Katsina Online Media

Katsina Online Media Stay connected with Katsina Online Media for the latest updates, news, and insights nationwide.

Ta leko ta koma - Daktar da aka bawa Rarara ta bogi ce domin ba daga jami’ar mu bane - inji Jami’ar European - American ...
21/09/2025

Ta leko ta koma - Daktar da aka bawa Rarara ta bogi ce domin ba daga jami’ar mu bane - inji Jami’ar European - American University

Jami’ar European American University ta ce bata bawa mawaki Rarara Dakta ba wasu ne kawai s**a wanke shi a Abuja

A sanarwar da jami’ar ta fitar ta ce itama a kafafen yada labaran Najeriya ta ga labarin cewa wai ta karrama Mawaki Dauda Kahutu Rarara da wasu mutane a Najeriya

To wannan ba gaskiya bane kuma duk mai son tabbatar da labarin zai iya ziyartar shafinmu ya duba, zai ga jerin sunayen mutanen da muka karrama, inji sanarwar jami’ar ta fitar.

Shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya amince da tada sabon ginin katangar da iskar damina ta k...
17/09/2025

Shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya amince da tada sabon ginin katangar da iskar damina ta kada a makarantar Garama Primary School, tare kuma da gyara azuzuwa guda ukku waɗanda ke buƙatar buƙawar gaugawa a cikin makarantar.

Happy Birthday Your Excellency, Mallam Dikko Umaru Radda, PhD, CON.On this special day, we join millions across Katsina ...
10/09/2025

Happy Birthday Your Excellency, Mallam Dikko Umaru Radda, PhD, CON.

On this special day, we join millions across Katsina State and beyond to celebrate a visionary leader, a patriot, and a man of purpose.

Your tireless dedication to the development of our dear state, your passion for empowering the youth, and your commitment to good governance continue to inspire hope and confidence in all of us.

May this new year of your life bring you more strength, wisdom, and divine guidance as you steer Katsina State towards progress, peace, and prosperity.

Ibrahim Danrimi
10th September, 2025.

Yanzu-Yanzu: Sojoji sun yi ajalin 'yan bindigā 23 sun ceto mata 12 da Kananan yara 11 a jihar Katsina Rundunar sojojin N...
08/09/2025

Yanzu-Yanzu: Sojoji sun yi ajalin 'yan bindigā 23 sun ceto mata 12 da Kananan yara 11 a jihar Katsina

Rundunar sojojin Najeriya sun yi ajalin barayin daji 23 sun ceto mata 12 da Kananan yara 11 a wata musayar wuta da s**a yi a dajin Pauwa na yankin ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina

Rundunar sojin “Operation Fansar Yamma” ta fatattaki sansanin barayin dajin tare da ƙwato Babura da injinan huda a yayin artabu da barayin dajin a Katsina.

Wane fata za kuyi ma sojojin?

Wannan shi ne jerin sunayen daliban da za su yi karatun Diploma da HND wadanda shugaban karamar hukumar Katsina Hon. Isa...
08/09/2025

Wannan shi ne jerin sunayen daliban da za su yi karatun Diploma da HND wadanda shugaban karamar hukumar Katsina Hon. Isah Miqdad AD Saude zai dauki nauyin karatunsu daga farko har karshe.

Ra'ayi: Ya kuke ji da mamakon ruwan sama a Katsina? Ya lamarin ya shafi harkokin ku na yau da kullum?
30/08/2025

Ra'ayi:

Ya kuke ji da mamakon ruwan sama a Katsina? Ya lamarin ya shafi harkokin ku na yau da kullum?

25/08/2025

Masu saurin chanja sunan nan, basu da bambanci da waɗanda s**a dinga wanka da Gishiri lokacin Ebola.

Muje Maha...
14/08/2025

Muje Maha...

Kimanin Mutane Sama Da Dubu Saba'in Da Shidda Ne S**a Nemi Aikin Ɗamara Daga Jihar Katsina...Akalla sama da mutane Milya...
11/08/2025

Kimanin Mutane Sama Da Dubu Saba'in Da Shidda Ne S**a Nemi Aikin Ɗamara Daga Jihar Katsina...

Akalla sama da mutane Milyan Ɗaya da Dubu Ɗari Tara 1.9 ne s**a nemi ayyukan Civil Defence, Jami'an Kashe Gobara Da Na Shige Da Fice Da Za A Ɗauka, yayinda kuma mutane Dubu 30 ne kacal za a ɗauka.

