17/02/2024
Shin da Gaske Malaman Darika suna Yakar Akidun ‘Yan Hakika?
Akwai wasu ‘Yan Darikar Tijjaniyya, sun fito suna bayyana cewa; Inyas Allah ne. Suna halasta alfasha da munkari, da sauran Akidu na Ilimin Hakika a cikin Sufanci.
Irin wadannan Akidu abu ne da dukkan mai hankali ya san cewa; Zindikanci ne da Kafirci, b***e kuma masu Ilimi da Imani. To wannan ya sa wasu ‘Yan Darika suke raya cewa; -wai- su ma suna yakar ‘Yan Hakikar.
To amma sai dai akwai abin tambaya a nan: Miye ne abin da ‘Yan Darikar suke yaka daga ‘Yan Hakikar?
Asali dai abin da ya kamata mutane su sani shi ne: Sufanci abu biyu ne:
1- DARIKA.
2- HAKIKA.
Ma'ana; akwai DARIKA, wato hanya wacce mutum zai bi ta kai shi ya isa zuwa ga HAKIKA. Idan ya isa zuwa ga HAKIKA to sai a ce: ya yi (WUSULI), ya isa kololuwar Sufanci.
To da zaran ya isa ga HAKIKA to ya fita daga SHARI’A ya shiga HAKIKA. Kawai zai yana aiki da Shari'a ne idan yana cikin jama'a.
Ilimin HAKIKA shi suke kira Ilmin Badini, Ilimin Sirruka.
Ilimin Shari’a kuma shi ne Ilimin Zahiri.
Ilimin HAKIKA, wato Ilimin Badini shi ne; sanin cewa:
- KOMAI ALLAH NE.
- Duk abin da mutum yake aikatawa Allah ne yake aikatawa, don haka aikin mutum kowane iri aikin Allah ne.
- Duk abin da mutum ya aikata da'a ma Allah ne, Allah yana sonsa.
Don haka zina, sata, da sauran alfasha da munkari duka aiyukan Allah ne - Subhanallahi - kuma Allah yana sonsu, ya yarda da su.
To wannan ya sa wanda zai yi aiki da Ilimin HAKIKA to zai aikata dukkan alfasha. Kuma a hakan da’a yake yi wa Allah, saboda Allah ne ya ga dama ya aikata.
To wannan Ilimi na HAKIKA kowane Sufiy dan Darika ya san ilimi ne ingantacce tabbatacce, kuma dadai ne, gaskiya ne. Wadanda suke inkarinsa dayan biyu ne; imma “Mahjubi” (wanda ba ya Darika, ba a yi masa kashafin ganin Ilimin Badini ba), imma dan Darika wanda bai yi WUSULI ba.
To amma wannan Ilmi na HAKIKA, wato Ilimin Badini, Sirri ne, ba a bayyana shi. Bayyana shin kafirci ne. Shi ya sa Gazaliy yana cikin bayanin Tauhidin “Mushada”, wato ganin komai ya zama abu daya, sai ya warware wata mushkila ya ce:
"فإن قلت: كيف يتصور أن لا يشاهد إلا واحد، وهو يشاهد السماء، والأرض، وسائر الأجسام المحسوسة، وهي كثيرة؟ فكيف يكون الكثير واحدا؟
فاعلم أن هذه غاية علوم المكاشفات. وأسرار هذا العلم لا يجوز أن تسطر في كتاب، فقد قال العارفون: إفشاء سر الربوبية كفر".
إحياء علوم الدين (٤/ ٢٤٦)
“Idan ka ce: ta yaya zai yiwu a ce ba a ganin komai sai abu daya, alhali mutum yana kallon sama da kasa, da sauran abubuwa na zahiri, ana kallonsu abubuwa masu yawa? Ta yaya abubuwa masu yawa za su zama abu daya?
To ka sani lallai isa zuwa ga wannan matsayi (ganin abubuwa masu yawa sun zama abu daya) shi ne kololuwar Ilimin KASHAFI. Kuma sirrukan wannan Ilimi bai halasta a rubata su a littafi ba. Hakika Arifai sun ce: Tona sirrin Rububiyya kafirci ne”.
