Humanity Hausa News

Humanity Hausa News Shafin wayar da kai ne game da rayuwa, ilimi, shugabanci da hakkokin al’umma. Tare muke gina al’umma muna da manufa mai kyau ga kowa
(1)

Muna taimaka wa matasa, iyaye, da shugabanni da dabarun rayuwa, kishin kasa da adalci.

KIMANIN 'YANJARIDA 248 GWAMNATIN ISRA' ILA TA KASHE A GAZA TUN FARA YUNKURINTA NA GANIN TA KORI AL'UMMA DAGA YANKINKiman...
03/09/2025

KIMANIN 'YANJARIDA 248 GWAMNATIN ISRA' ILA TA KASHE A GAZA TUN FARA YUNKURINTA NA GANIN TA KORI AL'UMMA DAGA YANKIN

Kimanin 'Yan jarida 248 gwamnatin' Yan mamaya ta Isra'ila ta kashe tun daga lokacin da ta ayyana yunkurin ganin bayan al'ummar Palasdinawa a zirin Gaza.
Wannan adadi ya zo ne bayan da sojojin mamaya na kasar s**a kashe wani danjarida Rasmi Salim,
mai aiki da gidan talabijin na Al'alam mallakin kasar Iran.
Shi dai Rasmi Salim, ya gamu da ajalinsa ne, ya yin da yake koma gida bayan ya tashi daga aiki, a lokacin da aka hate shi da jirgi marar matuki.
Rasmi, Dan shekara 29 ya kwashe kimanin shekaru takwas yana aiki da Kafar talabijin ta Al'alam kafin kashe shi. Abin da ya kawo adadin 'yanjarida 248 da Gwamnatin 'Yan mamaya ta hallaka, a kokarin ta na karya lagoon mane a labarai da suke aikin kawo Rahotanni abubuwan da suke faruwa a yankin.

Rahoton Musamman: Shin Gwamnatin Tinubu Na Mayar da Hankali Ne Kan Lagos Fiye da Jihohin Arewa?A cikin shekaru biyu kaca...
30/08/2025

Rahoton Musamman: Shin Gwamnatin Tinubu Na Mayar da Hankali Ne Kan Lagos Fiye da Jihohin Arewa?

A cikin shekaru biyu kacal na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jihar Lagos ta samu amincewar ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira tiriliyan 3.9 (₦3.9trn). Wannan adadi ya fi ninki jimillar ayyukan da dukkan jihohin Arewa da wasu daga yankunan Kudu s**a samu, wadanda gaba ɗayansu s**a kai kusan ₦3.56trn kacal. Wannan ya jawo cece-kuce a fagen siyasa da zamantakewa, musamman ganin yadda Arewa ta taka muhimmiyar rawa wajen zaben gwamnati mai ci.

Wani bangare da ya fi fito da wannan bambanci fili shi ne batun sabunta tashoshin jiragen sama, inda Lagos ta samu ₦712bn wajen inganta filin jirgin saman Murtala Muhammed, yayin da babban filin jirgin saman Kano ya samu ₦46bn kacal. Wannan rabo ya ninka sau goma sha biyar, abin da ya kara ƙarfafa zargin cewa ana fifita Lagos a kan sauran yankunan ƙasar.

Ra’ayoyi Daga Masana da Kungiyoyi

Dr. Kabiru Musa, masani a harkar tattalin arziki, ya bayyana cewa: “Idan aka ci gaba da irin wannan rabon albarkatun da bai daidaita ba, zai iya haifar da gibin rashin amincewa tsakanin jihohi. Adalci a rabon albarkatun ƙasa shi ne ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban Najeriya.”

Shi ma Kakakin Kungiyar Matasa ta Arewa (NYA) ya ce a cikin wata sanarwa: “Ba mu adawa da ci gaban Lagos, amma bai k**ata a bar sauran yankuna a baya ba. Muna kira ga gwamnatin tarayya ta tabbatar da daidaito domin kowace jiha ta amfana da rabon albarkatun ƙasa yadda ya dace.”

Kammalawa

Rahoton ya nuna cewa akwai babban gibi a tsarin rarraba ayyukan ci gaba tsakanin Lagos da sauran jihohi, musamman Arewa. Masu lura na ganin cewa idan gwamnati ba ta gyara wannan tsari ba, zai iya shafar haɗin kai da amincewar jama’a ga tsarin tarayya. Lokaci ya yi da gwamnati za ta samar da ingantaccen tsarin rabon ayyuka, domin kowace jiha ta ji tana da daraja da muhimmanci a cikin ƙasar.

BA SHAWARI NAKE NEMA BA.A Musanya ni da DCP Abba Kyari...inji Matashi Abu AshrafBUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA GWAMNATIN TARAYYA:Z...
29/08/2025

BA SHAWARI NAKE NEMA BA.

