A T V HAUSA

A T V  HAUSA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from A T V HAUSA, News & Media Website, Katsina.

ATV Hausa Kafa Na 1 Wanda Tayi Suna Wajen Kawo Maku Ingantattun Labarai na Cikin Gida Nigeria Dama Kasashen Ketare Kamar Labaran Al-Amuran Yau Da Kullum, Wasanni, Siyasa, Addinai, Kasuwanci Da Sauransu…

An Nada Ganduje A Matsayin Khaldimul Islam Na Kasa Baki DayaHadakar kungiyoyin Alarammomi da Mahaddata ne s**a yi masa n...
21/09/2025

An Nada Ganduje A Matsayin Khaldimul Islam Na Kasa Baki Daya

Hadakar kungiyoyin Alarammomi da Mahaddata ne s**a yi masa nadin a yau Lahadi.

Wata 'Yar Majalisa A Birtaniya 'Yar Asalin Nijeriya Kemi Badenoch, Ta Ýi Allah Wadai Kan Yadda Firaministan Birtaniya Mr...
21/09/2025

Wata 'Yar Majalisa A Birtaniya 'Yar Asalin Nijeriya Kemi Badenoch, Ta Ýi Allah Wadai Kan Yadda Firaministan Birtaniya Mr. Keir Starmer Ya Amince Da Kasar Palastinu A Matsayin Kasa Mai 'Yanci

Me za ku ce?

Wani ƙaramin yaro ya mutu acikin ruwan gulbin “ƙofar kware” anan sokotoWanda yasan yan uwan wannan yaron, ya sanar dasu....
21/09/2025

Wani ƙaramin yaro ya mutu acikin ruwan gulbin “ƙofar kware” anan sokoto

Wanda yasan yan uwan wannan yaron, ya sanar dasu. Yanzu haka gawar yaron tana “ƙwanni police station”

Allah ya jikanshi da Rahma

DA ƊUMI-ƊUMI: Wata matashiya daga ƙabilar Igbo mai suna Ufedo ta karɓi addinin Musuluncin a Masallacin juma'a na Abocho ...
21/09/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Wata matashiya daga ƙabilar Igbo mai suna Ufedo ta karɓi addinin Musuluncin a Masallacin juma'a na Abocho a jiya, inda ta canza suna zuwa Habibah.

Allah ya karfafa musuluncinta, ya tabbatar da ita a sunnar Manzon Allah SAW.

Ina Fama da Ciwon Zuciya Duk Aikin da Nake Zuwa Karfin Hali nakeyi, amma Ali Nuhu da Yaji labarin Shiya biya Kudi 1.5M a...
21/09/2025

Ina Fama da Ciwon Zuciya Duk Aikin da Nake Zuwa Karfin Hali nakeyi, amma Ali Nuhu da Yaji labarin Shiya biya Kudi 1.5M aka Kaini Asibiti, Kuma Duk Wata Shike biyamin dubu dari Kudin Magani inji Jarumin Kannywood Tahir Fagge

Tun Kafin Zuwan Musulunci; Bahaushe Asalinsa Mai Gaskiya Ne !Duk Bahaushen duniya har gobe casa'in cikin dari mutane ne ...
21/09/2025

Tun Kafin Zuwan Musulunci; Bahaushe Asalinsa Mai Gaskiya Ne !
Duk Bahaushen duniya har gobe casa'in cikin dari mutane ne masu tausayi, haƙuri da gaskiya , wannan ita ce babbar alama daga cikin halayen kabilar Hausa, kuma duk wani bahaushe ya gaji wannan ɗabi'ar ne ta jini haka yana yinsa yake bazai iya canja kansa ba. Bahaushen mutum madubi ne.
Prof. Aliyu Muhammad Bunza.

Yanzu YanzuEuropean American University tace: digirin karramawar da aka baiwa mawaƙi Dauda Kahutu Rarara na bogi ne.
20/09/2025

Yanzu Yanzu

European American University tace: digirin karramawar da aka baiwa mawaƙi Dauda Kahutu Rarara na bogi ne.

ZARAR BUNU: Ina taya Rarara murna, amma ina so matasan mu su sani, samun ilimi mai inganci ya fi wakewa, da wankewa da g...
20/09/2025

ZARAR BUNU: Ina taya Rarara murna, amma ina so matasan mu su sani, samun ilimi mai inganci ya fi wakewa, da wankewa da goyon bayan azzaluman ‘yan siyasa a duniya da lahira, ko da ba a karrama ka akai ba...

