The Fact 24/7

The Fact 24/7 Media Company

Tinubu Na Tsaka Mai Wuya Akan Zaben MataimakiDaga Aliyu U. TildeDaga ina zan dauki mataimakin sa? Wannan ita ce damuwar ...
10/06/2022

Tinubu Na Tsaka Mai Wuya Akan Zaben Mataimaki

Daga Aliyu U. Tilde

Daga ina zan dauki mataimakin sa? Wannan ita ce damuwar Bola Ahmed Tinubu, dantakarar shugaban kasa a APC, a yanzu.

Ba k**ar Atiku na PDP ba, wanda kai tsaye ya san daga kudancin Nijeriya zai dauko nasa, kuma Kirista, walau daga cikin Inyamurai ko daga y’an Neja Delta.

Shi Tinubu yana tsaka mai wuya. A Arewa wa zai dauka? Musulmi ko kirista?

Mutanensa Kirista irin su Babachir Lawal sun ce in ya dauki Musulmi tabbas ba zai ci zabe ba, saboda Kiristoci za su gwammace zabar Atiku wanda yake da Kirista mataimaki. Suna ganin lokaci ya canza ba k**ar zamanin Abiola da Kigibe ba.

A daya bangaren kuwa, idan Tinubu ya dauki Kirista, to Musulmi yan’arewa wadanda su ne wadanda s**a fi yawa a Arewa za su ga cewa an mai da su tsiraru, yankallo, abunda ba a taba yi ba a mulkin Nijeriya. Haka zai sa su runtuma wajen Atiku.

Da na sa wannan rubutu a Facebook, wani maibibiya ta ya ce dole Tinubu ya zabi dayan biyu: Idan adalci yake so, ya dauki Kirista; idan kuwa cin zabe yake so, to, ya dauki Musulmi. A yanzu wanne ne TInubu ke bukata: adalci ko cin zabe? Kar kuma ya yi kamun gafiyar ‘Baidu.

Da alama dai duk inda Tinubu ya yi, Atiku zai ce gaba ta kai shi. Ga shi magudi yana kara wuya. Ga shi ba zaben fid da gwani ba ne na mutane kalilan b***e a ce Dola za ta yi aiki. Ga INEC ta matsa ta ce cikin sati guda kowane ya fito da mataimakinsa.

Gaba kura, baya siyaki. Ni Tinubu! Ina zan sa kai na?

In da kai ne Tinubu, ya za ka yi?

Dr. Aliyu U. Tilde
10 Yuni 2022

GANGANCI NE ZABEN APC A 2023Daga Bello Muhammad SharaɗaIdan mutum ya tsufa, ba neman shugabanci ne ya hau shi ba, a yanz...
10/06/2022

GANGANCI NE ZABEN APC A 2023

Daga Bello Muhammad Sharaɗa

Idan mutum ya tsufa, ba neman shugabanci ne ya hau shi ba, a yanzu babu abin da ya dace da tsoho mai rauni sai hutu da ayyukan jinkai da ibada.

Magana ta gaskiya Bola Adekunle Ahmed Tinubu, a shekararsa 70, ya tsufa, ya gaji, amma da karfin tsiya gwamnonin APC s**a dankarawa mutanen Najeriya shi, don ya maye gurbin Buhari a 2023.

Ya matsu, ko ana so ba a so, wai burinsa ne "My life time ambition" kuma yadda yake fada kujerar shugaban kasa a 2023 ta Yarabawa ce, a Yarbawan kuma tasa ce, wai don ya wahala.!!!

HABA JAMA'A !!!

Sakan goma sha shida fa Bola Ahmed Tinubu ya yi kafin ya buda shafi na biyu a takardar da aka rubuta masa ya karanta a gaban dalaget ranar Talata wajen zaben fidda gwani.

