04/09/2026
Gwamna Radda Ya Halarci Ɗaurin Auren Ɗan Sanata Shekarau
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya halarci ɗaurin auren ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Khalid Ibrahim Shekarau, da amaryar sa, Elham Yakubu Adam Kofar Mata.
An gudanar da ɗaurin auren ne a Masallacin Juma’a na Sheikh Ahmed Tijjani da ke Ƙofar Mata, a cikin birnin Kano.
Gwamna Radda ya taya ma’auratan murna tare da yi musu addu’ar fatan zaman lafiya, soyayya da albarka a auren su.
Ɗaurin auren ya samu halartar Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, Tsofaffin Gwamnonin jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, da Sanata Kabiru Gaya, da dai sauran su.