
01/09/2025
Da Yardar Allah Zaman Lafiya Ya Dawo A Karamar Hukumar Musawa - Inji Matawallen Musawa
Matawallen Musawa kuma Darakta Janar na Madabba'ar Jihar Katsina Malam Honorabul Rufa'i Musawa ya bayyana cewa da izinin Allah daga yanzu zaman lafiya ya samu wanzuwa a Karamar Hukumar Musawa.
Honorabul Abba Rufa'i Musawa ya bayyana hakan ne a sa'ilinda yake zantawa da Manema Labarai ciki har da Accuracy News Hausa, jim kadan bayan kammala zaman sulhu da yan bindigar a Karamar Hukumar Musawa.
Matawallen na Musawa ya bayyana cewa, da wannan zaman sulhu da aka yi da yan bindigar dajin, akwai kyakkyawan yakinin cewa yankin zai dawo da kumarin shi na cigaban tattalin arziki da zaman lafiya a tsakanin al'umma da Fulanin yankin.
Darakta Janar din ya bayyana Jin dadi akan yadda ya ga fuskokin yan bindigar da al'ummar yankin cike da Farin ciki da walwala bisa ga tabbatar da zaman sulhun, wanda a cewar shi Insha Allah zai zamo abinda zai kawo karshen zubar da jini a yankin.
Daga nan sai ya yabawa Shugabancin Karamar Hukumar akan kyakkyawan tsari da aka yi na yarjejeniyar zaman lafiyar, tare da jaddada yakinin cewa hakan zai dore har abada.
Haka zalika, ya yi roko ga jama'ar yankin akan kada su gajiya wurin cigaba da yin addu'oin dorewar wannan sulhu, domin kara samun cigaban tattalin arziki da zamantakewa da juna kamar yadda addini ya tsara.
Matawallen na Musawa ya yi amfani da damar inda ya yabawa Gwamna Dikko Radda akan jajircewar shi na ganin an samu ingantaccen tsaro a Jihar Katsina, sai ya roki jama'ar yankin akan su Taya shi da addu'a, domin cimma nasarar wannan kudiri nashi.