A Musanya ni da DCP Abba Kyari...inji Matashi Abu Ashraf

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA GWAMNATIN TARAYYA:

Zuwa ga Gwamnatin Tarayya, Hukumar NDLEA, Federal High Court da kuma Supreme Court.

Ni Yahuza Shehu Allah Gaba, wanda akafi sani da Abu Ashraf.

Daga Jihar Bauchi, Nigeria. 🇳🇬

Kamar yadda na faɗi, cewa bani nema ko ɓuƙatar shawarin kowa akan wannan ƙudirin da na hukunta wa kaina, bayan yardan Mahaifiyata!

A shirye nake, idan har baici karo da dokar Ƙasa ba, wato "constitution" na amince matuƙar hakan mai yiwuwa ne, a saki DCP Abba Kyari, ta hanyar bayar da belinsa a kuma bashi dama ya cigaba da aikinsa na yaƙi da ta'addanci da 'yan ta'addan du s**a hana Ƙasar mu Nigeria 🇳🇬 zaman lafiya, musamman yankin mu na Arewa, a maye gurbinsa dani har zuwa lokacin da za'ayi hukunci da adalci akan zargin da akeyi masa wanda muna da yaƙinin bai aikata ba!

Idan kuma aka sameshi da laifi, ni Abu Ashraf na yarda na kuma amince a hukuntani a madadinsa! Matuƙar za'a barshi ya cigaba da aikin samar da tsaro ta hanyar kawo ƙarshen ta'addanci da 'yan ta'adda.

Babu wasa ko neman suna ko kokwanto cikin wannan saƙo nawa! Don haka hukumar tsaron Nigeria tun daga Police, 🚓 SSS, DSS, CIVIL DEFENCE, NDLEA, ARMY, NAVY, AIR FORCE, IMMIGRATION, PRISON SERVICE, CUSTOM, su sani kuma su zama shaida, matuƙar tsarin mulkin ƙasa ya ba daman maye gurbin wani da wani wallahi a shirye nake a gayyaceni!

Saboda Arewa babu tsaro sai tsoro! Fitinar da ke kunno kai, zai mamaye gami da cinye Arewa da 'yan Arewa idan muka zauna muka cigaba da zuba ido, cewa maciya amana cikin Shuwagabannin mu zasu iya tsare mana lafiya, rayuka da dukiyan mu!

Ga manyan ɓarayi suna yawo da jiniya (Siren 🚨), ba'a k**asu ba b***e a hukuntasu! A k**a wanda yake hana idonsa bacci don mu muyi bacci.

LAUYOYIN DCP ABBA KYARI GAREKU

Ga lambobin wayana:
08034441771,
08020822227,
08035243919.

I have said it and i will repeat it once again, bani buƙatar shawarin ka/ki matuƙar ba adu'a da ƙarfafa guiwa gare zakuyi.

FAƊI ALKHAIRI KO KAYI SHRIRU.🤫

29/08/2025

Awa24 Tv online

Ka na da labari na ƙorafi, tauye haƙƙi ko cin zalun da kake so mu taya ka yaɗawa?aza garzayo gare mu, zamu buga maka lab...
29/08/2025

Ka na da labari na ƙorafi, tauye haƙƙi ko cin zalun da kake so mu taya ka yaɗawa?aza garzayo gare mu, zamu buga maka labari kyauta madamar akan gaskiya ka gina labarin naka. Humanity Hausa News muryar mara Murya dama mai muryar.

"Matsalar Rashin Tsaro A Katsina Abin Duk Rurutawa ce Ta Ƴan Adawa—Dikko Raɗɗa da Tinubu za su lashe zaben 2027"Inji Dan...
29/08/2025

"Matsalar Rashin Tsaro A Katsina Abin Duk Rurutawa ce Ta Ƴan Adawa—Dikko Raɗɗa da Tinubu za su lashe zaben 2027"

Inji Dan Majalisar Kankia, Hon. Abdu Kwaskwaro.

Ɗan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Kankia, Hon. Abdu Kwaskwaro, ya bayyana cewa akasarin hayaniyar da ake ta yi kan matsalar tsaro a jihar, yan adawa ne s**a fi ruruta ta fiye da yadda lamarin yake a zahiri.

A cewarsa, duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan jihar, gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Dikko Umar Radda tana yin iyakar ƙoƙarinta wajen ganin an shawo kan matsalar.

Hon. Kwaskwaro ya ƙara da cewa, bisa hangen nesansa na siyasa, Gwamna Dikko tare da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne za su lashe babban zaɓen shekarar 2027.

