26/01/2026
Tabbas mun yi babban rashi na dattijo, malami, masanin fiqhu, kuma jajirtacce, mai amana - Inji Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah na Kasa Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya shigo garin Katsina a ranar Asabar domin kara yi ma shuwagabanni da iyalai ta'aziyyar rasuwar Sheikh Habibu Yahayya Kaura wanda Allah yayi ma rasuwa a daren ranar Laraba din da ta gabata aka kuma yi jana'izar shi a ranar Laraba a hedkwatar Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa da ke Abuja
Wanda tun bayan rasuwar ya turo Shugaban Majalisar Malamai na Kasa Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo da Sakataren Kungiyar na Kasa Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe domin zuwa su samu Shugaban Kwamitin Amintattun Kungiyar, Daraktan Da'awah na Kasa kuma Shugaban Kungiyar na Jihar Katsina Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina Sautus-Sunnah domin jajantawa juna da yin ta'aziyya ma juna bisa wannan babban rashi
Haka shi ma bayan ansar baki da ke zuwa yin ta'aziyya a hedkwatar Kungiyar a Abuja ya baro Abuja ya shigo Katsina tare da tawagar shi a ranar Asabar domin haduwa da Shugaban Majalisar Malamai da Sakatare
Yayin da tawagar Shugaban, ta isa gidan Sheikh Habibu Yahayya Kaura da yake jawabi Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa "babu shakka mun yi babban rashi na dattijo, malami, masanin fiqhu, kuma jajirtacce, mai amana
Sheikh Habibu Yahayya Kaura Allah ya gafarta ma shi, Allah yasa ya huta, Allah ya jikanshi da rahama. Babu shakka ba iyalansa ne kadai su kai wannan rashi ba, mu a wannan kungiya ta Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah mun yi babban rashi
Duk wanda zai ambaci Sheikh Habibu Yahayya Kaura zai ambace shi da amana da ayyuka na alkhairi, duk wanda ya san shi ya san mutun ne da ke in zai gaya maka magana ba boye boye babu mujamala, abinda ke cikin ransa, abinda ya gani zai nuna maka domin gyara
Duk lokacin da ya turo sako zai zamanto sako ne na fadakarwa, shawara kuma ba mu da wani malami da yake tsayawa yana kallon Manara TV ya ga ko wane malami aka saka wane irin gyara ya kamata, wace irin shawara za'a ba shi
Duk lokacin da wani abu ya taso a kungiya ta ke neman wata shawara ko abinda zai haifar da rigingimu a cikin al-umma, yana daya daga cikin wadan da za su bada shawarar meye ya kamata ayi
Aikin sa na karshe shi ne sulhu da muka tura shi yayi a garin Funtua akan wani abu da ke faruwa, bayan mun tattauna da Shugaban Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa mun yanke tura kwamiti domin zuwa a tattauna kuma samar da mafita akan abinda ya faru. Sheikh Habibu Yahayya Kaura jagoranci kwamitin sun je an zauna an tattauna har an rubuta rahoto, amman bai iya mika mana rohoton ba, saboda yana sauka ya gamu da wannan ciwo wanda kuma yana ji ya kira waya tace yaji wani abu a jikinshi da baya tsammanin zan iya rayuwa
Nayi ma shi addu'ar Allah ya ba shi lafiya. Bayan an kwana daya ya turo sakon murya yace ina bar maku wasiya ina fatan wasiya ta ce itace ku tsaya kan littafin Allah da sunnar Annabi (S.W.A) duk yadda za'ayi shugaba kada ku canza daga wannan manhaji itace hanyar da zata kai mu ga tsira. Wannan shi ne maganar shi ta karshe tsakanin mu, bayan kwana biyu jiki yayi zafi. Wanda daga nan aka cigaba da jinya har zuwa lokacin da Allah yayi ma shi rasuwa"
Daga nan Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah) a madadin iyalan Sheikh Habibu Yahayya Kaura da Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina , yayi godiya ga Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau bisa kulawa da dawainiyar da su kai tun farkon fara wannan jinya har zuwa yanzu da muke ma juna ta'aziyya
Bayan nan Sheikh Sautus-Sunnah ya jagoranci Shugaba Sheikh Abdullahi Bala Lau da tawagarsa domin shiga cikin gida wajen iyalai da yan'uwan Marigayi Sheikh Habibu Yahayya Kaura domin yi ma juna ta'aziyya a madadin wannan Kungiya ta Kasa baki daya
Haka kuma bayan fitowa daga cikin gidan Shugaban Kungiya na Kasa Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya gabatar da sakon godiya a madadin Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta tarayyar Najeriya baki daya kamar haka
"A madadin wannan Kungiya ta mu ta Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa baki daya a madadin shugabanni, madadin kuma iyalai na marigayi Sheikh Habibu Yahayya Kaura wanda nan muna gidansa bayan mun shiga zuwa ga iyalinsa, bayan kuma mun yi ta'aziyya ga sauran yan'uwa bayan mun mika ta'aziyyar mu ga kowa da kowa daga cikin al-ummar mu na wannan kasa harma da makwabtan mu
