05/09/2026
’YAN SANDAN YOBE SUN CAFKE JAMI’AR MONIEPOINT KAN ZARGIN DAMFARAR ₦74M
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta sanar da k**a wata jami’ar kamfanin Moniepoint mai aiki a matsayin Field Loan Officer, bisa zargin damfarar wasu ma’aikatan POS guda bakwai a Damaturu, da kuɗin da ake hasashen sun kai ₦74,000,000.
A ranar 4 ga Satumba 2026, ma’aikatan POS ɗin bakwai sun kai ƙorafi daban-daban a Hedikwatar ’Yan Sandan ‘A’ Division da ke Damaturu, inda s**a zargi jami’ar mai suna Thlakham Daniel, mai shekaru 32, da amfani da bayanan asusunsu wajen karɓar lamuni ba tare da izininsu ba.
A cewar masu ƙorafin, jami’ar ta riƙa ziyartar wuraren kasuwancinsu, inda ta yi musu rajista tare da karɓar bayanan asusun su, tana mai cewa za ta taimaka musu wajen samun lamuni.
Sai dai daga baya s**a gano cewa an karɓi lamuni ta amfani da bayanan asusunsu ba tare da saninsu ko amincewarsu ba.
Bayan samun rahoton, jami’an bincike s**a fara gudanar da bincike tare da bin diddigin lamarin, wanda ya kai ga k**a wadda ake zargin. Haka kuma, an ƙwace wata mota da ake zargin an saya da kuɗin da aka samu daga laifin.
Rundunar ta ce a yayin binciken farko, wadda ake zargin ta amsa hannu a aikata laifin, yayin da jimillar kuɗin da ake bincike a kansu s**a kai kusan ₦74m.
Ana ci gaba da bincike domin gano cikakken yadda lamarin ya faru da kuma tantance ko akwai wasu mutane da ke da hannu a ciki.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da bibiyar laifukan damfara da sauran laifukan kuɗi cikin ƙwarewa.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa taka-tsantsan wajen bayar da bayanan asusun banki da na kuɗin zamani, domin kare kansu daga fadawa hannun masu damfara.
SAURAN BAYANI: An samar da hoton da ke tare da wannan rahoto ne ta amfani da Fasahar AI.