Wannan shine jaddawalin yawan mutanen da s**a nemi ayyukan daga kowace jiha a faɗin Najeriya:

Kogi - 116,133

Kaduna - 114,507

Benue - 110,536

Kano - 89,362

Niger - 79,510

Kwara - 78,423

Katsina - 76,809

Nasarawa - 76,586

Adamawa - 68,305

Oyo - 67,200

Plateau - 63,393

Osun - 62,356

Borno - 56,907

Ondo - 53,920

Akwa-ibom - 52,474

Bauchi - 52,068

Imo - 48,262

Taraba - 45,147

Gombe - 45,023

Jigawa - 44,416

Ogun - 42,052

Enugu - 41,251

Yobe - 38,122

Kebbi - 34,575

Edo - 33,559

Anambra - 32,910

Ekiti - 32,676

Cross river - 32,188

Abia - 31,684

Sokoto - 31,130

FCT - 30,290

Zamfara - 29,256

Delta - 27,957

Ebonyi - 23,601

Ruvers - 22,208

Lagos - 14,215

Bayelsa - 11,669

HON. ISAH MIQDAD YA KADDAMAR DA GINA OFISHIN JAMI’AN FARIN KAYA (CIVIL DEFENCE) A GABAS IIShugaban Karamar Hukumar Katsi...
10/08/2025

HON. ISAH MIQDAD YA KADDAMAR DA GINA OFISHIN JAMI’AN FARIN KAYA (CIVIL DEFENCE) A GABAS II

Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya gudanar da bikin kaddamar da ginin sabon ofishin jami’an tsaro na farin kaya (Civil Defence) a Dustin Amare, Gabas II.

Taron ya fara da jawabin maraba daga Hon. Mustapha Musa Kofar Bai, shugaban jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Katsina, sannan jagoran shirin, Injiniya Ibrahim Lawal, ya bayyana godiya bisa wannan gagarumin mataki na tabbatar da tsaro ga al’ummar Gabas II. Haka nan, Hon. Hamisu Gambo Dan Lawal ya yaba wa shugaban bisa saurin aiwatar da aikin.

A yayin taron, al’ummar yankin masu kishin ci gaba sun bayar da gudummawar kuɗi iri-iri domin ganin an kammala aikin cikin nasara, tare da yi wa shugaban addu’ar alkhairi.

A cikin jawabinsa na kaddamarwa, Hon. Isah Miqdad ya gode wa dukkan masu hannu da shuni da kuma duk wanda ya tallafa, inda ya bayyana cewa zai gina wannan ofishi ne da kuɗin aljihunsa a matsayin sadaqatul jariya domin tunawa da mahaifinsa, marigayi Hon. Miqdad AD Saude.

Ya Kuma yi kira ga Matasan yankin dasu ka sance masu biyayya da da'a ga jam'ian da za'a turo a wannan sabon ofishi domin gudunar da aiki cikin sauki, har ila yau, ya Kara yin kira gare su da su Saka Ido a yayin gudunar da aikin da Kuma bayan kammala shi.

Ya kuma jaddada kudurinsa na kawo ayyukan ci gaba ba kawai a Gabas II ba, har ma a dukkan mazabu 12 na Karamar Hukumar Katsina, tare da gode wa jama’ar Katsina bisa ci gaba da ba wa gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda, PhD da kuma nasa shugabanci cikakken goyon baya.

Jim kadan bayan kammala kaddamar war, Shugaban yayi fira da gidajen jaridu na TVC, KTTV da sauran su, inda ya jaddada aniyar sa ta ci gaba da kawo ayyukan raya kasa a cikin Karamar Hukumar Katsina, musamman a bangaren Samar da tsaro.

Zaharaddeen Muazu Rafindadi
Sakataren Yada Labarai na Shugaban Karamar Hukumar Katsina

10-08-2025

HON. ISAH MIQDAD AD SAUDE YA SA FITILUN ZAMANI A MAZABAR WAKILIN GABAS (1)Domin samar da walawala da kuma tsaro ga al'um...
06/08/2025

HON. ISAH MIQDAD AD SAUDE YA SA FITILUN ZAMANI A MAZABAR WAKILIN GABAS (1)

Domin samar da walawala da kuma tsaro ga al'umma, Shugaban Ƙaramar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya sanya sabbin fitilun zamani masu amfani da haskena rana a wasu unguwanni na mazabar Wakilin Gabas l.

Unguwannin da s**a amfana da fitilun sun haɗa da:

1. Zanguna

2. Kofar Sauri

3. Tudun Wada Gawo

4. Makera

5. Filin Samji

6. Bayan Kayalwa Primary

7. Social bayan Makabarta

8. Kofar Bai

Aikin saka fitilun masu aiki da hasken rana ya gudana ne a karkashin jagorancin Kansilan mazabar ta Gabas l, Hon. Zaharaddin Surajo (One Second)

Al'umma suna ta godiya da kuma jin dadi, Allah Ya saka da alkhairi.

Masarautar Katsina ta amince da naɗin sabbin hakimmai guda shidda.
02/08/2025

Masarautar Katsina ta amince da naɗin sabbin hakimmai guda shidda.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina Online Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share