Voice of naija

Voice of naija 📢 Voice of Naija — Muryar Jama’ar Najeriya! Muna kawo muku labarai na gaskiya, nishadi mai fa’ida, da ilimi mai gina al’umma.

Ku kasance tare da mu domin jin muryar gaskiya daga kowane yanki na Naija 🇳🇬

24/11/2025

KULLUM DA SABON LABARI MARA DADI A NIGERIA ALLAH MUNTUBA😭🙏

Rahotanni daga Jihar Borno sun tabbatar da cewa may@kqn !SWAP sun sace akalla ’yan mata 13 a yankin ƙaramar hukumar Askira Uba, yayin da suke kan hanyarsu zuwa gona.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Abdullahi Askira, ya tabbatar da lamarin, inda ya bayyana cewa an sace su ne a gundumar M***a a ranar Lahadi. Hikima Radio & TV.

Labari Da Dumin SaMa’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Katsina ta umarci rufe dukkan makarantun gwamnati da ...
21/11/2025

Labari Da Dumin Sa

Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Katsina ta umarci rufe dukkan makarantun gwamnati da ke faɗin jihar saboda dalilai na tsaro.

Ma’aikatar ta ja hankalin iyaye, malamai da al’umma gaba ɗaya da su bi wannan umarnin nan take, yayin da ake ci gaba da bibiyar yanayin tsaron jihar baki ɗaya don tabbatar da kare rayuwar ɗalibai da ma’aikata.

DADUMI-DUMI: Soja Yarima yasha dakyar a kokarin hallakashi yanzu cikin daren nan a Abuja, kamar yadda jaridar VANGUARD t...
16/11/2025

DADUMI-DUMI: Soja Yarima yasha dakyar a kokarin hallakashi yanzu cikin daren nan a Abuja, kamar yadda jaridar VANGUARD ta ruwaito.

Rahoton ya nuna cewa Sojan ya lura da wasu mutane da s**a rufe fuskarsu a cikin motoci biyu kirar Hilux dai-dai gidan mai din NIPCO dake Abuja s**a biyoshi, inda ya samu yasha dakyar.

Jami’ar Jihar Abia Ta Cire Tambaya Da Ta Shafi Rikicin Ministan FCT Abuja Da Soja AM Yerima Jami’ar Jihar Abia (Abia Sta...
15/11/2025

Jami’ar Jihar Abia Ta Cire Tambaya Da Ta Shafi Rikicin Ministan FCT Abuja Da Soja AM Yerima

Jami’ar Jihar Abia (Abia State University (ABSU), sashen Political Science, ta cire wata tambaya daga jarrabawar dalibai bayan ta jawo ce-ce-ku-ce saboda tana da alaƙa da rikicin da ake dangantawa da Ministan Babban Birnin Tarayya da jami’an tsaro.

Tambayar da aka zagaye a rubutun jarrabawar ta ce, “How would you ascertain the cause of conflict between the Minister of the F.C.T. and the military?”

Daga Muhammad Kwairi Waziri

YANZU-YANZU: Chaina ta Dauki Alkawarin bawa Najeriya goyon baya akan sha'anin tsaro.Jakadan ƙasar China a Najeriya ya ga...
06/11/2025

YANZU-YANZU: Chaina ta Dauki Alkawarin bawa Najeriya goyon baya akan sha'anin tsaro.

Jakadan ƙasar China a Najeriya ya gana da Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, a yau bayan wani muhimmin taron dabarun tsaro.

A yayin ganawar, jakadan ya bayyana cewa ƙasarsu za ta ci gaba da ba da tallafi ga Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin gida.

Haka kuma, ya bayyana adawar ƙasar China ga duk wata ƙasa da ke tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu ƙasashe da sunan addini ko kare ‘yancin ɗan adam, tare da nuna rashin amincewa da barazanar sanya takunkumi ba tare da hujja ba.

- ATP Hausa

TIRKASHI: Wata budurwa a jihar Benue ta kera kayan yaki, don shirin tunkarar yaki da Donald Trump.
05/11/2025

TIRKASHI: Wata budurwa a jihar Benue ta kera kayan yaki, don shirin tunkarar yaki da Donald Trump.

DA DUMI-DUMI: Sojojin Nigeria sun gudanar da wani atisaye inda s**ayi gwajin wasu makamaiAmma abun takaici da baƙinciki ...
04/11/2025

DA DUMI-DUMI: Sojojin Nigeria sun gudanar da wani atisaye inda s**ayi gwajin wasu makamai

Amma abun takaici da baƙinciki shine:

Wannan makamin sunansa (73mm SPG-9 recoilless rifle)

Wannan wani tsohon makami ne da ƙasar Russia 🇷🇺 ta ƙera a shekarar 1962

Shekaru 64 kenan da aka ƙera wannan makamin

Muna amfani da tsofaffin makamai, yan ta'adda na amfani da sababbin makamai na zamani, taya za'a shawo kan matsalar tsaro a Nigeria 🇳🇬?
-------------------------

Sojoji na amfani da hotson makami, yan majalissu na siyen sabbin motoci (Toyota Lexus 2026) 🥲

Wannan wace irin ƙasa ce?

Daga Alhassan Mai Lafia

Da alamu dai Donald Trump yaki ke son yi da Nigeria, amma dai kamar yadda ya fada idan har ‘yan ta’addan da s**a addabi ...
02/11/2025

Da alamu dai Donald Trump yaki ke son yi da Nigeria, amma dai kamar yadda ya fada idan har ‘yan ta’addan da s**a addabi kowa da Musulman da Kiristan su za su shigo su yaka su kawar mana da su, ai kowa ma zai goyi bayan hakan.

A cikin wani sabon ƙunshin sunaye da Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Sanda na c...
29/10/2025

A cikin wani sabon ƙunshin sunaye da Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Sanda na cikin mutane 86 da shugaban ya rage wa hukuncinsu.

Bayanin ya nuna cewa an rage mata hukuncin ne laʼakari da makomar ƴaʼyanta da kuma halaye masu kyau da ta nuna yayin da take tsare a gidan gyaran hali.

Wani aiki Sai A Afrika: Jerin shugabannin Nigeria da Shugaban kasa Paul Biya na Jamhuriyar Cameroun yayi shugabanci da s...
29/10/2025

Wani aiki Sai A Afrika: Jerin shugabannin Nigeria da Shugaban kasa Paul Biya na Jamhuriyar Cameroun yayi shugabanci da su har Zuwa yanzu,

Mezakuce?

Sabbin Shugabannin Tsaro Sun Gana Da Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu
28/10/2025

Sabbin Shugabannin Tsaro Sun Gana Da Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu

21/10/2025

Labari Yanzu-Yanzu: Tankar Mai ta faɗi a Najeriya

Rahotanni daga [Jahar Naija] sun tabbatar da cewa wata tankar mai ta faɗi a yau.

Shaidu sun bayyana cewa lamarin ya jawo cunkoso da fargaba a yankin, yayin da jami’an tsaro da ma’aikatan kashe gobara s**a isa wajen domin kaucewa hatsari.

Har yanzu ba a tabbatar da adadin rayukan ba, amma an yi kira ga direbobi da jama’a su guji taruwa kusa da wurin don kaucewa haɗari ko fashewa.

📍 Voice of Naija – Muryar Jama’ar Najeriya
Ku ci gaba da bibiyar mu don karin bayani kai tsaye daga Naija. 🇳🇬

Address

Masanawa
Katsina

Telephone

+2349024825403

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Voice of naija posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Voice of naija:

Share