
04/07/2024
HAR ZUWA YANZU ALMAJIRAN SHAIKH IBRAHIM YAQOUB AL-ZAKZAKY(H) NA CIGABA DA BUKUKUWAN GHADEER-KHUM A NIGERIA.
Daga Abdurrahman Tasi'u Rimi.
Yau Alhamis 27/12/1445H Wanda yai dai-dai da 4/07/2024M Almajiran Shaikh Zakzaky(H) a karamar hukumar Rimin jihar Katsina Nigeria, sun gabatar gabatar da shagulgulan bikin Edil Ghadeer-Khum nuna murna da zagayowar irin ranar da Manzon tsira(S) ya nasabta Imam Aliyu bin Abidalib(As) a matsayin khalifa wanda zai gaje shi a bayansa.
Bukukuwan sun fara tun da yammacin karfe huda da mintuna(mintota) wanda Matasa s**a gabatar da takaitaccen zageyen Muzahara da sakin wakokin da suke isar da sako ga al'umar gari. Bayan kammala Muzahara Ittihadu sun cigaba da majalisi har zuwa lokacin sallar Magriba aka tashi.
Bayan dawowa daga sallah Program ya cigaba da gudana a Muhallin tsohuwar makarantar Fudiyya dake unguwar Kofar-yamma cikin garin Rimin, wanda bayan bude taro da addu'a da sauran abubuwan da aka saba Dalibai Yan Fudiyya sun bayar da tsaraba wanda ta hada da wakoki da karatukan Ayoyi da Hadisan da s**a dangancin Ghadeer-Khum din.
Daga Karshe an saurari jawabi daga bakin wakilin yan'uwa na Da'irar wato Malam Aminu Usman Jakara har zuwa kammalawa aka gabatar da walima aka yi addu'a aka sallami kowa.
Ga hotunan yadda shagulgulan s**a gudana mun dauko maku a kasa.
'irarRimiMediaForum.
04Jul2024M_27-12-1445H.