Tsufan Bola Ahmed Tinubu ya kai ko sakan biyar ba zai iya yi ba, yana rike da tutar takarar shugabancin Najeriya ta APC da aka bashi, gagararsa tayi, sai da shugaban kasa Muhammad Buhari da shugaban jam'iyya na kasa Sanata Abdullah Adamu s**a taya shi riketa.

Salla sai dai ya yi a zaune. Ga gigin tsufa da saurin mantuwa.

Amma a haka, wai shi ne zai tashi haikan cikin shekara hudu zai farfado da Najeriya, har karfin tattalin ta, wato GDP ya karu da kashi 12.

KARYAR FARKO DA APC ta fara yi mana.
Haka Bayo Ononuga

Fata Na Allah Ya Kara Tsarkake Mani Zuciya Ta Wurin Kyautatawa Al'umma Idan Na Zama Gwamnan Jihar Katsina -  Cewar Dan T...
10/06/2022

Fata Na Allah Ya Kara Tsarkake Mani Zuciya Ta Wurin Kyautatawa Al'umma Idan Na Zama Gwamnan Jihar Katsina - Cewar Dan Takarar Jam'iyyar Accord

Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam'iyyar Accord Dr. Muhammad Bara'u Tanimu, ya yi fatan cewa Allah SWT ya tsarkake mashi zuciyar shi ta fuskar inganta rayuwar al'umma idan Allah ya bashi damar zama Gwamnan Jihar.

Dr. Muhammad Bara'u Tanimu na magana ne a lokacin da Shuwagabannin Jam'iyyar na Jiha s**a kaddamar da shi a matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina a zaben Shekarar 2023 da ke tafe.

Dan Takarar Gwamnan wanda kuma shine Shugaban sanannar Gidauniyar nan ta tallafawa al'umma a Jihar wato, ''ISLAND SURVIVE FOUNDATION'', ya ce fatan shi ya samu kwarin gwuiwar fadada ayyukan cigaba da gidauniyar tashi ta saba yi idan ya zama Gwamnan Jihar Katsina.

A cewar shi, batun Inganta Tsaro wanda a halin yanzu ya tabarbare, batu ne da ke bukatar a shawo kan shi daga tushe, kuma tabbatar da adalci a tsakanin dukkan al'umma tare da koya wa matasa sana'oin dogaro da kai shine zai sanya a gaba wurin ganin an shawo kan matsalar.

Dr. Muhammad Bara'u Tanimu ya ce zai yi amfani da tsarin Gidauniyar shi ta fuskar aiwatar da cigaban al'umma, wanda sanin kowa ne gidauniyar ta yi dumbin shirye-shirye da s**a taba rayuwar mabukata kai tsaye.

Dan Takarar ya yi fatan cewa al'ummar Jihar Katsina zasu duba chanchantar shi kuma su bashi dama don ganin ya yi amfani da basirar da Allah ya bashi ta fuskar inganta rayuwar su.

A nashi jawabin, Shugaban Jam'iyyar Accord na Jihar Katsina Muhammad Boyi, ya che Dan Takarar nasu yana da kwarin gwuiwar tafiyar da Jihar Katsina bisa gaskiya da adalci.

A sabili da haka ne ya yi fatan cewa Jama'ar Jihar zasu kalli chanchantar shi kuma su kada mashi kuri'ar su a lokacin zaben game gari domin ganin ya samu nasara.

Sauran wadanda s**a maganta a lokacin taron, sun yi magana mai tsawo akan nagartar Dr. Muhammad Bara'u Tanimu ta fuskar shugabancin al'umma.

Sun kuma yi magana mai tsawo akan irin dumbin ayyukan taimakon al'umma da Dan Takarar ya aiwatar a fadin Jihar Katsina ba tare da yana rike da wani mukamin siyasa ba, sai s**a yi fatan cewa idan Allah ya tashi damar zama Gwamnan Jihar Katsina wadannan ayyuka zasu fadada.

