɗuwar ƙananan makamai da manyan su na ci gaba da rura wutar ayyukan ƴan bindiga da rikice-rikicen al’umma a Nijeriya.

Ribadu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin wani taron bita na kwana ɗaya da aka gudanar kan ƙananan makamai da manyan su

Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na samar da ayyukan more rayuwa da dam...
20/08/2026

Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na samar da ayyukan more rayuwa da damammakin tattalin arziƙi a sassan ƙasar, domin rage cunkoso, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa ci gaban ƙasa.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ya ƙaddamar da aikin tagwayen hanyoyi mai tsawon kilomita 33.5 a Jihar Rivers, a madadin Shugaba Tinubu.

20/08/2026

WANNAN SAKO AN DAUKIN NAUYIN SHI!!

Al'ummar mani/bindawa na jahar katsina ku zabi chanchanta domin wakilci na gari. Honourable ALIYU HARUNA JANI (Dallatun Mani) Hon. Aliyu Haruna Jani

Dan majalasar Tarayyah mai wakiltar kananan Hukumomin MANI/BINDAWA

karshin jam'iyyar PDP.......

Wanan Sako ne daga Usman Zubairu Jani

20/08/2026

WANNAN SAKON AN DAUKI NAUYIN SHI

Katsinawan dikko shekaru na aiki da cika alkawari sun tabbata. Mu hadu domin sake zaben Malam Umar Dikko Radda a matsayin Gwamnan jahar katsina a zaben 2027

Sako daga : Saudaukin kaita Dan amanar katsina. Dr Haruna maiwada

19/08/2026
17/08/2026

Al’ummar Bakori da Danja na Jihar Katsina, ku saurari saƙon al’umma ga Hon. Abduljabbar Guga, ɗan majalisar da ake fatan zai wakilce ku. Saƙo daga masoya da magoya bayan Guga. Abduljabbar Surajo Guga

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da jami’an tsaro da su tabbata...
15/08/2026

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da jami’an tsaro da su tabbatar da gudanar da zaben gwamnan Jihar Osun da za a yi ranar Asabar cikin lumana, gaskiya da kuma sahihanci.

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci masu kada kuri’a da s**a cancanta su fito domin gudanar da hakkin da kundin tsarin mulki ya ba su, tare da tabbatar musu da cewa za a samar da isasshen tsaro kafin zaben, yayin gudanar da shi da kuma bayan kammalawarsa.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale, ya kammala wa’adinsa a matsayin babban jami’in ma’aik...
15/08/2026

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale, ya kammala wa’adinsa a matsayin babban jami’in ma’aikatan jihar, bayan shafe shekaru 35 yana aiki a gwamnatin jihar.

Bawale, wanda ya kasance kan gaba wajen tafiyar da harkokin ma’aikatan gwamnati a jihar, ya bar aikin gwamnati ne bayan cika wa’adin da aka tanada na yin ritaya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wa’adinsa a matsayin Shugaban Ma’aikatan Jihar Katsina ya kare a wannan watan na Agusta.

Rahoton LabaraiKATSINA A yayin bikin Ranar Matasa ta Duniya (International Youth Day) da aka gudanar a Jihar Katsina, wa...
13/08/2026

Rahoton Labarai

KATSINA

A yayin bikin Ranar Matasa ta Duniya (International Youth Day) da aka gudanar a Jihar Katsina, wanda kungiyar matasa ta kasa reshen jahar katsina karkashin jagoranahin Yusuf abubakar.

matashiya ‘yar jarida, wadda kuma ita ce Shugabar kamfanin gidan jarida na Fadak Media Hub, Fatima Dauda Kurfi, ta yi kira ga matasa da su kasance masu ƙaunar juna, su rungumi kyawawan ɗabi’u tare da ba da gudummawa wajen gina makoma mai kyau ga ƙasa.

Fatima Dauda Kurfi, wadda ta fito daga Ƙaramar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina, ta bayyana a jawabinta cewa kyawawan ɗabi’u su ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. Ta ce idan aka yi watsi da tarbiyya da kyawawan halaye, hakan na nufin an raunana tushen ci gaban ƙasa.

Ta ƙara da cewa matasa su ne ginshiƙan gina makomar Najeriya, don haka ya zama wajibi su kasance masu kishin ƙasa, jajircewa da kuma amfani da basirarsu wajen kawo ci gaba.

A matsayin wani ɓangare na ƙudurin da take da shi na bunƙasa rayuwar matasa ta hannun kamfaninta na Fadak Media Hub, Fatima ta yi alƙawarin horas da matasa maza yadda za su yi amfani da kafafen sada zumunta da sauran dandamalin zamani cikin hikima, domin su samar wa kansu sana’o’i masu ɗorewa da kuma dogaro da kai.

Hakazalika, ta bayyana cewa ta hannun cibiyarta ta Her Majesty Beauty Lounge, za ta ci gaba da ƙarfafa matasa mata ta hanyar ba su horo kan sana’o’i daban-daban, ciki har da sana’ar kwalliya (Make-up Artistry) da sauran sana’o’in da za su taimaka musu su dogara da kansu tare da inganta rayuwarsu.

Fatima Dauda Kurfi ta ce babban burinta shi ne ganin matasa sun zama masu dogaro da kai, masu anfani ga al’umma, kuma abin alfahari ga iyayensu, al’ummominsu da kuma ƙasa baki ɗaya.

Taron ya samu halartar manyan baƙi da dama, ciki har da Mai Girma Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda, da ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Tarayya, Hon. Abba Dahiru Mangal, tare da manyan jami’an gwamnati, shugabannin hukumomi da kuma fitattun ’yan kasuwa daga sassa daban-daban.

Masu halartar taron sun yaba da jawabin da kuma ƙudurin Fatima Dauda Kurfi na ci gaba da tallafa wa matasa, tare da bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye za su taimaka wajen bunƙasa rayuwar matasa da kuma ci gaban al’umma.

An kammala taron da addu’o’in fatan alheri ga matasa tare da fatan Allah Ya ƙara masu hikima da nasara domin cigaban kasar mu.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fadak Media Hub posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share