Har yanzu dai mutanen jahar ta kantsina suna ci gaba da mamakin wannan batu na ɗan siyasar, musamman ganin yanda lamarin tsaron ya ƙara dagulewa a jahar,, ƴan nindiga na ci gaba da cin karen su babu babbaka ta hanyar sarayar da rayukan talakawa da kuma sace su domin neman kuɗin fansa, amma a sami wani daga cikin wakilan al'ummar ya siyasantar da rayukan da ya k**ata ya kare.

26/08/2025

Ranar Hausa Ta Duniya Idan Kana Alfahari da Yaren Hausa Ka Ajiye Mana Karin Maganar da Kafi So A Ranka!

NLC Ta Yi Alkawarin Matsawa Gwamnati Kan Biyan Bashin N-PowerƘungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta sha alwashin matsa wa...
26/08/2025

NLC Ta Yi Alkawarin Matsawa Gwamnati Kan Biyan Bashin N-Power

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta sha alwashin matsa wa Gwamnatin Tarayya lamba domin ta gaggauta biyan kuɗaɗen alawus-alawus da ake bin masu amfana da shirin N-Power bashi.

Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa da aka yi a jiya tsakanin shugabannin NLC da wakilan Ƙungiyar Ƙasa ta Masu Amfana da Shirin N-Power, wacce aka ce ta gudana cikin nasara.

A cikin bayanin da Ƙungiyar ta fitar, an bayyana cewa NLC ta yi alkawarin rubuta wasiƙu kai tsaye ga Ministan Harkokin Jin Kai da kuma Ministan Kuɗi, tana neman a fara biyan kuɗaɗen nan take ba tare da wani jinkiri ba.

Haka kuma, NLC ta ƙara da cewa za ta sanya wa gwamnati tak**aiman wa’adi, inda ta yi gargaɗi cewa idan gwamnati ta kasa aiwatar da wannan bukata a cikin lokacin da aka tsara, to za a ɗauki matakan da s**a dace.

Ƙungiyar ta kuma shawarci duk masu amfana da shirin N-Power da su ci gaba da matsa lamba ta hanyoyi daban-daban ta kafafen sada zumunta da kuma ta zahiri domin tabbatar da cewa muryarsu tana ƙara samun tasiri.

Taron ya samu halartar mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa na NLC, tare da wakilan ƙungiyoyin NUPENG, PENGASSAN, NUJ da kuma shugabannin N-Power na ƙasa.

Ƙungiyar Masu Amfana da Shirin N-Power ta nuna godiyarta ga NLC bisa goyon bayan da ta nuna, tare da kira ga duk masu amfana da shirin da su kasance tsintsiya madauri ɗaya a wannan fafutuka.

25/08/2025

MI YA SA HUKUMOMI A NIGERIA SUKE TSARE DA SHUGABAN AL'UMMAR PALATINE?

Myanmar : Shekaru takwas bayan tilastawa 'yan Kabilar Rohingya gudun hijira,  Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin da k...
25/08/2025

Myanmar : Shekaru takwas bayan tilastawa 'yan Kabilar Rohingya gudun hijira, Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin da ke fuskantarsu yana kara k**ari.

Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya (OHCHR) ta yi kira da a kawo karshen rashin hukunta masu hannu a cin zarafin da ake yi wa ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Kakakin hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar dinkin duniya Jeremy Laurence ya ce, "Ƙawo karshen rashin hukunta masu laifi da tabbatar da 'yanci tsaro na' Yan kasa ga ' Yan Kabilar Rohingya gami da samar da daidaito suna da mahimmanci don dakile yanayin tashin hankalin,"

Kimanin Mutane miliyan daya daga cikin tsirarun musulmin kasar ne s**a tsere daga harin da sojoji s**a kaddamar a ranar 25 ga watan Agustan 2017, yakin da masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya s**a bayyana a matsayin "yunkurin share wata kabila".

Wasu ruhotannin sun bayyana cewa, "Fiye da 'Yan Kabilar Rohingya miliyan guda ne s**a tsallaka zuwa kasar Bangladesh inda suke ci gaba da zama a sansanonin' Yan gudun hijirar da ba su da ra'ayin komawa gida, kuma galibi ana hana su zama 'yan kasa da basu sauran hakkokinsu."

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ta ce tana bukatar kusan dala miliyan 256 domin tallafawa ‘yan Kabilar ta Rohingya da s**a rasa matsugunansu a wannan shekarar,Saidai hukumar ta samu alkawuran kusan kashi 38 cikin 100 na kudaden.

"Muna kira ga al'ummar duniya da su kara kaimi wajen tallafawa 'yan Rohingya ta hanyar kara tallafin jinkai don samun damar biyan bukatu da muhimman ayyuka," in ji shi.

Address

Katsina
820001

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Telephone

+2348024449793

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Humanity Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Humanity Hausa News:

Share

Category