Sheikh Abdulmudallib Muhammad Gusau

Sheikh Abdulmudallib Muhammad Gusau A Personal Blog.

25/11/2021

MUHIMMAN ABUBUWAN DA S**A FARU A ZAMAN KOTU NA YAU 25-11-2021
(Inda ba ƙasa, nan ake gardamar kokawa)...

Cikin ikon Allah yau ce rana ta tara a cikin jerin ranakun da ake zaman sauraron shari'ar Abduljabbar Nasiru Kabara.

A zaman na yau wanda aka kwashe awanni 5 ana sauraron shari'ar, muhimman abubuwa da yawa sun faru, ga kadan daga ciki:-

1. Ganin sababbin fuskoki a matsayin lauyoyin Abduljabbar ya ja hankalin al'umma, musamman da aka duba ba'a ga tsofaffin lauyoyin nasa ba, musamman. Barrister Umar Muhammad, Barrister Hassan Umar, da kuma Barrister Umar Faruq.

Dama ana ta samun sabani tsakanin lauyoyin da Abduljabbar, saboda shi yana so a tafiyar da Shari'ar ta yadda su masana sharia suke ganin hakan ba daidai bane.

Bayan kwanaki kadan da wancan zaman da aka yi, an samu bullar wata waya da ta gudana tsakanin Barrister Umar Muhammad, da wani jagora a ashabul Kahfi, inda shi Baristan yake nuna yadda Abduljabbar yake tafka kusakurai, yake kokarin jefa kansa a ramin da ba zai iya fita ba. Har ma shi lauyan yake tabbatar da cewa ya tambayi Abduljabbar shin kalmomin da ake tuhumar sa akan su, akwai su a Bukhari ko Muslim ko a maganganun wasu malamai? Abduljabbar yace masa babu, shine ya fada a lokacin da yake sharhi.

Watakila wannan tirka-tirkar ce ta janyo rabuwar lauyoyin da Abduljabbar, wanda dama sau biyu yana cewa ya kore su a kotu, alƙali ne yake sasanta su domin samar da daidaito.

2. Kamar yadda kotu ta nema a baya, wadansu mutane guda biyu daga jami'ar Bayero sun kawo litattafan Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim, kuma sun mikawa kotu littattafan, kotu ta duba, kuma ta bawa lauyoyin kowanne bangare domin su duba su tabbatar littattafan ne ba wasu ba? Kuma lauyoyin kowanne bangaren, har da wanda ake ƙara, sun tabbatar cewa Bukhari da Muslim ne. A karshe kotu ta yiwa littattafan lamba kamar yadda doka ta tanada.

3. Alƙali ya tambayi lauyoyi masu ƙara, shin sun cika alkawarin su na bawa Abduljabbar kudin siyan littafi?
Lauyoyin sun amsa, sun shaidawa kotu cewa sun bawa Abduljabbar ₦20,000 domin siyan Bukhari da Muslim. Kuma an tambayi lauyansa, kuma ya tabbatar da hakan.

4. A karo na uku, an kuma gabatar da shaida na biyu domin wanda ake ƙara ya cigaba da yi masa tambayoyi.

Abduljabbar ya dauki dogon lokaci yana yiwa shaida na biyun tambayoyi, kuma yayi tambayoyi masu kyau, sai dai biyu bisa uku na tambayoyin nasa basu da alaka da abinda shaida ya faɗa a gaban kotu.

Hakan ne yasa jagoran lauyoyi masu kara yake mikewa ya nemi kotu ta dakatar da shi. Shi kansa alƙali yayi wannan kokarin na nunawa Abduljabbar saukar sa daga kan layi akan tambayoyin da yake yi. Ba ma wannan ba, har Jagoran lauyoyin nasa sai da ya mike har sau uku yana jan hankalin sa akan tambayoyin da yake yi din ba muhallin yin su bane yanzu.

