13/05/2025
MATAR KA tana so da kuma buqatar abubuwa guda 20 daga gareka ME GIDA...........
Musamman idan ta kasance ta Gari ce ita.
❤1) Tana son ka dinga Hira da ita, da janta a jiki da Raha da wasa ko wasanni.✍
❤2) Tana son idan ta yi fushi ko wata damuwa ka rarrashe ta kuma ka ji "Ba'asin fishin✍
❤3) Tana son ka dinga dan shigo mata da abin kwadayi daidai qarfin ka.✍
❤4) Tana son idan ta kyautata maka ka gode mata kuma ka yabe ta, in so samu ka mata Addu'a.✍
❤5) Tana son ka dinga girmama kishin ta, ma'ana duk abin da zai motsa kishin ta ka kiyaye gwargwado ✍
❤6) Tana buqatar ka dinga mata uziri a wasu lokutan da kuma Haquri da ita✍
❤7) Tana son ka dinga son ýan uwanta da nuna kulawa garesu.✍
❤8) Tana son ka dinga nuna mata soyayya da kalaman soyayya da kulawa da bata kariya, da tsare mutuncinta fiye da yanda ka mata a waje.✍
❤9) Tana son ka dinga fita da ita tana dan ganin Gari saboda mata da yawa zaman wuri ďaya su dade yana jefa su a damuwa, kuma ka barta ta dinga shaqatawa kar ka cika matsatsi gareta don kar zama da kai da gidan ka ya gundire ta, ko wani Buri gareta a Rayuwa ko wani abu da take aiwatarwa idan ba barna sai ka shige mata gaba duk ta yi su tare da bata goyon baya, wannan duk yana zabgewa mace Damuwa da qunci madamar ba barna a ciki✍
❤10) Ka dinga kula da Haqqinta iya yinka na Ciyarwa, tufafi, magani, kayan Ado da tsafta, da dan kudin kashewa saboda tsaro.
❤11) Tana son ka dinga nuna mata kana tausayin ta sosai da damuwa da damuwar ta, da nuna mata bata maka tsufa✍
❤12) Idan ta bata maka rai kar ka mata tsawa ko ka ci zarafinta ko aibantata b***e a kai ga zagi, ka mata Nasiha, ka mata gyara cikin mutunci, domin kalma Dafi ce ga zuciya.✍
❤13) Matarka Tana so ka damu da buqatar ta ta shinfida ka yi duk me yiyuwa wurin ganin tana gamsuwa, kuma ka yawaita bibiya da tuntuba✍
❤14) Idan ta yi tafiya ka bibiyi yaya Hanya, yaya ta sauqa? Yaushe za ta dawo? Ka yi missing da sauran su, idan kwana ta yi ka kira a waya ku gaisa da sauran kulawa idan da yara duk ka tambaya ko ku yi waya da su suma, haka ko dawowa ta yi ka yi qoqari ka ji yaya Hanya da sauran su?? In son samu ne ma akwai dama duk inda za su je ka kaisu da kanka.✍
❤15) Idan ta haihu da kai ka nuna mata kana matuqar Qaunar ta da abin da ta haifa, kar ka guje su ko ka qyamace su, kuma ka kyautata iya kyautatawa garesu da kula da su.✍
❤16) Ka taya ta sadar da zumuncinta, ka kuma qarfafe ta kansa gwargwado ✍
❤17) Ka zama kana Adalci a zahiri, da boye na zuciya sosai idan matan ka sun kasance sama da 1, haka tsakanin ýaýa ma.✍
❤18) Ka dinga taimaka mata da Aikin Gida idan kana Gida ko da kuwa da riqe mata Yaro ne, ayyukan da s**a shafi Qarfi ka daure kai ka dinga yi.✍
❤19) Idan tana cikin Jinya ta rashin Lafiya, ko wata jarrabawa ka yi qoqari ka nuna mata ka fi kowa damuwa da Halin da take ciki a aikace.✍
❤20) Ka kula da Addinin ta da Tarbiyyar ta Haqqi ne wannan a kanka, kuma ka dinga yiwa zaman ku Addu'a sosai da zuri'ar ku.✍
Allah ya bayar da zaman lafiya. Ameeen.
Zoohrah Oummu Deederht