
11/08/2025
Alhamdulillah, yau na ɗaya daga cikin lokutan da s**a fi taɓa zuciyata a rayuwa, domin na kaddamar da aikin gina sabon ofishin Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) a Dutsin Amare, Gabas II.
Wannan aiki ba daga kuɗin gwamnati ba ne. Sadaukarwa ce ta kaina, wacce na bayar a matsayin Sadaqatul Jariyah don tunawa da mahaifina, 𝐇𝐨𝐧. 𝐌𝐢𝐪𝐝𝐚𝐝 𝐀𝐃-𝐒𝐚𝐮𝐝𝐞 (Allah ya jikansa da rahama), mutum ne wanda rayuwarsa ta kasance abin koyi wajen hidima ga al'umma, gaskiya, da tsantsar jajircewa akan hidimar al’umma.
Mahaifina ya koya min cewa nagartaccen shugabanci ba-a-auna-shi da abinda mutum ya samu, a'a sai dai-abin-da-ya-bayar. A cikin girmamawa gare shi, ina roƙon Allah ya sanya wannan aiki ya zama alheri mai ɗorewa ya kai ladar gareshi, kuma ya tsare jama’armu har bayanmu, In shaa Allah. Dutsin Amare a Gabas II da sauran mazabu a cikin Karamar Hukumar Katsina za su ci gaba da kasancewa cikin tsaro, zaman lafiya, da haɗin kai In shaa Allah.
Ina kira ga matasanmu da su rungumi zaman lafiya, su zam ma su ladabi, girmamawa, da haɗin kai ga jami’an tsaro, domin zaman lafiya shi ne tubalin ginuwar ci gaba.
Allah Ya albarkaci Katsina.
Allah Ya albarkaci jiharmu mai albarka.
Allah Ya albarkaci ƙasarmu, Najeriya