Abin da muke so mutane su fahimta shine, tambayoyin da muke cewa Abduljabbar yana yi ba bisa ka'ida ba, suna da muhalli a Shari'ar, musamman idan yazo DEFENCE, ba shaida zai yiwa su ba. Shi kuma a nasa rashin sanin dokar, sai yake dauko abinda yake da damar yi anan gaba, yace dole yanzu zai yi. Kuma da nayi tsammanin yana da baiwar rike abubuwa, amma sai naga duk lokacin da yayi tambayar da ba daidai ba, alƙali zai taka masa birki, kuma ya tsaya yayi masa bayanin doka game da hakan, amma da ya tashi yin wata tambayar sai kaga ya kuma fadawa wani ramin.

A karshe dai an kammala da sauraron wannan shaida na biyu, kuma za'a gabatar da shaida na uku a zama na gaba.

5. Bayan kammala sauraron shaida, Abduljabbar yayi s**a akan shaidar inda ya bayyana abubuwa kamar haƙa:
A. Yayi masa karya akan shiga ajinsu a MA'AHAD, domin ya daina shiga makarantar shekara biyu kafin shigar shaida makarantar.
B. Shaidar makiyinsa ne, domin shekara 6 da s**a wuce ya rubuta masa littafin Raddi kuma yaci mutuncin sa dana mahaifinsa.
3. A shafukan sada zumunta da ake zargin na shaidan ne, an ga hotunan wasu malaman Izala, wasu ma tare da shaidan, sannan an gani a rubuce cewa shaidan yana aiki da Jibwis Nigeria.

Da aka waiwayo ga shaida domin ya kare kansa, ya bayyana cewa tabbas ya yiwa Abduljabbar raddi a rubuce, ba don kiyayya ba, sai don rokon da Abduljabbar din yake yi na neman gyara, musamman a rubuce.

Sannan kuma ya tabbatar da cewa yayi ma'ahad, kuma Abduljabbar din yana shiga ajinsu ya yi musu kissoshi da tambayoyi (ba wai malami ne da yake karantawa permanent ba), kuma shaidan yace yana da takardu masu nuna hakan. A batun shafin sada zumunta kuma , ya bayyana cewa anyi masa kutse a kwanakin baya, inda ya samu wandansu abubuwa ba daidai ba a shafin nasa.

An tuntubi lauyoyi masu kara, ko zasu fadi wani abu akan s**ar da aka yiwa shaidan su, kuma lauyoyin sun gabatar da dalillai masu yawa da suke neman ayi watsi da s**ar.

Su ma lauyoyin Abduljabbar, sun gabatar da nasu jawaban inda suke rokon kotu tayi watsi da shaidar da shaida na biyu ya bayar.

Alƙali yace zai fadi matsayar sa akan shaida na biyun a gaba.

6. Duk da kudin da aka bashi domin siyan Bukhari da Muslim, amma har yau ya kasa nuna inda kalaman da yada suke a cikin littattafan. Hakan ya kara tabbatar da maganar Barrister Umar Muhammad na cewa ya tambayi Abduljabbar, yace masa babu a littafin, shine ya fada.

7. A lokacin da Abduljabbar yake gabatar da tambayoyi ga shaida na biyu, akan maganar sadaki, yayi ikirarin cewa Allah ya wajabtawa Annabi SAW bayar da sadaki na kudi ko kadara, da ya tashi kafa hujja, sai ya yi kokarin jawo aya ta 50 a cikin Suratul Ahzab, amma yana fara jan ayar sai ya ɓalle mata kafar dama da hannun hagu, abinda ya haifar da hayaniya a kotun, ayar dai taki jawuwa, yayi kokarin karasa ta da hannu (demonstration), amma hakan ma yaci tura, Allah Allah ya taimaka wasu sun taya shi ya karasa ayar har zuwa karshe. Da yazo fassara ayar, sai ya dauko iyaka inda yake so ya fassara, har aka yi, aka yi ya fassara ayar daga farko har karshe, amma yace a'a iyaka inda yake buƙata zai fassara. Hmmmm Allah ya taimaki Mujaddadin zamani.

8. Alƙali ya daga zaman kotun zuwa ranar 9-12-2021.

Allah Ya taimaki gaskiya da masu gaskiya, Allah Ya rusa karya da makaryata.



Awaisu Al'arabee Fagge
Jibwis Social Media
Kano State.

