Humanity Today

Humanity Today Shafin wayar da kai ne game da rayuwa, ilimi, shugabanci da hakkokin al’umma. Tare muke gina al’umma muna da manufa mai kyau ga kowa
(1)

Muna taimaka wa matasa, iyaye, da shugabanni da dabarun rayuwa, kishin kasa da adalci.

02/08/2026
02/08/2026

Allah yayi Wa Ƙosan Waƙa Rasuwa

**Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.**Allah ya yiwa Shahararren mawaƙin siyasa Kosan Waka rasuwa.  Allah ya jikan shi d...
02/08/2026

**Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.**

Allah ya yiwa Shahararren mawaƙin siyasa Kosan Waka rasuwa.

Allah ya jikan shi da rahama, ya gafarta masa dukkan zunubansa, ya haskaka kabarinsa, kuma ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Mun yi masa addu’a da kuma ga iyalansa da abokansa. Allah ya ba su hakuri da imani.

Ameen.

📢 HUMANITY TODAY — YOUR VOICE, YOUR STORY, YOUR PLATFORM 🌍Do you have a story to share, a complaint to report, a human r...
31/07/2026

📢 HUMANITY TODAY — YOUR VOICE, YOUR STORY, YOUR PLATFORM 🌍

Do you have a story to share, a complaint to report, a human rights concern, an unusual experience, breaking news, or important information that deserves public attention?

Humanity Today is here to listen and give your voice a platform.

📰 We welcome:
• Human-interest stories and community issues
• Complaints and reports of rights violations
• Extraordinary and inspiring stories
• Breaking news and important updates
• Business advertisements and promotional content
• Public announcements and information of community interest

📩 Get in touch with us:

📧 Email: [email protected]
📞 Call/WhatsApp: 08024449793 | 07033397038
📥 Facebook Inbox: Humanity Today
▶️ YouTube: Humanity TV
🎵 TikTok: Hamanity

📸 You can send us your story, photos, videos, or relevant evidence, along with the necessary details.

Humanity Today — We listen. We report. We give people a voice. 🤝🌍

📢 HUMANITY TODAY — MURYAR AL’UMMA 🌍Kuna da labari, korafi, matsalar take haƙƙi, wani abu mai ban mamaki, ko wani muhimmi...
31/07/2026

📢 HUMANITY TODAY — MURYAR AL’UMMA 🌍

Kuna da labari, korafi, matsalar take haƙƙi, wani abu mai ban mamaki, ko wani muhimmin bayani da kuke son jama’a su sani? Ku tuntuɓe mu!

📰 Muna karɓar:
• Labaran al’umma da abubuwan da s**a shafi ɗan Adam
• Korafe-korafe da rahotannin take haƙƙi
• Abubuwan ban mamaki da labarai masu jan hankali
• Labaran gaggawa da muhimman abubuwan da s**a shafi al’umma
• Tallace-tallace da sanarwar kasuwanci
• Wasu muhimman bayanai da s**a dace a isar da su ga jama’a

📩 Hanyoyin Tuntuɓarmu:
📧 Email: [email protected]
📞 Kira/WhatsApp: 08024449793 | 07033397038
📥 Inbox: Humanity Today
▶️ YouTube: Humanity TV
🎵 TikTok: Hamanity

📸 Ku aiko mana da labari, hoto ko bidiyo tare da cikakken bayani.

Humanity Today — Muna sauraron ku, muna isar da saƙonku. 🤝🌍

Subscribe to get exclusive benefits:
https://www.facebook.com/insaniyyah/subscribenow

Babbar Mai Shari'a ta kasa ta haramta amfani da sunan Barrister ga LauyoyiBabbar Alƙaliyar Najeriya, Mai Shari’a Kudirat...
31/07/2026

Babbar Mai Shari'a ta kasa ta haramta amfani da sunan Barrister ga Lauyoyi

Babbar Alƙaliyar Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, dauki mataki ma Lauyoyi, inda ta haramta masu amfani da kalmar Barrister a gaban sunayensu a duk wata hulda da Kotun koli. Wannan na junshe a cikin takardar sanarwa da Babban Magatakardan Kotun Koli, Kabir Akanbi, ya sanya wa hannu, a ranar 13 ga watan Yuli 2026. Sanarwar ta umurci lauyoyi, ma’aikatan shari’a, magatakarda da duk wanda ke aiki da Kotun Koli da su daina amfani da taken a wasiƙu, bayanan aiki, katunan shaida da sauran takardun hukuma.
Babbar mai shari'ar ta bayyana cewa, ci gaba da amfani da kalmar “Barrister” bai yi daidai da matakin ƙwarewar aiki da Kotun Koli ke ƙoƙarin tabbatarwa ba.Umarnin ya fara aiki nan take.
Wannan mataki na da nufin ƙara daidaita tsarin takardu da ƙara ƙwarewar aiki a cikin babbar kotun ƙasa.

31/07/2026

Me kuku fahimta a wannan video? Ku bayyana mana a Comment section.