Me zaku ce?

"Saurayi na ya taɓa gayyata ta gidan yar uwar sa, s**a haɗa baki da ita domin yai min fyađe.Ina zuwa gidan ta kawo min L...
20/09/2025

"Saurayi na ya taɓa gayyata ta gidan yar uwar sa, s**a haɗa baki da ita domin yai min fyađe.

Ina zuwa gidan ta kawo min Lemo mai sanyi da naji zuciyata bata aminta ba shine nace zan shiga bayi, ina shiga naji yana cewa yar uwar tasa ki tabbata Tasha lemon nan.

Dana fito na tarar bata nan ashe ta fita ne da sunan in Nasha yai abinda zaiyi shikenan sai ta dawo, ina zuwa ya matsan akan Nasha naƙi.

Daya gane nasan abinda ya shirya saiya neman da gaske naki nace kaima kanada kanwa da ya, kaji tsoron Allah duk abinda kaiwa wani sai anyi maka, yaso yaimin ta karfi Allah ya kwace ni yar gidan ta dawo dole na fita daga gidan yana kallo.

~ inji wannan matashiyar

Daga Salisu Editor,

Yanzu Yanzu: Wani Matashi Mai Suna Kabiru Ɗan Auta Dake Kofar Kibo Zariya Ta Cinnawa Takardun Degree Dinsa Wuta Sabo da ...
20/09/2025

Yanzu Yanzu: Wani Matashi Mai Suna Kabiru Ɗan Auta Dake Kofar Kibo Zariya Ta Cinnawa Takardun Degree Dinsa Wuta Sabo da Acewar sa Yau Shekarar Sa 3 Da Gama Degree Bai Samu Aiki Ba, Amma Sai Ga Mawaki Rarara Wai Yagama Degree Harda Shaidar Girmamawa,Yace Gara Ya Kona Takardun Yakoma Kasuwanci Kawai~ Daga Maryam Sabo.

DA DUMI DUMI: Zan iya Tashin Wannan duniyar cikin yan Mintina,  Ƙasar Amurka ta Gargaɗi ƙasashen duniya kan cewa kada Su...
20/09/2025

DA DUMI DUMI: Zan iya Tashin Wannan duniyar cikin yan Mintina, Ƙasar Amurka ta Gargaɗi ƙasashen duniya kan cewa kada Su ɓata Mata Rai, Sannan tace Subi a Hankali domin ta ƙirƙiri Makamin da Zai iya Tashin duniya gaba ɗaya idan ta Harba Shi.

Amurka tayi ikirarin cewa wannan makamin nata yana iya halakar da duniya

Kasar Amurka ta kerawa Sojojin ruwanta sabon makami mafi hatsari a fadin duniya, makamin da ake farmakan abokan gaba da ita ta karkashin ruwa"

"A sabon rahoton da Amurka din ta fitar kai tsaye daga babban kafar Sojojin ruwan kasar ta Amurka mai suna "Navy Stories" Bisani ta bibiya lamarin, kamar yadda Amurka din ke cewa. Wannan sabon makamin na iya halakar da duniya daga lokacin data so harbawa ga wata kasa a domin gwabza yaki"

Ko masu karatu me zakuce kan wannan ikirarin ta Amurka ga Duniya ?!

Ƴar Asalin Jihar Katsina Ta Zama Wakiliyar Nijeriya A Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur Na Duniya (OPEC) Kamfanin ...
20/09/2025

Ƴar Asalin Jihar Katsina Ta Zama Wakiliyar Nijeriya A Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur Na Duniya (OPEC)

Kamfanin Mai Na Kasa NNPCL A Karkashin Jagorancin Bayo Ojulari Ya Amince Da Naɗa Hajia Maryam Idris Bagiwa, Ƴar Asalin Jihar Katsina, A Matsayin Wakiliyar Najeriya A Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur Na Duniya (OPEC) Wadda Daman Ita Ce Manajan Daraktan Kasuwancin Kamfanin.

Wace Irin Fata Za Ku Yi Mata?

Daga Jamilu Dabawa

Address

Katsina
820101

Telephone

+2347010942309

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when A T V HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share