An K**a Yan Damfara Ta Yanar Gizo (Yahoo) Su 140 A Wani Otel Din LegasHukumar EFCC a Najeriya ta k**a mutum 140 da ake z...
10/06/2022

An K**a Yan Damfara Ta Yanar Gizo (Yahoo) Su 140 A Wani Otel Din Legas

Hukumar EFCC a Najeriya ta k**a mutum 140 da ake zargi suna damfara ta Intanet wanda ake kira "yan yahoo" a wani otel da ke Legas

Jami'in yaɗa labarai na hukumar, Mista Wilson Uwujaren, ya ce mutanen masu shekara tsakanin 16 zuwa 42, an k**a su ne a wasu otel biyu da ke yankin Ikorodu.

Uwajaren ya ce kamen ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan ayyukan da suke aikatawa na kutse da damfara a shafukan Intanet.

Abubuwan da aka k**a matasan da su sun hada da motocin alfarma da naurorin laturoni da kamfutoci da kuma wayoyin hannu.

Za a gabatar da matasan a gaban kotu nan bada jimawa ba, a cewar jami'in.

Yadda Al'umma Ke Kokawa Akan Wasu  Hanyoyi Da Ke Tara Ruwa A Kofar Kwaya Cikin Birnin Katsina....Abin Kaicho, Masu Sana'...
10/06/2022

Yadda Al'umma Ke Kokawa Akan Wasu Hanyoyi Da Ke Tara Ruwa A Kofar Kwaya Cikin Birnin Katsina
....Abin Kaicho, Masu Sana'a Kusa Da Wurin Suna Da Karfin Gyara Hanyoyin Amma Sun Yi Burus Suna Jiran Gwamnati Ta Gyara.

Masu amfani da ababen hawa na cigaba da kokawa akan yanayin da wasu hanyoyi ke ciki a gefen gidan man Danmarna da gefen masu saida Mashina da ke Kofar Kwaya a cikin Birnin Katsina.

Su dai wadannan hanyoyi sun kasance wadanda masu ababen hawan ke amfani da su a sabili da aikin gada da gwamnati ke gudanarwa a shatale-talen Kofar Kwaya.

A sa'ilinda The Fact 24/7 ta ziyarci wurin, duka hanyoyin biyu sun chunkushe, babu inda ruwa zai bi ya wuce, musamman a wannan yanayi na damina da ake ciki.

Sai dai abin kaicho, The Fact 24/7 ta lura da cewar, wadannan hanyoyi ba wani babban aiki suke bukata ba, amma masu sana'a a wuraren sun yi kunnen uwar shegiya akan matsalar suna jiran sai gwamnati ta zo ta gyara wuraren.

Har ila yau, duk da cewar su kansu masana'antu da suke a wurin suna cikin yanayi na rashin jin dadin gudanar da harkoki a sabili da wannan matsala, amma jira suke sai an zo an gyara ba tare da su sun bada gudummuwa ba ta wannan fuska.

The Fact 24/7 ta lura da cewar, a gefen wadannan hanyoyi akwai masana'ntu da s**a hada da Gidan Mai da Gidan Sayar Da Taya gami da Wurin sayar da mashina na Kofar Kwaya da sauran masana'antu.

Duk da cewa gwamnati ita ce da alhakin gyara irin wadannan wurare, amma akwai aikin taimakon al'umma da ya rataya a wuyan kamfanoni da masana'antu a tsarin Kasar nan, amma duk da haka masana'antu da ke wannan wuri sun kauda wuya akan wannan hanyoyi.

Wasu masu ababen hawa da aka zanta da su, sun yi roko ga gwamnati akan ta kawo dauki ta hanyar gyara wadannan wurare tunda dai makwabtan wurin da ke Sana'a sunyi ko in kula akan lamarin.