WANI ABU DA BA KU SANI BA GAME DA RAYUWAR LIONEL MESSIMutane da yawa sun san Lionel Messi a matsayin gwarzon ƙwallon ƙaf...
28/07/2026

WANI ABU DA BA KU SANI BA GAME DA RAYUWAR LIONEL MESSI

Mutane da yawa sun san Lionel Messi a matsayin gwarzon ƙwallon ƙafa, amma kaɗan ne s**a san cewa yana ɗan shekara 11 aka gano yana da matsalar rashin isasshen sinadarin girma (Growth Hormone Deficiency). Likitoci sun ce idan ba a yi masa magani ba, watakila ba zai yi tsayin da zai ba shi damar taka ƙwallon ƙafa a matakin koli ba. Iyalinsa ba su iya ɗaukar kuɗin maganin ba, har sai Barcelona ta amince ta biya kuɗin jinyarsa bayan ta ga irin baiwar da yake da ita. Abin mamaki shi ne, har yanzu Messi yana ɗaya daga cikin ƴan wasan da ba sa yawan magana a ɗakin canji, ya fi barin ƙafafunsa su yi magana a filin wasa.

Wani abin da ba kowa ya sani ba shi ne cewa kwantiragin farko da Barcelona ta yi da Messi an rubuta shi ne a kan takardar "napkin" saboda masu kula da ƙungiyar ba sa son wata ƙungiya ta riga su ɗaukarsa. Haka kuma, Messi ya ƙi tayin buga wa ƙasar Spain wasa duk da cewa yana da damar yin hakan, saboda ya ce burinsa tun yana yaro shi ne ya wakilci Argentina. A rayuwarsa ta sirri kuma, ya auri budurwar da ya sani tun suna yara, Antonela Roccuzzo, abin da ya sa ake kallon rayuwarsa a matsayin mai natsuwa idan aka kwatanta da ta wasu fitattun 'yan wasa.

Duk da wannan nasara, rayuwar Messi ba ta rasa ƙalubale ba. A shekarar 2016, shi da mahaifinsa sun fuskanci shari'ar kauce wa biyan haraji a Spain, kuma kotu ta same su da laifi, lamarin da ya jawo s**a daga mutane da dama. Sai dai daga baya Messi ya ci gaba da mayar da hankali kan ƙwallon ƙafa, inda ya cika babban burinsa na lashe Kofin Duniya da Argentina, abin da ya ƙara tabbatar da matsayinsa a tarihin wasan ƙwallon ƙafa.

RUNDUNAR 'YAN SANDA A JIHAR KEBBI TA KADDAMAR DA WANI SAMAME DON CETO BABBAN ALKALIN DA' YAN BINDIGA S**A SACERundunar '...
27/07/2026

RUNDUNAR 'YAN SANDA A JIHAR KEBBI TA KADDAMAR DA WANI SAMAME DON CETO BABBAN ALKALIN DA' YAN BINDIGA S**A SACE

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta ƙaddamar da wani gagarumin samame domin ceto Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari'a Faruku Hassan Bunza, wanda ake zargin 'yan bindiga sun yi garkuwa da shi a ƙaramar hukumar Bunza ta jihar.
Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce rundunar ta gaggauta ɗaukar mataki bayan samun rahoton gaggawa.
Ya bayyana cewa Kwamishinan 'Yan Sandan jihar, CP Umar Muhammad Hadejia, ya bayar da umarnin tura jami'an rundunonin musamman da na tattara bayanan sirri nan take domin tabbatar da ceto alƙalin cikin koshin lafiya.
A cewarsa, jami'an tsaro sun fara gudanar da bincike mai zurfi a wuraren da aka gano suna da haɗari, ciki har da dazukan da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutanen na iya buya a cikinsu.

Kimanin mutane  30 ne 'yan bindiga s**a hallaka a jihar KadunaWasu 'yan bindiga masu yawa sun kai hari a daren Lahadi a ...
27/07/2026

Kimanin mutane 30 ne 'yan bindiga s**a hallaka a jihar Kaduna

Wasu 'yan bindiga masu yawa sun kai hari a daren Lahadi a ƙauyen Naridon da ke gundumar Kamaru, a Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna, inda s**a kashe kimanin mutum 30.
Saidai rundunar 'yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Dangin waɗanda abin ya shafa da mazauna yankin sun bayyana abin da ya faru ga kafar yada labarai ta DAILY POST cewa, "Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 30 sakamakon harin 'yan bindigar. Har yanzu mutane da dama sun ɓace domin sun gudu saboda tsira da rayukansu. Haka kuma mutane da yawa sun jikkata, kuma an kai su cibiyoyin lafiya domin samun magani."
Majiyar tamu ta kara da cewa, "An ƙone gidaje da dama, sannan an lalata dukiyoyi na miliyoyin naira."
Harin 'yan bindigar ya ya jefa al'ummar yankin cikin jimami, tare da nuna fargabar cewa adadin waɗanda s**a mutu na iya ƙaruwa yayin da ake ci gaba da tattara bayanai da tantance halin da ake ciki bayan harin.

Saidai an yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su gaggauta ƙarfafa matakan tsaro a yankunan da abin ya shafa domin dawo da zaman lafiya, tare da ba manoma damar komawa gonakinsu.

Address

Katsina
820001

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Telephone

+2348024449793

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Humanity Today posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Humanity Today:

Share

Category