19/04/2026
Gudunmawar Pantami wajen Sabunta Hanyar Gombe–Kumo–Billiri–Kaltungo zuwa Cham–Numan (Yola)
A ranar 26/08/2022, an ƙaddamar da muhimmin aikin hanyar Gwamnatin Tarayya a garin Gombe wacce ta haɗa Gombe–Kumo–Billiri–Kaltungo zuwa Cham–Numan (Yola), a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, GCFR, wanda Professor Isa Ali Pantami ya wakilta. Wannan nasara ta biyo bayan ƙoƙari da jajircewarsa wajen bibiyar matsalolin hanyoyin Gombe, musamman hanyar Cham zuwa Numan, wadda ta daɗe tana tafiyar hawainiya tun bayan bayar da aikin a shekarar 2017.
Ta hanyar tuntuba da Ministocin Ayyuka tare da gabatar da hujjoji kan matsalolin fasaha da s**a haɗa da Black Cotton Soil da buƙatar sake gina gada, an samu amincewar ƙarin kuɗi sama da Naira biliyan 7.6 domin tabbatar da ingantaccen kammala aikin.
Titin ya haɗa muhimman yankuna da s**a haɗa da Gombe, Kumo, Billiri da Kaltungo, tare da ƙarfafa alaƙa tsakanin jihohin Gombe, Adamawa da Taraba. Wannan haɗin kai ya sauƙaƙa zirga-zirga, ya bunƙasa kasuwanci, tare da inganta rayuwar al’umma, musamman manoma da ‘yan kasuwa da ke anfani da hanyar a kullum. Hanyar na daga cikin muhimman ayyukan more rayuwa da ke ƙara tabbatar da tasirin wakilci da himmar Pantami wajen jawo ayyukan ci gaba zuwa jiharsa.
Maigirma Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, da Lamido Akko na daga cikin manyan baƙi da s**a halarci bikin ƙaddamarwar. Kasancewar su ya nuna muhimmancin aikin da kuma yadda haɗin gwiwar gwamnati ke samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’umma. Wannan aiki ya zama shaida a fili cewa nagartaccen wakilci da hangen nesa na iya haifar da ainihin sauyi a rayuwar jama’a.
Akwai wasiƙar da tsohon Ministan Sadarwa, Prof. Isa Ali Pantami, ya rubutawa Ministan Ayyuka na wancan lokaci, Raji Fashola (SAN), a ranar 16 ga Satumba, 2019, kan buƙatar ƙarin tallafi domin kammala wannan muhimmin aikin hanya a yankin Arewa maso Gabas. Za a kawo cikakken bayani kan wannan wasiƙa nan ba da jimawa ba, in sha Allah.