Abduljabbar: Abubuwan mamakin da s**a faru ranar rasuwar mahaifiya ta, har sama sai da...
24/11/2021

Abduljabbar: Abubuwan mamakin da s**a faru ranar rasuwar mahaifiya ta, har sama sai da...

Abduljabbar yayi bayanin wadansu Abubuwan mamakin da s**a faru ranar rasuwar mahaifiya ta, har sama sai da tayi rashin lafiya a fadar sa.

AL-WASILAH TV  A YOUTUBEKu danna mana SUBSCRIBE na wannan Channel tamu mai albarka, domin samun shirye shirye masu fa'id...
13/11/2021

AL-WASILAH TV A YOUTUBE

Ku danna mana SUBSCRIBE na wannan Channel tamu mai albarka, domin samun shirye shirye masu fa'ida, daga malaman Musulunci daban daban dake fadin kasar nan.

https://youtube.com/c/AlWasilahTv
Ku danna mana Subscribe....

Al-Wasilah Tv is a 24/7 Tv show channel which features live and pre-recorded programs of multiple Islamic scholars, in Hausa, English And Arabic.

Martanin Alqali Mustapha Ga Lauyan Kaninsa Abduljabbar
30/10/2021

Martanin Alqali Mustapha Ga Lauyan Kaninsa Abduljabbar

Martanin Alqali Mustapha Ga Lauyan Kaninsa (Abduljabbar)

Karatun Littafin Muwadda Malik, Darasi Na 212 ll Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar
30/10/2021

Karatun Littafin Muwadda Malik, Darasi Na 212 ll Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar

Karatun Littafin Muwadda Malik 212 ll Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar...

Hirar Da Akayi Da Lauyan Abduljabbar A Tashar Qibla Fm Akan Zaman Kotu Na Jiya
29/10/2021

Hirar Da Akayi Da Lauyan Abduljabbar A Tashar Qibla Fm Akan Zaman Kotu Na Jiya

A zaman kotu. a jiya, an samu tirka tirka mai yawa, ku saurari wannan hira da akayi da ɗaya daga cikin lauyoyin Abduljabbar mai suna Barrister Umar Hassan, d...

MUHIMMAN ABUBUWAN DA S**A FARU A ZAMAN KOTU NA YAU 28--10-2021(Mai hali ba ya fasa halin sa)Yau ce rana ta bakwai a jeri...
28/10/2021

MUHIMMAN ABUBUWAN DA S**A FARU A ZAMAN KOTU NA YAU 28--10-2021
(Mai hali ba ya fasa halin sa)

Yau ce rana ta bakwai a jerin ranakun da aka zauna domin cigaba da sauraron shari'ar batanci da ake zargin Abduljabbar Kabara da aikatawa. Kuma a zaman na yau, akwai muhimman abubuwan da s**a faru, ga su kamar haka:-

1. Bayyanar wadansu sababbin fuskoki a cikin lauyoyin Abduljabbar: Barista Umar Muhd, shine lauyan dake jagorantar lauyoyin Abduljabbar, amma a yau wani lauya mai suna Muhd Aliyu, shine ya jagoranci lauyoyin Abduljabbar din, tare da rakiyar waɗansu lauyoyin, ciki har da na baya. Watakila hakan ta faru ne saboda saɓanin da Abduljabbar ya samu da jagoran lauyoyin nasa.

2. Karatun Baya: Idan zaku iya tunawa, a zaman da ya gabata, alƙali yayi umarni ga masu ƙara akan su tabbatar a yau sun gabatar da hujjojin su akan tsayuwar SAN a gaban irin wannan kotun, da kuma yin bayani akan damar da Attorney General ya bawa lauyoyi masu zaman kansu domin shiga wannan Shari'a, da kuma hujja akan takardar Charges da s**a mikawa kotu, bayan FIR din da ƴan sanda s**a gabatar tun a farkon shari'ar.

A nan ne jagoran lauyoyi masu gabatar da kara ya mike ya gabatar da tarin hujjojin akan damar da A/G ya bawa lauyoyi masu zaman kansu, sannan ya bawa Barista Usman Zunnurayn dama ya karanta nassoshi da s**a bada bada ga mai ƙara ya yi karin bayani ko ya fayyace wani abu da bai fito fili ba acikin tuhumar sa da ta gabata.