Bayan godiyar ga Allah (S.W.A) muna isar da godiya ta musamman ga Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da ya aiko da tawaga ta musamman domin zuwa ayi mana ta'aziyya, a tausaya mana saboda wannan gibi da rashi babba da wannan Kungiya tayi
Mai Girma Shugaban kasa muna godiya, tawagar da ka turo sun zo, Allah ya saka da alkhairi, ya bar zumunci. Haka ya kamata duk lokacin da aka shiga damuwa a nuna mana tausayi domin nuna ana jagorantar mu, kuma ana mana yadda ya kamata don bada hakkin da mu ke da shi a jagorancin
Bayan haka muna godiya ga mai girma gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Radda. Gwamnan Jihar Katsina ya cancanci ayi ma shi godiya ta musamman Allah ya saka ma shi da alkhairi. Tun farkon lokacin da Sheikh Habibu Yahayya Kaura yayi kwanciyar rashin lafiya, yayi iya kokari na ganin duk abinda za'ayi na jinya a nan Katsina ya dauki dawainiya
Lokacin da Kungiya tace a maido shi Abuja nan ma yace a Abuja din zai bada gudummuwar da za'a kai shi asibitin Nizamiye, mu kuma mun ce a kawo shi asibitin kasa (National Hospital) amman duk da haka yace tunda mun ce akai can ya hakura a je can. Saboda haka an je asibitin kasa amman daga karshe an koma Nizamiye wanda ya koma ya cigaba da daukar dawainiya nauyin dukkan abinda aka kashe har zuwa lokacin karshen rayuwarsa
Mai girma gwamna muna godiya Allah ya saka da alkhairi, gudummuwar da aka bayar da kuma kokarin da ake niyyar cigaba da kara tallafama gidan, da sanya yaran kan hanya, da ma ba su abinda za su yi na sana'a ko shigar da su ayyuka da aka ce za'ayi daga gareka da kuma sauran abokanan ka. Muna godiya
Haka kuma muna godiya ga Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, Hon. Abdulmalik Zannan Bungudu bisa irin gudummuwar da su ka bada wurin samar da kokari a dawo da abinda ake iya yi da hali a lokacin da Sheikh yake da rai da kuma irin gudummuwar da su ka bada domin tallafama gidan, Allah ya saka masu da alkhairi da sauran daidai kun da su ka bada gudummuwa ta dukiya don tallafawa wurin jinya, sannan bayan baya raye su ka bada gudummuwa da tallafi don tausayawa gidan. Muna addu'a duk wanda ya bada gudummuwa Allah ya saka ma shi da alkhairi
Alh. Ibrahim Masari mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa yazo asibiti ya duba duk abinda ya kamata ayi ana yi har ma ya bada tabbacin cewa idan da halin a dauke shi zuwa kasar waje duk za su dauki dawainiya sai dai yana yin jikin ba zai bari ba ayi haka kuma daga lokacin da ake jinya har zuwa bayan rasuwar har zuwa wannan lokaci duk irin gudummuwar da ya kamata ya bayar, yayi iya kokarin shi, shi da sauran abokanan shi irinsu gwamnan Yobe Mai Mala Buni da sauran wadan da ya kamata ace sun bada tallafi da gudummuwa. Muna godiya Allah ya saka da alkhairi
Tsohon gwamnan Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari shi ma da shi akai duk abinda ya kamata ayi. Allah madaukakin sarki ya saka da alkhairi
Akwai kuma wadanda su ma sun bada gudummuwa wadan da ba zamu iya tunawa ba kowa da irin abinda ya bayar na gudummuwa da wadan da su kai addu'o'i da wadan da kuma su ka zo su kai mana ta'aziyya daga Janhuriyar Niger da sauran kasashe makwabta da nan cikin gida Najeriya da Shuwagabannin wannan Kungiya na Jihohi kowa yayi iya abinda ya kamata
Ba za mu gushe ba shugaban wannan Kungiya ta Jihar Katsina Sheikh Dr Yakubu Musa Hassan Katsina Sautus-Sunnah kuma Daraktan Da'awah wajen tsayawa da jajircewa da yayi wajen ganin duk abinda ya kamata ayi wa Sheikh Habibu Yahayya Kaura yana raye an yi da kuma abinda ya kamata ayi na kulawa da gidan muna mashi addu'ar Allah ya saka mashi da alkhairi, Allah ya bada ikon kulawa, Allah ya sanya albarka
Daga karshe ina kira ga 'ya'yan sa da sauran makwabta da al-umma baki daya a cigaba da addu'a Allah ya gafarta ma Sheikh Habibu Yahayya Kaura. Sannan duk inda ya ke da zumuncin da yake sadarwa a cigaba da sadar da shi
Kuma wannan kungiya ba zata manta da shi ba kuma kaman yadda ta ke kulawa da sauran gidajen na marigaya hakan za mu cigaba da kulawa mu GA abinda ke gudana cikin wannan gidaje
Ina addu'a Allah maɗaukakin sarki ya gafarta ma Sheikh Habibu Yahayya Kaura, Allah kada ya jarabci bayansa, Allah ya kyautata karshen mu baki daya, Allah ya kara sanya mana albarka, Jihar Katsina da sauran jahohin mu Allah ya kara tabbatar mana da zaman lafiya"
Daga karshe Shugaban ya jagoranci tawagar domin zuwa dubiyar jinya ga Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Kasa Sheikh Barr. Ibrahim Sabi'u Jibia ya ke yi a gida sanadiyyar kara da ya samu a kafarsa
Shugaban ya duba jikin na shi tare da yi mashi addu'ar kara samun lafiya