09/10/2025
HANYOYI 10 DA C**A KE RUSA RAYUWAR MATASHI A HANKALI.
MATASHI: KAFIN KA CE 'BET', GA HADARI GUDA 10:
Caca/Betting yaudara ce ta samun kudi cikin sauki. Ga ainihin gaskiyar abin da take yi:
1.JARABA MAI TSANANI:
Yana k**a ka k**ar ƙugiya, ba za ka iya dainawa ba koda kana asara. (Addiction)
2.TALAUCI DA BASUSSuka:
Zai cinye maka duk kuɗinka ya jefa ka cikin basussuka marasa iyaka.
3.DAMUWA DA BAƘIN CIKI:
Rashin nasara yana kawo baƙin ciki, tashin hankali, da rashin bacci.
4.HANYA ZUWA GA SATA:
Idan kuɗi sun ƙare, c**a tana tura mutum zuwa ga satar kuɗin wasu.
5.RUSHEWAR ALAƘA:
Za ka fara yi wa iyalanka da abokanka ƙarya don ka ɓoye asarar da ka yi.
6.RASA AIKI KO MAKARANTA:
Hankalinka zai karkata daga aiki ko karatu zuwa kan c**a kawai.
7.RUƊIN SAMUN ARZIKI:
Yana sayar maka da mafarkin ƙarya, ya hana ka aiki tuƙuru.
8.RASHIN ALBARKA DA IMANI:
Haramun ne a addini kuma yana gusar da albarka gaba ɗaya a rayuwa.
9.BIN HASARA:
Za ka ci gaba da c**a don ka ciko asara, amma sai ƙara zurmewa kake yi.
10. ZUBAR DA MUTUNCI:
Yana sa ka raina kanka kuma ka zama abin tausayi a idon mutane.
Gumin goshinka shi ne ainihin 'Jackpot' ɗinka. Saboda haka ka AJIYE BETTING.
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️