A nan, alƙali ya tambayi lauyoyin Abduljabbar shin suna da s**a? Sun amsa masa cewa suna da ita, amma sai a zama na gaba.

3. Gabatar da Shaida na biyu: A wancan zaman an saurari shaida na farko ne, amma fusatarwar da Abduljabbar ya yi wa lauyan sa, yasa s**a nemi a dage sauraron shaida na biyu sai a yau.

An gabatar da shaida na biyu a yau, kuma alƙali da kuma lauyan masu ƙara, sun yi masa tambayoyi masu yawa bayan alƙali ya saka shaidan ya ɗauki alkawarin zai fadi gaskiya a shaidar da zai bayar.

4. Saɓani tsakanin lauyoyin Abduljabbar: Bayan alƙali da lauyan masu ƙara sun gama yiwa shaida na 2 tambayoyi, alƙali ya waiwayi lauyoyin Abduljabbar, ko sun amince da shaidar da aka gabatar?
"A'a, bamu amince da shaidar da ba, suna da tambayoyi da s**a akan shaidar sa, amma ina neman izinin kotu wajen gabatar abokin aiki na domin ya yi tambayoyi ga shaidan". Inji Jagoran lauyoyin Abduljabbar. Kuma kotu ta ba shi damar hakan.

Shi lauyan da aka bawa dama yayi tambayoyin, yana mike wa, sai yace "Dan uwa na lauya yayi AZARBABI, domin muna da tambayoyi da s**a ga shaida, amma sai bayan mun yi roko"...

Alƙali: Na baku damar ku yi roƙon muddin akan wannan ne ba akan wani abin daban ba.

A nan ne lauyan ya bukaci a basu dama domin shi Abduljabbar ya yiwa shaida tambayoyi da kansa a madadin lauyoyin, ana mai Shari'a ya turje, ya jawo Constitution ya fassara. "A tsarin doka, idan mutum yana da lauya, to ba shi da damar yin hakan, sai dai ya bar lauyan sa yayi, ko ya rubuta wa lauyan abin da yake buƙata, shi kuma ya karanta. In kuwa har ana so wanda ake ƙara yayi abinda kuke bukata, to sai dai ya sallami lauyoyin sa, ya cigaba da kare kansa har karshen Shari'a. Haka yake a doka" In ji Alƙali. A nan tsaya akayi ta ruwan sakin layi domin samun daidaito.

5. Abduljabbar ya a fatattaki lauyoyin sa: Ana tsaka da tafka muhawara akan abinda na ambata a baya, sai aka ga wanda ake ƙara ya daga hannu, alamar yana da magana. Kotu ta bashi dama domin yayi magana, kuma yayi maganganu masu yawa, ga muhimmai daga ciki wadanda ya faɗa da bakinsa:

A. Na kasance mai biyayya ga doka da kuma lauyoyi na akan aikinsu. Irin wannan biyayyar da nake yi wa lauyoyin nawa ne tasa suna sakani nayi shiru a lokacin da aka karanta min tuhumomi, kuma na tambaye su matsayin hakan s**a ce min babu wata matsala, APPEAL Kawai zasu yi akan karanta tuhumomin, kuma a gabanku, basu yi ba.

B. Na hadu da matsaloli da yawa tsakani na da Lauyoyi da likitoci, na faɗa wa kotu wasu, wasu kuma na barwa Allah, a ciki har da keta alfarmar iyali na.

C. Ba muyi da lauyoyi na zasu fita ba, kawai a kotu na ga sun bayyana hakan, abinda na sani kawai shine, na nuna musu damuwa ta akan abinda s**a saka ni nayi, da kuma illar da hakan ya jawo, ba dan Allah ya kiyaye ba, da an samu matsala (a ƙwaƙwalwa ta) da duk ayyukan da nayi sun rushe).

D. Na rantse wa lauyoyi na da Allah, ba zan kuma yin shiru akan wannan tuhumomi da ake min ba.

E. Tunda aka karanta min tuhumomi na san ina da amsar su, ko a yanzu, banda wadannan littattfan (35 ne kamar yadda na ƙirga su) akwai fiye da 100 a cikin mota (wadda ake kawo shi daga gidan gyaran hali).