Zaben 2023 : Jerin Sunayen Jam'iyyu Da Yan Takarar Kujerar Shugabancin Ƙasa Na Jam'iyyun1. Accord (A) : Christopher Imum...
10/06/2022

Zaben 2023 : Jerin Sunayen Jam'iyyu Da Yan Takarar Kujerar Shugabancin Ƙasa Na Jam'iyyun

1. Accord (A) :
Christopher Imumolen.

2. Action Alliance (AA) :
Dr Major Hamza Al Mustapha

3 Action Democratic Party (ADP) :
Yabagi Sani

4. African Action Congress (AAC) :
Omoyele Sowore

5. African Democratic Congress (ADC) :
Dumebi Kachikwu

6. All Progressives Congress (APC) :
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

7. All Progressives Grand Alliance (APGA) :
Peter Umeadi

8. Allied Peoples Movement (APM) :
Yusuf Mamman Dantalle

9. Boot Party (BP) :
Sunday Adenuga

10. Labour Party (LP) :
Peter Obi

11. National Rescue Movement (NRM) :
Okwudili Nwa-Anyajike

12. New Nigeria Peoples Party (NNPP) :
Rabiu Musa Kwankwaso

13. Peoples Democratic Party (PDP) :
Alhaji Atiku Abubakar.

14. Peoples Redemption Party (PRP) :
Kolawole Abiola Latifu

15. Social Democratic Party (SDP) :
Adewole Adebayo

16. Young Progressive Party (YPP) :
Prince Malik Ado-Ibrahim

17. Zenith Labour Party (ZLP) :
Chief Dan Nwanyanwu

Da In Zabi Atiku Ko Tinubu Gwara Na Yi Asarar Kuri'a Ta - Cewar Aisha Yusuf.Sanannar Mai Rajin Kare Hakkin Bil'adama A N...
10/06/2022

Da In Zabi Atiku Ko Tinubu Gwara Na Yi Asarar Kuri'a Ta - Cewar Aisha Yusuf.

Sanannar Mai Rajin Kare Hakkin Bil'adama A Najeriya Aisha Yusuf, Ta Bayyana Cewar Wasa Ne Da Rayuwar Ta Ne Zaben Atiku Ko Tinubu, A Sabili Da Haka Gwara Ta Yi Asarar Kuri'ar Ta Da Ta Zabi Daya Daga Cikin Su.

An Sanar Da Litinin A Matsayin Ranar Hutu Domin Bikin Ranar DamakaradiyyaGwamnatin Tarayya ta sanya ranar Litinin 13 ga ...
10/06/2022

An Sanar Da Litinin A Matsayin Ranar Hutu Domin Bikin Ranar Damakaradiyya

Gwamnatin Tarayya ta sanya ranar Litinin 13 ga Mayun wannan shekara ta 2022 a matsayin hutun aiki ga kowa da kowa a Nijeriya.

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a ranar Alhimis din nan, inda ya ce Gwamnatin Tarayya ta sanya hutun ne domin murnar zagayowar ranar dimokaradiyya a Nijeriya da ta k**a ranar Lahadi 12 ga watan Yuni.

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Sama Da 80 A Karamar Hukumar Jibia.... Sun Maida Sama Da Mutane 2000 Yan Gudun Hi...
09/06/2022

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Sama Da 80 A Karamar Hukumar Jibia
.... Sun Maida Sama Da Mutane 2000 Yan Gudun Hijira.

Ƴan Bindiga Su Sama Da 200 A Saman Babura, Sun Kai Wani Mummunan Hari A Kauyen Faru Dake Cikin Karamar Hukumar Jibia A Jihar Katsina.

K**ar Yadda Majiyar Mu Ta Tabbatar Yan Bindigar Sun Yi Awon Gaba Da Mata Da Kananan Yara Sama Da Tamanin,Tare Da Kone Gidaje Da Kuma Maida Sama Da Mutum Dubu Biyu Ƴan Gudun Hijira.

Majiyar Jaridar Focus News Hausa Ta Shaida Mata Cewa, Yan Bindigar Dauke Da Bindigogi, S**a Yi Wa Garin Kawanya S**a Yi Ta Harbin Mai Kan Uwa Da Wabi, S**a Cigaba Da Farfasa Shaguna Tare Da Kone Gidajen Kauyen.

