13/08/2026
Kar ki maida zaɓen gwamna na Osun ya zama yaƙi, Atiku ya gargaɗi gwamnatin tarayya
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya gargadi Gwamnatin Tarayya da INEC da jami’an tsaro kan amfani da karfin gwamnati wajen neman fifita wata jam’iyya a zaben gwamnan Jihar Osun.
Atiku ya bayyana hakan ne a yayin taron shugabannin matasan ADC na kasa da aka gudanar a Abuja, inda ya ce zaben Osun zai zama gwajin yadda Najeriya za ta iya gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya da adalci.
Ya ce yawan jami’an tsaron da aka tura domin gudanar da zaben ya yi k**a da shirin yaki, maimakon zaben dimokuradiyya.
Ya kuma bukaci INEC da ta tabbatar da cewa an kai kayan zabe a kan lokaci, an bai wa jama’a damar kada kuri’a ba tare da wata tangarda ba, sannan a gudanar da kirga da bayyana sak**akon zabe cikin gaskiya da kuma bayyananniyar hanya.
Atiku ya ce jami’an tsaro da INEC na kasa ne baki daya, ba na wata jam’iyya ba, yana mai kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa kuri’ar jama’a ce ta yanke hukunci a zaben Osun.
Atiku ya kuma sake yin kira da a binciki takardar shaidar kammala karatu daga Chicago State University da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa INEC, yana mai cewa akwai wasu bambance-bambance tsakanin takardar da aka gabatar da wata takarda da aka danganta da bayanan jami’ar.
Ya ce ya k**ata a tabbatar da sahihancin takardar da aka gabatar wa INEC, domin doka ta tanadi hukunci kan dan takarar da ya gabatar da takardar shaidar bogi.
A bangaren matasa kuwa, Atiku ya yi alkawarin cewa a karkashin tsarin siyasarsa, akalla kashi 30 cikin 100 na ‘yan takarar majalisun dokoki za su kasance ‘yan kasa da shekaru 40, tare da ba matasa masu shekaru kasa da 30 muhimmiyar dama.
Ya bukaci matasan Najeriya da su yi rajista, su shiga harkokin siyasa kuma su taka rawar gani wajen tsara makomar kasar.