F. Gazawar lauyoyi na wajen yin tambayoyin da s**a kamata akan shaidar na farko, shi yasa na zo da sabon lauya. Saboda wancan tun a Prison, na zauna da shi, na tsara masa abinda nakeso ya tambayi shaida, na basu MP3 da zasu danna wasu muryoyi, na basu Full karatuttukan da ake magana a kansu, na je musu da littattafan da nake so su bawa shaida ya karanta amma duk basu yi ba.

G. NA TABBATA BABU WANI LAUYA DA ZAI IYA KARE NI DAGA WANNAN TUHUMOMI DA AKE YI MIN.

H. Idan na bari lauyoyi s**a jagorance shari'a ta a haka, (to laifi zai tabbata a kai na) amma ba hukunci nake tsoro ba, bacin suna a wajen Allah da wajen mutane ne bana so. Ko mun zauna da lauyoyi na ko bamu zauna ba, amsar ɗaya ce, ba zasu taba iya bayanin hujjoji na ba.

I. Lauyan da yake jin Larabci a cikinsu ma, YANZU NA BASHI LITTAFI, NA JA MASA LAYI DAIDAI INDA NAKE SO YA BAYAR A KARANTA, AMMA KO BAƘIN YA KASA JA, B***E YA FAHIMCI SHARHIN MAGANAR, saboda haka wannan CASE din na hadisai ne ba na LAW ba.

J. Duk shawarin da alƙali ya bani na yin hakuri da zama da lauyoyi na, nayi, amma babu chanji, nayi zama da su nayi musu SEMINA, amma abin ya ci tura. Sun ce min wai shaida na farko jahili ne shi yasa basu bashi littafi ba, sai nace musu ta yaya jahili zai haddace Kur'ani, ya karanta littattafan fikihu sama da 10, na hadisi 20?

K. Na jarraba wadancan lauyoyin sun kasa, kuma ba'a saran mumini sau biyu a rami sai biyu, sabo da haka NA CIRE LAUYOYI NA, ZAN KARE KAI NA.

Haka dai Abduljabbar yayi ta bayani a kotu.

Amma alƙali yayi iyaka ƙoƙarin sa wajen kara yin sulhu tsakanin Abduljabbar da lauyoyin nasa, kamar yadda ya yi a wancan zaman.

Abinda muka iya tsakuro muku kenan daga zaman kotu na yau. Kuma muna baku hakuri bisa tsayin da rubutun ya yi, babu makawa ne sai hakan ya faru.



Awaisu Al'arabee Fagge
Jibwis Social Media
Kano State.

TIrƙashi: 1. Yadda Abduljabbar yake yiwa iyayensa laɓe idan suna magana, 2.Yadda Mahaifiyar sa take kokawa da halayyar s...
22/10/2021

TIrƙashi:
1. Yadda Abduljabbar yake yiwa iyayensa laɓe idan suna magana, 2.Yadda Mahaifiyar sa take kokawa da halayyar sa,
3. Yadda yace sunyi tafiya zuwa Zaria a Taku daya, kuma sun dawo a Taku daya.

Ku kalli bidiyon dake kasa, kuma ku danna mana Subscribe...

ku Kalla ku ji yadda Abduljabbar yake ƙaryar karama da shi da mahaifinsa wai sunje Zaria a Taku daya.

Gudummawar da Sahabbai s**a bayar a addinin Musulunci- Sheikh Lawan Abubakar Triumph...
22/10/2021

Gudummawar da Sahabbai s**a bayar a addinin Musulunci
- Sheikh Lawan Abubakar Triumph...

Gudummawar Sahabbai A Musulunci || Sheikh Lawan Abubakar Triumph

Tafsirin Suratut-taubah aya ta 113 ll Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale
20/10/2021

Tafsirin Suratut-taubah aya ta 113 ll Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale

Tafsirin Suratut-taubah, aya ta 113 ll Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale

Address

Katsina

Telephone

+2348030918468

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Abdulmudallib Muhammad Gusau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sheikh Abdulmudallib Muhammad Gusau:

Share