24/12/2025
DA ƊUMI ƊUMI: Naira Tiriliyan 210 Ta Yi ɓatan dabo a NNPC — Majalisar Dattawa Ta Tashi Tsaye
An shiga ruɗani da ɗaga hankali bayan gano wani babban gibi na kuɗaɗe da ya kai Naira Tiriliyan 210 a cikin rahoton kuɗin Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Limited), lamarin da ya girgiza Majalisar Dattawan Najeriya.
Binciken ya nuna cewa kuɗaɗen sun bayyana a matsayin bashi da kuma kuɗin da ake bin wasu, amma babu cikakken bayani kan inda s**a dosa ko yadda aka tafiyar da su.
Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a ya nuna matukar rashin gamsuwa da bayanan da NNPC ta gabatar, inda ya bukaci kamfanin da ya fito fili ya yi bayani dalla-dalla kan asalin kuɗaɗen da kuma inda s**a nufa.
Majalisar ta jaddada cewa ba za ta lamunci sakaci ko rashin gaskiya wajen tafiyar da dukiyar ƙasa ba, tare da gargadin cewa za a ɗauki ƙarin matakan bincike idan aka kasa bayar da bayanin da ya gamsar.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, NNPC Limited ba ta warware gibin ba, yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da bibiyar yadda wannan al’amari mai girma zai kaya.
👉 Ku bi shafin ATV Hausa domin samun sahihan labarai cikin sauri — Kada ku bari komai ya wuce ku.