17/04/2024
KATSINA STATE HISBAH BOARD
FITOWA TA BIYU
Nura A Yar'adua Assalafy
09031599997
Assalamu Alaikum,
YADDA AKE SAMUN IZININ GUDANAR DA TARURRUKA NA AL'ADA DAGA HUKUMAR HISBAH TA JAHAR KATSINA
Wannan hukuma mai albarka ba ta haramta dukkan tarurruka na al'ada ba, saidai wadanda s**a saba ma shari'ah ta Muslunci, musamman wadda cikinta akwai shaye-shaye, DJ, cakuduwar maza da mata, Gala, da sauransu. Kamar yadda hukumar ta fitar da sanarwar cewa ta haramta duk wadancan miyagun al'adu.
Amma idan mutane s**a shirya taron da babu wadancan abubuwan ko masu k**a da su, to Hisbah ba ta hanawa.
Saidai ana so kafin ku gudanar da tarurruka na al'ada ana so ku rubuto takardar neman izini tare da bayyana abubuwan da taron ya tattaro da yadda taron zai gudana, hade da takardar tsarin gudanar taron (programme of events).
Hukumar Hisbah za ta duba ta gani, idan taron bai ci karo da doka ba, za ta bada izini a rubuce, inda gyara za ta gyara. Sai ku je ku yi taronku lafiya. Idan ko ku ka yi cin amana bayan an ba ku izini, ta hanyar shigo da abubuwan da aka hana ku, to hukumar Hisbah za ta dauki matakin da ya dace.
Dan Uwanku A Muslunci kuma mai kaunar ku saboda Allah mai fatan alkhairi ga Jahar Katsina da al'ummarta:-
Nura A Yar'adua Assalafy
09031599997
E-mail:- [email protected]