A Halin Yanzu Kimanin Sama Da Dubu Biyu Ke Zaman Gudun Hijira A Garin Magamar Jibia Da Kuma Karamar Hukumar Jibia.

Dan Shekara 18 Ya Kashe Uwa Da Danta A Jihar Adamawa, Yayin Da Ya Je Yi Mata Fyade hukumar ‘yan sanda ta jihar Adamawa, ...
09/06/2022

Dan Shekara 18 Ya Kashe Uwa Da Danta A Jihar Adamawa, Yayin Da Ya Je Yi Mata Fyade

hukumar ‘yan sanda ta jihar Adamawa, a ranar Litinin 6 ga watan Yuni, ta k**a wani dan shekara 18 da ake zargi da mummunan kisa ga wata mata mai suna Talatu Alh. Usman, da dan ta dan shekara daya, a karamar hukumar Lamurde dake jihar Adamawa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda mai suna SP Suleiman Nguroje, ya bayyana cewa, mai laifin Volamu Kalbes, da kuma wadda aka hallaka, suna zaune ne gidajen dake a kauyen Sabon Layi dake karamar hukumar Lamurde.

Wanda ake zargin ya farma matar ne a bakin kogi, inda ta je domin yin wanka, tare da danta a gefen ta.

Marigayiyar tayi kokarin yin turjiya ne ga kokarin da wanda ake zargin yayi domin yi mata fyade, amma cikin rashin sa’a sai ya rinjaye ta sak**akon ya fi karfin ta, inda ya danna ta a cikin ruwa har sai da ta mutu.

Shima dandan nata ya danna shi a cikin ruwan har saida ya mutu.”

A sak**akon haka, an k**a mai laifin, inda aka meka shi ofishin yan sanda na Lamurde, biyo bayan rahoton da mijin matar mai suna Alh. Usman Abdul, ya shigar, wanda shi a halin yanzu yake cikin tashin hankali, a sak**akon rashin matar sa da kuma dan sa. ” K**ar yadda rahoton ya nuna.

A yanzude anmika ragamar binciken ga mataimakin Kwamashinan wanda shine yake kula da bangaren SCID.

Haka kuma, ya yi kira ga al’umma da su kauracewa aikata laifuka, domin jami’an tsaro baza su yi kasa a gwiwa ba wajen zakulo masu laifi domin gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin karya dokar kasa.

Matashiya Kshama Bindu Yar Kasar Indiya Na Shirin Auren Kanta Da KantaTana Shirin Gudanar Da Bikin K**ar Yadda Al'adar H...
09/06/2022

Matashiya Kshama Bindu Yar Kasar Indiya Na Shirin Auren Kanta Da Kanta

Tana Shirin Gudanar Da Bikin K**ar Yadda Al'adar Hindu A Ranar 11 Ga Watan Yuni, 2022 A Birnin Vadodara Dake Yammacin Jihar Gujarati A Ƙasar Indiya, Wanda Wannan Biki Shine Na Farko A Kasar Indiya Inda Mace Za Ta Auri Kanta Da Kanta.

Tun Karfe 12 Na Rana Atiku Zai Sha Kaye A Hannun Tinubu - Cewar Mawakin Siyasa RararaShahararren Mawakin Siyasa A Najeri...
09/06/2022

Tun Karfe 12 Na Rana Atiku Zai Sha Kaye A Hannun Tinubu - Cewar Mawakin Siyasa Rarara

Shahararren Mawakin Siyasa A Najeriya Dauda Adamu Kahutu Rarara Ya Jaddada Yakinin Cewa Tun Karfe 12 Na Rana Bola Ahmed Tinubu Zai Lashe Zaɓen 2023 Idan Mu Na Da Rai Da Lafiya.

Me Zaku Ce Akan Wannan Kalamai?.

Address

Katsina

Telephone

+17033444156

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when The Fact 24/7 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to The Fact 24/7:

Share