APA Hausa

APA Hausa African Press Associated (APA)

For Advertising your Business

Contact us through WhatsApp on this
+2348117479303

Masha Allah Sabon Gero yazo a garin Yamaltu Deba dake jihar Gombe.Yaya abun yake a garuruwan ku?
23/07/2025

Masha Allah Sabon Gero yazo a garin Yamaltu Deba dake jihar Gombe.

Yaya abun yake a garuruwan ku?

Wasu fusatattun matasa sun yi kukan kura sun banka wa wani baburin Adaidaita Sahu wuta da ake zargin na 'yan ƙwacen waya...
23/07/2025

Wasu fusatattun matasa sun yi kukan kura sun banka wa wani baburin Adaidaita Sahu wuta da ake zargin na 'yan ƙwacen waya ne, a unguwar Sharada dake birnin Kano.

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN:Ýar Gidan Sarkin Hadejia Ta RasuAllah Ya yi wa 'ýar sarkin Hadejia rasuwa mai suna K...
23/07/2025

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN:

Ýar Gidan Sarkin Hadejia Ta Rasu

Allah Ya yi wa 'ýar sarkin Hadejia rasuwa mai suna Khadijah Adamu Abubakar Maje (con) (Nana).

Za a gabatar da sallar jana'iza a babban masallacin Juma'a na Sarki, misalin karfe 4:00pm na yamma da zarar an idar da Sallar la'asar a yau Laraba.

Allah Ya yi mata rahama.

Saje Hadejia

Wa zai faɗa mana a wacce jiha wannan Roundabout ɗin yake a Najeriya?
23/07/2025

Wa zai faɗa mana a wacce jiha wannan Roundabout ɗin yake a Najeriya?

Ma yasa wasu samarin ke cewa basa iya auren ƴar Talla?
23/07/2025

Ma yasa wasu samarin ke cewa basa iya auren ƴar Talla?

Mahaifiyar ka ta taɓa ɗora maka farantin Talla a kai?
23/07/2025

Mahaifiyar ka ta taɓa ɗora maka farantin Talla a kai?

KARIN MAGANA:Na duƙe?
23/07/2025

KARIN MAGANA:

Na duƙe?

Masoyana ina godiya da irin so da  ƙaunar da kuke nuna min ba dare ba rana, amma don Allah ku daina zuwa shafinmu inda n...
23/07/2025

Masoyana ina godiya da irin so da ƙaunar da kuke nuna min ba dare ba rana, amma don Allah ku daina zuwa shafinmu inda nake aiki kuna kushe abokan aikina zaku iya jawo min matsala nagode—Hauwa Gwangwazo

"Idan Ina Son Saurayi Har Cikin Raina, Wanda Allah Ya Zaɓa Min Shi, Ko Iyayena Ba Sa So Sai Na Aure Shi, Koda Talaka Ne ...
23/07/2025

"Idan Ina Son Saurayi Har Cikin Raina, Wanda Allah Ya Zaɓa Min Shi, Ko Iyayena Ba Sa So Sai Na Aure Shi, Koda Talaka Ne Shi"—Inji Wannan Matashiya

'Yan Nijeriya Su Kara Baiwa Tinubu Lokaci Su Ga Aiki Da Cikawa, Domin Shine Maganin Matsalolin Dake Addabar Nijeriya,—At...
23/07/2025

'Yan Nijeriya Su Kara Baiwa Tinubu Lokaci Su Ga Aiki Da Cikawa, Domin Shine Maganin Matsalolin Dake Addabar Nijeriya,—Attahiru Jega

Gaskiya abinda Isr@ila ke aikatawa na azabtarwa da yunwa har a mutu, ko marigayi Fir'auna bai yi musu haka ba a lokacin ...
22/07/2025

Gaskiya abinda Isr@ila ke aikatawa na azabtarwa da yunwa har a mutu, ko marigayi Fir'auna bai yi musu haka ba a lokacin da yana gallaza musu kafin ceton Allah ta hannun Annabi Musa AS ya zo musu.

Tana yi musu ruwan bama-bamai ba dare ba rana , ta lalata komai na rayuwa a Gaza, ta hana majalisar ɗinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji shiga inda suke don raba musu abinci da ruwa, tace zata kula da basu abincin amma da zarar sun yi tururuwa zasu karaɓa sai a bisu da ruwan harsasai.

