11/08/2026
Gwamnatin Dikko Radda Za Ta Kafa Cibiyar Binciken Noma da Kiwo a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sanar da shirin gwamnatin jihar na kafa Cibiyar Binciken Harkokin Noma da Kiwo, domin ƙarfafa bincike, inganta hanyoyin noma da kiwo, tare da bunƙasa amfani da sabbin fasahohi wajen ƙara yawan amfanin gona da dabbobi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, lokacin da ya karɓi shugabannin Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), reshen Jihar Katsina, a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Katsina. Ya bayyana noma da kiwo a matsayin ginshiƙan tattalin arzikin jihar, yana mai cewa kusan kashi 90 cikin 100 na al’ummar Katsina suna dogaro da waɗannan fannoni kai tsaye ko a kaikaice.
Ya ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin sauya tsarin noma daga tsoffin hanyoyi zuwa tsarin zamani, ta hanyar samar da taraktoci, injinan noma, ban-ruwa, ingantattun iri, takin zamani da ƙara yawan malaman gona.
Gwamnan ya bayyana cewa an ɗauki malaman gona biyu daga kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 34 na jihar, tare da ba su babura da injinan feshi. Haka kuma, ana horas da mutum biyu daga kowace gundumar zaɓe cikin gundumomi 361 kan ingantattun hanyoyin noma da samar da iri masu inganci.
A wani mataki na bunƙasa noman rani, Gwamna Radda ya ce gwamnati na shirin gina rijiyoyin burtsatse guda 3,000, tare da farfaɗo da noman auduga a yankin Funtua da ƙarfafa noman zogale, ridi, waken soya, dawa da zobo.
Ya kuma bayyana shirin kafa cibiyoyin sarrafa amfanin gona da kuma gina katafaren wurin sarrafa nama na zamani a Katsina, domin ƙara darajar amfanin gona da dabbobi, samar da ayyukan yi da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga ga manoma da masu kiwo.
Gwamnan ya tabbatar wa manoma cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan magance matsalolin da ke fuskantar noman kankana, shinkafa, dankalin turawa mai ɗauke da sinadarin Vitamin A, da kuma kiwo.
A nasa jawabin, Shugaban AFAN na Jihar Katsina, Hon. Ya’u Umar Gwajo-Gwajo, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa matakan da ta ɗauka wajen inganta harkokin noma, musamman ƙara damar manoma samun filayen noma da kuma rarraba takin zamani cikin lokaci.
Wakilan manoman sun kuma nemi ƙarin saka hannun jari wajen sarrafa amfanin gona, samar da wuraren busar da amfanin gona, magance cututtukan amfanin gona da kuma ƙara samar da filayen noma.
Haka kuma, wakiliyar mata masu kiwon dabbobi ta yaba da shirin rabon awaki da gwamnatin jihar ta aiwatar, tare da yin kira da a faɗaɗa shirin domin ƙarin mata su samu damar cin gajiyarsa.