
01/09/2025
Tabkin Ramin-masu Ya Cinye Gidajen Da Ke Kewaye Da Shi, Al'umma Sun yi Kira Ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Dr. Dikko Umaru Radda Ya Kawo Masu Dauki Tare shugaban Karamar Hukumar Katsina Isah Miqdad AD Saude.
Da Su Ke Bayyana Damuwarsu Ga Gwamnati Al'umma Unguwar Gafai, Lungun makerar Farfaru Sun Bayyana Halin Da Su ke ciki ne Jiya Lahadi Gaban Tsohon Tabkin Na Ramin Masu Dake Kewaye Da Unguwannin Nasu Ya Na Cinye Masu Gidaje, Al'ummar Unguwar Sun Ce Suna Fatan Mai Girma Gwamnan jihar Zai Hada Wannan Aikin Da Aikin Titin Da Za a Gabatar Daga CPS Zuwa Kofar Yandaka.
Sun Bayyana Cewa Idan Aka Gabatar Da Rusan Aikin Gida 2 Ne Kacal Zai Rage Tsakanin Titin Da Wannan Tabkin Mai Cinye Masu Gidaje, Daga Karshen Al'umma Sun Ce Sun Sadaukar Da Filin Tabkin Idan Aka Cike Ga Gwamnati Ta Yi Makaranta Ko Asibiti Domin Amfanin Jama'a. Sun yi Addu'a Ga Fatan Alkhairi Ga Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda Da Kuma Shugaban karamar hukumar Katsina Malam Isa Miqdad AD Saude.
Rahoton
Jaridar YTD Hausa