Don haka Ilmin HAKIKA SIRRI ne, ba a bayyana shi, saboda Ilmi ne na Badini. Duk wanda ya bayyana shi to ya yi laifi, Sufaye za su iya ce masa: kafiri, saboda ya tona sirrin da ya wajaba a boye.
Shi ya sa hatta su ma manyan Sufayen suke boyewa, Sha’araniy ya hakaito daga Junaidu:
"وكان الجنيد لا يتكلم قط في علم التوحيد إلا في قعر بيته، بعد أن يغلق أبواب داره، ويأخذ مفاتيحها تحت وركه، ويقول: "أتحبون أن يكذب الناس أولياء الله تعالى وخاصته، ويرمونهم بالزندقة والكفر؟".
الطبقات الكبرى للشعراني (١/ ١٠)
“Junaidu ya kasance ba ya magana a kan Ilimin Tauhidi (na Sufanci) sai a wuri mafi zurfi a gidansa, bayan ya rufe kofofin gidan, ya sanya makullayen a karkashin mazauninsa, sannan sai ya ce: “So kuke yi mutane su karyata Waliyyan Allah, kuma kebantattunsa, a jefe su da Zindikanci da kafirci?”.
Haka ya kawo kissar wani Arifi, ya ce:
“أبو عبد الله القرشي: أن أصحابه طلبوا منه أن يسمعهم شيئا من علم الحقائق، فقال لهم: كم أصحابي اليوم؟ فقالوا: ستمائة رجل. فقال الشيخ: اختاروا لكم منهم مائة، فاختاروا. فقال: اختاروا من المائة عشرين، فاختاروا. فقال: اختاروا من العشرين أربعة، فاختاروا. قلت: وكان هؤلاء الأربعة أصحاب كشوفات ومعارف، فقال الشيخ: لو تكلمت عليكم في علم الحقائق والأسرار لكان أول من يفتي بكفري هؤلاء الأربعة”.
الطبقات الكبرى للشعراني (١/ ١٠)
"Almajiran Abu Abdillah al-Qurashiy s**a nemi ya fada musu wani abu daga Ilimin HAKIKA, sai ya ce musu: Yau Almajiraina nawa ne?
Sai s**a ce: mutum 600 ne.
Sai ya ce: to a cikinsu ku zaba mini mutum 100. Sai s**a zabo.
Sai ya ce: ku zaba mini 20 daga 100. Sai s**a zabo su.
Sai ya ce: ku zaba mini mutum 4 daga 20. Sai s**a zabo su.
Na ce: Kuma wadannan mutum 4 suna da ILMOMIN KASHAFI da MA’ARIFA.
Sai Shehin ya ce: Da a ce zan yi magana a ILIMIN HAKIKA da SIRRUKA da farkon wadanda za su yi Fatawan na kafirta su ne wadannan mutum 4”.
Wadannan kissoshi guda biyu, mai littafin “Jawahirul Ma’aniy” ya kawo su a “Muqaddima”, a (1/ 19).
Saboda haka wannan Ilimin HAKIKAN Kafirci ne da Zindikanci a madubin Shari’a. Don Ilimi ne mai warware Shari’a ya rusa ta. Amma kuma shi ne kololuwar Sufanci. Wanda ya isa gare shi to shi ne ya zama Waliyyi, Arifi, cikakken Sufiy dan Darika, wanda ya yi WUSULI.
Saboda haka a wajen Sufaye, abin da ‘Yan Hakika suke fada asali ba laifi ba ne, dadai ne, gaskiya ne, amma sai dai Sirri ne da ba a bayyana shi. Duk wanda ya bayyana to shi ne ya yi laifi.
Don haka a Sufanci, duka abin da ‘Yan Hakika suke fada gaskiya ne, dadai ne, amma laifinsu daya shi ne BAYYANA SIRRI.
Da wannan za ka fahimci cewa; masu inkari ga 'Yan Hakika cikin Sufaye, ba Akidun 'Yan Hakikar suke inkari ba, a'a, bayyanawa suke inkari.
Dr. Aliyu Muh'd Sani