Wane irin bala'i ne wannan, ƙasashen Musulmi sun zuba ido suna kallon abunda ke faruwa sun kasa cewa uffan, ku duba ku gani duk rashin imanin Faransa da Birtaniya su da kansu yau sun fito sun ce zalincin nan yayi yawa saboda haka Isr@ila ta dakata hakanan.

Zan yi Addu'a,

Ya Allah ni bawanka Salisu Saminu Na Annabi ina roƙon ka da dukkan wani abu mai daraja a wajenka, ya Allah ka jarabci waɗannan miyagun bayi naka Yahudawa da bala'i da musibar da tafi wacce ka jarabce su da ita a zamanin Fir'auna kuma ya Allah ka ƙasƙantar dasu fiye da yadda Fir'auna ya ƙasƙantar da su a doron ƙasa, da gaggawa sannan ka hana musu mataimaki.

Don Allah duk wanda yaga rubun nan nau ya taimaka min wajen tura shi koda groups 5 ne kacal don sauran ƴan'uwa musulmin Duniya su taya mu da cewa Ameen da bakunan su masu albarka.

Muna rokon Allah ya karɓi wannan addu'a tamu daga

✍️Salisu Saminu Na Annabi

Kun san cewa Kwankwaso ya Kafa wa shugaba Bola Tinubu Sharaɗin shiga jam'iyyar APC ciki harda tsige Ganduje.Rahotanni su...
22/07/2025

Kun san cewa Kwankwaso ya Kafa wa shugaba Bola Tinubu Sharaɗin shiga jam'iyyar APC ciki harda tsige Ganduje.

Rahotanni sun bayyana cewa Sanata Rabi’u Kwankwaso yana tattaunawa da shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan yiwuwar ficewa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), amma ba ya shirye ya sauya sheka matukar ba a biya wasu bukatu ba.

Tsawon watanni dai jiga-jigan jam’iyyar APC na kokarin shawo kan Kwankwaso ya koma jam’iyyarsu a wani bangare na dabarun da za su yi gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Ya kasance daya daga cikin jiga-jigan siyasar Arewa, tare da dimbin magoya bayansa, musamman a Kano da sauran manyan jihohin Arewa.

Ana kallon tasirinsa a matsayin wata fa'ida ga duk jam'iyyar da ke shirin tunkarar babban zabe mai zuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa Kwankwaso da Tinubu sun yi taruka da dama, amma rahotanni sun ce tsohon gwamnan na Kano ya dage kan wasu sharudda.

Daya daga cikinsu shi ne ya tsige Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa, lamarin da aka yi magana bayan murabus din Ganduje.

Sai dai har yanzu Kwankwaso yana son ya mallaki tsarin APC a Kano, ya kuma nemi wani kwakkwaran matsayi a madadinsa. Ya ce wannan tayin zai taimaka masa ya ci gaba da rike dimbin magoya bayansa na siyasa.

Ga dukkan alamu wannan bukatar na kara daukar hankali a cikin jam’iyyar APC, musamman ma dai tattaunawa da ake yi cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ba zai yi takara da Tinubu ba a 2027.

Ana ci gaba da cece-kuce a cikin jam’iyyar na cewa watakila Shettima ya daina samun cikakken goyon bayan shugaban kasa.

A kwanakin baya ne wani shugaban jam’iyyar Salihu Isa Nataro ya bayyana cewa Shettima ya yi la’akari da ficewa daga jam’iyyar idan da gaske yana son ajandar shugaban kasa ta yi nasara.

Ya shawarci Shettima da ya bayyana matakinsa a bainar jama’a kuma ya yi alkawarin taimakawa wajen yakin neman zaben shugaban kasa daga yankin Arewa maso Gabas.

Yuwuwar sauya shekar Kwankwaso kuma tana shafar jam’iyyar NNPP.

Duk da dai ba a bayyana komai a hukumance ba, dukkan alamu sun nuna Kwankwaso ya dauki matakin siyasa mai tsauri.

A yanzu haka dai shugabannin jam’iyyar APC sun sa ido sosai yayin da ake ci gaba da tattaunawa kuma ana sa ran za a yanke hukunci nan da makonni masu zuwa.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when APA Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to APA Hausa:

Share