
07/05/2023
Duk da Goyon bayan da zaɓaɓɓen shugaban kasa Tinubu ke nuna wa Akan Akpabio ba zai hana ni neman shugabancin majalisa ba' inji Abdul'aziz yari.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanatan da aka zaɓa Abdul’Aziz Yari, ya jaddada buƙatarsa ta neman shugabancin majalisar ƙasar.
Daily Trust ta ruwaito cewa sauran waɗanda suke neman wannan matsayi, akwai Gwamna Ebonyi Dave Umahi da Sanata Ali Ndume waɗanda s**a janye daga takarar domin marawa wanda jam'iyya ta zaɓa tsohon gwamnan Akwa-Ibom Godswill-Akpabio.
Amma yari ya ce nuna goyon bayan da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi kan Godswill, ba zai hana shi takarar ba.
Ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a tafiyar Tinubu da Shettima wanda shugabanta na ƙasa Khailani Muhammad ya jagoranta a Abuja ranar Asabar.