24/02/2024
Saliha Episode 01
(A true story about my life)
Akwai ababen da ke sa mutum farin ciki akwai masu bata ran mutum, wasu sukan ba mutum tsoro wasu zasu maisheka jarumi, wasu kau su mai da kai sakarai marar amfani ga al'ummar yankin ku.
Abinda yafi ja min hankali shine minene zanyi na zama jaruma, watau ina nufin in zama mai amfani ga al'umma ta, yan kina kuma?
Rayuwa kenan, sunana Saliha Sa'id Sambo ana kirana da S3.
Yarinya ce ni wacce na ta so mai taurin kai, mai son iyawa, gashi na sami gata a wurin iyaye na fiye da sauran Yaran gidan mu, duk haka ya kasance domin ni Diya ce mai kyau sosai, ina da gashi, gani fara, kin kowa wanda ya rasa, a gaskiya koni na hallaci kaina haka zanyi kaina.
Rayuwata!!!
Bani da abokan fada sai maza, kusan duk wanda na tunkara sukan sha dibga a wurina, wannan dalilin yasa na raina maza, nake ganinsu su ba komai bane fyace abin reni a gareni.
Nayi primary, sai Allah yasa inada ko k'ari, wannan ya kara sa min nayi takama acikin mutane. Ga kyau, ga elimi, ga gata, ga rufin asiri a gidanmu daidai bakin gwalgwado.
Duk abinda na nema iyayena basu taba hanani ba, uwa uba su ga raina ya bace, hankalinsu idan yayi dubu sai ya tashi. Gatan da aka bani zan iya cewa yafi na kowa a duniya, har wasu suna kirana da 'YAR GATA.
Hmnn rayuwa kenan kowa akwai kalubalen da yake fuskanta, wasu laifinsu ne wasu kuma jama su akayi.
Banason naji wani yace yana sona, domin gani nake ka rena ni idan kace kana sona, na ci zarafin samari sosai.
Wata rana da na girma, inada kimanin shekara 17, sai mahaifina ya fito min da maganar aure. Jin wannan kalmar ce tashin hankalin da na shiga mafi muni a rayuwata.
Ka biyo ni zuwa Episode 02 don jin yanda ya kasance dani.
Muhadu a wannan dadandalin a sati mai zuwa.
Sunana
SALIHA SA'ID SAMBO S3
Credit: HHFM