
07/08/2022
Ku Zabi Dikko Radda Cikin Ikon Allah Ba Zamu Yi Nadama Ba - Sakon Jikamshi Ga Katsinawa
Kwararrarren Masanin Tattalin Arziki kuma masani akan sha'anin Masana'antun wanda kuma shine Shugaban Hukumar Zuba Hannun Jari Ta Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Tukur Jiƙamshi, ya bayyana cewa al'ummar jihar Katsina ba zasu yi da na sani ba idan s**a ba Dr.Dikko Umar Radda damar zama Gwamnan Jihar.
Alhaji Ibrahim Tukur Jiƙamshi ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kammala wata ganawa ta musamman da dan takarar gwamnan jihar Katsina a karƙashin jam'iyyar APC, Dakta Dikko Umar Radda a Ofishin yakin neman zaɓensa dake cikin garin Katsina.
Jikamshi ya ja hankalin yan Jihar akan su fito kwansu da kwarkwatarsu su zazzaga wa Dr. Dikko Umar Radda kuri'unsu don ganin ya samu nasarar lashe zaɓen Gwamnan Jihar zabe mai zuwa.
Ya kara tabbatar da cewa ba za su taɓa yin nadama ba, saboda saboda gogewar Radda a fannoni daban-daban da s**a shafi cigaban al'umma da kuma tarin Ilimin Addini da na boko da yake da shi da kuma hangen nesa.
Shugaban Hukumar Kula Da Zuba Hannun Jarin ya kara da cewar, a wannan zaɓe mai karatowa na 2023, al'ummar jihar idan s**a dubi kafatanin yan takarar gwamnan jihar Katsina a jam'iyyu mabanbanta yana da wahalar gaske a samu nagartaccen dan takarar kamar Dr. Dikko Umar Radda.
Al'ummar Najeriya gaba daya sun amfana da irin kyakkyawan shugabancinsa na yadda ya riƙe Hukumar Kula Da Kanana Da Matsakaitan Masana'antun Ta Najeriya da kuma irin sauye-sauye da ya kawo a Hukumar cikin shekara biyar.
Alhaji Ibrahim Tukur Jiƙamshi ya cigaba da cewa jihar Katsina ana buƙatar matashin dattijo irin Dr. Dikko Umar Radda saboda irin baiwa da basira da kokarin ganin ya inganta rayuwar al'umma musamman matasa da kuma Kananan Masana'antun wanda ya ke da gogewa akan fannin.
''Ina da tabbacin zai kawo sauye-sauye masu ma'ana da za su inganta rayuwar al'umma jihar Katsina idan har s**a bashi dama ya zama Gwamnan Jihar''.