03/05/2024
Waye dan jarida? Menene aikin dan jarida?
Wanda ya rubuta ✍️
Comr Abba Sani Pantami
Waye dan jarida?
Dan jarida shine mai nemo labarai yana yadawa a gidajen jaridu, gidajen Talabijin, gidajen Rediyo da kuma kafofin sada zumunta.
Akwai dan jarida mai zaman kansa akwai masu yiwa gidajen jaridu da kuma kafar yada labarai, ta Rediyo ko Talabijin aiki.
Menene aikin dan jarida?
Aikin jarida ya kasu kashi-kashi, gasu kamar haka;
1, Akwai mai rubutu da nazarin labarai.
2, Akwai wanda ke gabatar da labarai a gidajen Rediyo da Talabijin da kuma gidajen jaridun kafofin sada zumunta.
3, Akwai mai dauko rahoto daga nesa, daga gidajen Rediyo ko Talabijin ko daga gidajen jaridun kafofin sada zumunta ko daga wani gari mai nisa koma daga wata kasar.
4, Akwai wanda shi aikinsa duba kuskuren rubutu da duba gyare-gyaren yadda labari yake.
5, Akwai wanda ke gabatar da labarai da hira da mutane a jaridun kafofin sada zumunta da gidajen Rediyo da Talabijin da sauran shafukan sada zumunta.
6, Akwai dan jarida mai daukar hoto da bidiyo.
7, Akwai mai dauko rahoto daga lungu da sako na dukkannin abubuwan da ke faruwa a cikin gida.
8, Akwai dan jarida wanda yake bincike kuma ya rubuta rahoto.
9, Akwai dan jarida mai sharhi a kafofin sada zumunta ko rubuta sharhi a gidajen jaridu da kafofin sada zumunta.
10, Akwai kwararran dan soshiyal midiya da yake rikidewa ya koma dan jarida a kafofin sada zumunta ba tare da ya karanci aikin jarida ba.
Jan hankali....
Dolene masu rubuta labarai da sharhi su zama masu fadin gaskiya, fadin gaskiya yana da matukar muhimmancin gaske ga aikin jarida.
Idan Dan jarida ya zama baya fadin gaskiya a labaransa ko kuma rahotanninsa to yakan fuskanci hukunci na dakatarwa ko ma kora baki daya.
'Yan jaridu masu dauko rahoto na fuskantar matsaloli da dama wajen dauko rahoto, sau da yawa 'yan jarida kan samu kawunansu a hadura, musamman ma wajen da ake samun rikicin ta'addanci ko fagen yaki.
Kasashe da dama suna ta daure 'yan jaridu har ma da kasar mu ta Najeriya.
Kai a matsayinka na dan soshiyal midiya, marubuci kuma dan jarida a wane sashi kake?