
30/07/2025
Ma'aikatar lafiya ta jiha, ta shirya bada horon na kwana 2 kan kula da lafiyar Idanu a matakin farko (PRIMARY EYE CARE) a Katsina ta tsakiya
Gwamnatin jihar Katsina, a ɓangaren Ma'aikatar lafiya ta jiha, ta shirya bada horon na kwana 2 kan kula da lafiyar Idanu a matakin farko (PRIMARY EYE CARE) a Katsina ta tsakiya, bayan sun kammala kwana 2 kan bada horo a Shiyya Funtua.
Tunda farko, horon wanda aka fara bi Shiyyar Funtua don bada horo, tare da kammalawa da Shiyyar Funtua, inda ya zuwa yanzu ake ci gaba da gudanarwa a Katsina ta tsakiya, da kuma Shiyyar Daura nan ba da jimawa ba.
Kafin fara horaswsr, jami'an sun tsara cewa, daga kowacce mazaɓa sun ɗauki mutum ɗaya, daga cikin Mazaɓu 361 dake jihar Katsina, domin ba su horo kan inganta lafiyar idanu.
Kamar yadda Katsina Post ta samu, tunda farko, Kwamishinan Lafiya na jihar Katsina, Hon. Musa Adamu Funtua, shi ne ya umarci jami'an da su ɗauki Mutum ɗaya kowacce mazaɓa don ganin shirin ya inganta a sassan jihar.
Ya shaida ma su da su kasance masu bin kanun abubuwan da aka koyar da su, tare da bada ilimin da aka ba su ga al'ummar jihar Katsina don ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Shirin horaswar wanda gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki nauyi, ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa, za a kammala nan ba da daɗewa ba a jihar Katsina.