17/10/2024
Kungiyoyin Matasan Najeriya Ta Gudanar Da Zàñga-zàñĝar Neman A Gudanar Da Bincike Kan Sanata Shehu Buba Bisa Zargin Taimakawa Ta'addanci
DAGA Ƙungiyar Muryar PDP Ta Najeriya
A yayin wani gangamin nuna goyon baya da s**a gudanar, ƙungiyar gamayyar ƙungiyoyin matasa ta Najeriya, "National Coalition of Youths", ƙarƙashin jagorancin Bashir Gusau, ta gudanar da zanga-zangar lumana a birnin tarayya Abuja, inda ta yi kira kan a gudanar da bincike game da zargin hannu a ayyukan ƴan bindiga da ake yi kan Sanata Shehu Umar Buba, sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu.
A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, Zàñga-zàñĝar wacce ta haɗa ɗaruruwan ƴan Najeriya, sun kuma yi zantawa da manema labarai inda s**a nemi a tabbatar da gaskiya da adalci.
Ƙungiyar ta maida hankali kacokan kan wannan zargi wanda ya faro a farkon wannan watan, inda ake tuhumar Sanata Buba da hannu cikin ayyukan ƴan biɲdiĝá. Duk da cewar babu wata tuhuma yanzu haka a hukumance, duba da girman lamarin akwai buƙatar hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike na gaggawa musamman ma la'akari da yadda ƙasar ta ke cigaba da fuskar ƙalubalen tsaro can da can.
Kiran Gusau Kan A Tabbatar Da Adalci:
A yayin zantawarsu da manema labarai, shugaban ƙungiyar, Bashir Gusau ya nuna buƙatar gudanar da bincike na haƙiƙa. A cewarsa, babu wani mutum wanda ya fi ƙarfin a gudanar da bincike a kansa a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso komai matsayinsa musamman ma kan lamarin da ya shafi tsaron ƙasa.
"Tsaro da zaman lafiyar al'ummarmu shi ne abin da ya zama wajibi kowane shugaba ya fi ba wa fifiko a ƙasar nan. Ba abu ne da za a yarda da shi ba a zaɓi mutum domin ya kare muradun al'ummar Bauchi ta Kudu ya kuma yi tarayya da ƴan bindiga ko wasu masu aikata miyagun laifuffuka ba. Hakan ya sa mu ke kira da a gudanar da bincike kan wannan zargi da ake yi wa Sanata Buba". Cewar Gusau.
Ya ƙara da cewa wannan Zàñga-zàñĝa tasu ba ta da alaƙa da siyasa face neman a tabbatar da adalci, zaman lafiya da tsaro a Jihar Bauchi da kewayenta. Ya ƙara da cewa matsalar tsaro ta ratsa kusan ko'ina a ƙasar nan ta jefa al'umma cikin firgici da razani duba da wannan dan mutum yana riƙe da wani matsayi bai kamata ya samu garkuwa daga neman tabbatar da adalci ba.
Neman A Ɗauki Mataki Na Gaggawa:
Ƙungiyar ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, majalissar ƙasa, da kuma hukumomin tsaro na ƙasa da su ɗauki ƙwaƙƙwaran matakin da ya dace. A cewar Gusau, barin wannan zargi batare da an yi bincike ba babu abin da zai haifar face jefa rashin yarda kan hukumomin Najeriya a zukatan jama'a gami da sanyaya gwiwar al'umma kan yaƙi da ta'addanci.
"Mun yi imani cewa idan aka gudanar da bincike har aka gano Sanata Buba ba shi da laifi, to adalci yana nan. Amma idan har akwai gaskiya a zargin ya zama wajibi doka ta yi aikinta a kansa batare da duban matsayinsa ba. Al'ummar Bauchi ta Kudu da dukkan ƴan Najeriya sun cancanta su san gaskiya kan wannan batu". Cewar Gusau.
Martanin Masu Ruwa Da Tsaki:
Tuni zanga-zangar ta fara samun martani daga masu ruwa da tsaki daban-daban. Wasu daga cikin al'ummar Bauchi ta Kudu sun yabawa matasan bisa tsayuwarsu kan ƙalubalantar ba daidai ba, yayin da wasu kuma suke kallon lamarin ta fuskar siyasa.
Duk da waɗannan ra'ayoyi daban-daban, ƙungiyar ta jaddada ƙudirinta na cigaba da bibiyar lamarin cikin lumana tare da jan hankalin sauran ƴan Najeriya da su shigo cikin wannan gwagwarmaya ta neman tabbatar da adalci.
Bayani Na Gaba
Daga ƙarshe ƙungiyar ta yi fatan saƙon nata zai isa ga gwamnati da hukumomin tsaro. Manufar ƙungiyar shi ne a tabbatar da gaskiya da adalci musamman kan lamarin da yake da alaƙa da tsaro da zaman lafiyar ƙasa.
Zàñga-zàñgar lumanar wacce Bashir Gusau da ƴan tawagarsa s**a jagoranta sun ja hankalin ƙasa kan zargin da ake yi wa Sanata Shehu Buba tare da fatan ƴan ƙasa, masu nazarin siyasa da hukumomin tsaro za su sanya Ido kan lamarin.
Yanzu haka, lamarin ya je gaban hukumomin tsaro daban-daban, al'umma kuma na cigaba da zaman dakon a gudanar da cikakken bincike na haƙiƙa duba da yanayin siyasa a yankin Bauchi ta Kudu.
Kamar yadda Najeriya ta ke cigaba da yaƙi da matsalar rashin tsaro, zanga-zanga irin wannan ta na nuna irin rawar da ya kamata ƴan ƙasa su taka wajen tabbatar da adalci a ƙasa. Ƙungiyar gamayyar matasan ta Najeriya ta tura saƙo mai ƙarfi kan lallai ya zama wajibi a gudanar da komai cikin gaskiya da adalci da daidaito kan yaƙi da ƴan bindiga batare da duba sanayya, girman matsayi ko sassautawa ba.