Amira Reporters

Amira Reporters Bringing you the most recent, dependable news from Nigeria and across the world. Stay informed and empowered.

INNALILLAHI WA'INNAHI ILAIHI RAJI'UNAllah Ya yi wa mahaifiyar jarumar Kannywood, Asiya Chairlady, rasuwa.Allah Ya jiƙan ...
16/08/2026

INNALILLAHI WA'INNAHI ILAIHI RAJI'UN

Allah Ya yi wa mahaifiyar jarumar Kannywood, Asiya Chairlady, rasuwa.

Allah Ya jiƙan ta da rahama, Ya gafarta mata, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarta.

A matsayinka na ɗan Katsina, za ka iya zaɓar Sanata Ahmad Babba Kaita a matsayin gwamnan jihar?
16/08/2026

A matsayinka na ɗan Katsina, za ka iya zaɓar Sanata Ahmad Babba Kaita a matsayin gwamnan jihar?

Me za ku ce?
16/08/2026

Me za ku ce?

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Musa Kwa...
16/08/2026

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, murnar lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 15 ga Agusta 2026.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana Adeleke a matsayin abokinsa tare da taya shi murnar samun nasara a ƙarƙashin tutar jam’iyyar Accord Party.

Amira Reporters ta ruwaito cewa Kwankwaso ya yaba wa al’ummar Osun kan yadda s**a fito s**a yi amfani da ’yancinsu na zaɓe. Ya ce a matsayinsa na ɗaya daga cikin shugabannin adawa kuma mai kishin dimokuraɗiyya, yana ganin sak**akon ya nuna ƙarfin ikon jama’a wajen zaɓar shugabanninsu.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ce ta bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen da sanyin safiyar Lahadi, bayan ya doke ɗan takarar APC, Asiwaju Bola Oyebamiji.

Adeleke ya samu ƙuri’u 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815. Adeleke ya lashe ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar, yayin da Oyebamiji ya lashe 11. Ɗan takarar ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku da ƙuri’u 17,180.

Da Dumi-Dumi:Gwamna Ademola Adeleke ya sake lashe zaben jihar OsunINEC ta ayyana Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord a m...
16/08/2026

Da Dumi-Dumi:

Gwamna Ademola Adeleke ya sake lashe zaben jihar Osun

INEC ta ayyana Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun, wanda hakan ya ba shi damar sake yin gwamna a karo na biyu a jihar

Wane fata za ku yi masa?

16/08/2026

Labarin Sheikh Yahaya Jingir a Jos

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gudanar da mulkin Kano ba abu ne mai sauƙi ba, saboda yawan al’umm...
16/08/2026

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gudanar da mulkin Kano ba abu ne mai sauƙi ba, saboda yawan al’ummarta da kuma kasancewarta jiha mai cike da mutane daga sassa daban-daban na Nijeriya. Ya ce saboda haka Kano tana k**a da “ƙaramar Nijeriya.”

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ambassador Ibrahim Waiya, wanda ya wakilce shi a taron shekara-shekara na farko na Institute of Security and Strategic Studies (ISSS), inda aka karrama Gwamna Abba da lambar yabo ta ƙwarewa wajen tafiyar da harkokin tsaro.

Amira Reporters ta ruwaito cewa Waiya ya ce gwamnatin Kano ta rungumi dabarun tsaro na amfani da ƙarfi da kuma hanyoyin da ba na ƙarfi ba wajen yaƙi da rashin tsaro. Ya bayyana cewa an horar da kusan matasa 2,000, maza da mata, ƙarƙashin tsarin Neighbourhood Watch, sannan aka tura su cikin ƙananan hukumomi 44 domin taimaka wa hukumomin tsaro.

Ya kuma ce gwamnatin ta kafa Anti-Phone Snatching Corps, tare da shirin Safe Corridor, wanda aka tsara domin ƙarfafa matasan da ke shiga daba ko tashin hankalin siyasa su ajiye mak**ai su rungumi zaman lafiya. A cewarsa, an yi wa matasa kusan 340 rajista tare da tantance su a ƙarƙashin shirin, yayin da gwamnatin ta ware sama da Naira miliyan 500 domin gudanar da shi.

Da yake magana kan ƙalubalen shugabanci, Gwamna Yusuf ya ce Kano tana da yawan jama’a sosai kuma mutane daga sassa daban-daban na Nijeriya suna rayuwa a cikinta. Ya ce wannan yanayin ya sa gudanar da jihar ke buƙatar ƙoƙari da jajircewa sosai.

A nasa jawabin, masanin tsaro Dr Muhammad Ali ya yi kira ga ƙasashen Arewa maso Yamma da su ƙara haɗin gwiwa wajen yaƙi da ’yan bindiga, satar shanu, garkuwa da mutane, haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ma sauran laifuka. Ya kuma buƙaci gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai su haɗa kai wajen musayar bayanan sirri da sintiri a iyakoki.

Me za ku ce?

Gwamnatin Katsina za ta dasa bishiyoyi miliyan biyu a fadin jihar Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Di...
15/08/2026

Gwamnatin Katsina za ta dasa bishiyoyi miliyan biyu a fadin jihar

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Radda ta sanar da shirinta mai suna Katsina-One-Person-One-Tree (KT1T) na dasa bishiyoyi a fadin kananan hukumomi 34.

Matakin ya kunshi dasa da kula da bishiyoyi miliyan biyu a shekarar 2026 a wurare 6,652, yayin da babban shirin shi ne dasa bishiyoyi akalla miliyan 11 tsakanin 2026 zuwa 2030, tare da samar da inganta tattalin arziki ga wadanda za su amfana.

Gwamnatin ta amince da bayar da kwangilolin ayyukan dakile zaizayar kasa da ambaliyar ruwa a wurare 17 da ke fadin jihar

Me za ku ce?

Halin da makarantar Rahama primary school Machika ward ke ciki a karamar hukumar Mani a jihar KatsinaPHOTOS: 📸 Engr Imra...
15/08/2026

Halin da makarantar Rahama primary school Machika ward ke ciki a karamar hukumar Mani a jihar Katsina

PHOTOS: 📸 Engr Imran Abdullahi Randawa

“Abin kunya APC, muna kan hanyar lashe Osun” — DavidoFitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Dav...
15/08/2026

“Abin kunya APC, muna kan hanyar lashe Osun” — Davido

Fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi ikirarin cewa kawunsa, Gwamnan Jihar Osun Sanata Ademola Adeleke, ne ke kan gaba yayin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri’un zaɓen gwamnan jihar.

Davido ya bayyana hakan ne a jerin saƙonnin da ya wallafa a kafafen sada zumunta yayin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri’u a sassa daban-daban na jihar. Ya kuma yi ikirarin cewa jam’iyyar APC ta sha kaye a mazabar tsohon Gwamnan Jihar Osun, Cif Bisi Akande.

Amira Reporters ta ruwaito cewa Davido, wanda ya fito fili yana ƙoƙarin wayar da kan jama’a domin goyon bayan Adeleke, ya rubuta cewa: “Jam'iyyarsu ta rikice! Baba Akande ya sha kaye a mazabarsa. Gwamna Adeleke na kan hanyar samun nasara. Abin kunya APC. Osun ba Edo ba ne!”. A cewar sa.

Kuna ganin Kawun Davido zai yi nasara?

Address

Katsina
820

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amira Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share